Musa Ya Maimaita Dokar Hukunci (continued)

1451 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Maimaitawar Shari’a 19–20

1 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya hallakar da al’ummai waɗanda yake ba ku ƙasarsu, sa’ad da kuka kore su, kuka kuma zauna a birane da gidajensu, 2 sai ku keɓe wa kanku birane uku waɗanda suke a tsakiyar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka. 3 Ku gina hanyoyi zuwa cikinsu, ku kuma raba ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo kashi uku, saboda duk wani da ya yi kisankai yă iya gudu zuwa can.

4 Ga doka game da mutumin da ya kashe wani, ya kuma gudu don yă cece ransa, wani wanda ya kashe maƙwabcinsa ba da gangan ba, ba kuwa da wata ƙiyayya a tsakaninsu a dā ba. 5 Misali, in mutum ya je jeji da maƙwabcinsa domin yankan itace, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe daga ƙotar yayinda yake saran itacen, ya sari maƙwabcin har ya mutu. Mutumin nan zai iya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane don yă ceci ransa. 6 In ba haka ba mai neman ɗaukan fansa jini, zai iya binsa cikin fushi, yă cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da yake ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā. 7 Wannan ne ya sa na umarce ku ku keɓe wa kanku birane uku.

8 In Ubangiji Allahnku ya fadada yankinku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa wa kakanninku, ya kuma ba ku ƙasar gaba ɗaya kamar yadda ya yi musu alkawari, 9 idan dai kun lura, kuka kiyaye umarnin da nake ba ku a yau, wato, ta wurin ƙaunar Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya kullum cikin hanyoyinsa, to, sai ku keɓe ƙarin birane uku. 10 Ku yi haka don kada a zub da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, don kada ku kuma zama masu laifin zub da jini.

11 Amma idan wani mutum yana ƙin maƙwabcinsa, ya kuma yi kwanto yana fakonsa, ya yi masa rauni, har ya kashe shi, sa’an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane, 12 dattawan garinsa za su aika a kawo shi, a dawo da shi daga birnin, a miƙa shi ga mai neman fansar jini don yă kashe shi. 13 Kada ku ji tausayinsa. Dole ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga Isra’ila, don ku sami zaman lafiya.

14 Kada ka gusar da dutsen nuna shaidar iyakar maƙwabcinka wanda kakanni suka sa, a gādon da ka samu a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka mallaka.

15 Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku.

16 In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi, 17 dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin. 18 Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne, 19 to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku. 20 Sauran mutane za su ji wannan su kuma ji tsoro, ba kuwa za a ƙara yin irin wannan mugun abu a cikinku ba. 21 Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa.

20:1 Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, kuka ga dawakai da kekunan yaƙi da kuma mayaƙan da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu, domin Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar zai kasance tare da ku. 2 Sa’ad da kuke gab da kama yaƙi, sai firist yă zo gaba yă yi wa mayaƙan jawabi. 3 Zai ce, “Ku ji, ya Isra’ila, yau kuna gab da kama da abokan gābanku. Kada ku karai, ko ku ji tsoro; kada ku firgita, ko ku yi rawar jiki a gabansu. 4 Gama Ubangiji Allahnku, yana tafe tare da ku, zai yaƙi abokan gābanku dominku, yă ba ku nasara.”

5 Hafsoshi za su ce wa mayaƙa, “Ko akwai wanda ya gina sabon gida bai kuma buɗe shi ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă buɗe shi. 6 Ko akwai wani da ya shuka inabi, bai kuwa fara jin daɗinsa ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă ji daɗinsa. 7 Ko akwai wani da aka yi masa alkawarin mata, bai kuwa aure ta ko ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă aure ta.” 8 Sa’an nan hafsoshin za su ƙara da cewa, “Ko akwai wani da yake tsoro, ko ya karai? Bari yă tafi gida don kada ’yan’uwansa su karai su ma.” 9 Sa’ad da hafsoshin suka gama magana da mayaƙan, sai su naɗa komandodi a kansu.

10 Sa’ad da kuka haura don ku fāɗa wa birni, sai ku fara neman garin da salama. 11 In sun yarda da salamar, suka buɗe ƙofofin garinsu, to, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su kuma yi muku aiki. 12 In kuwa suka ƙi salamar, suka fāɗa muku da yaƙi, sai ku yi wa wannan birni ƙawanya. 13 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba da shi cikin hannunku, sai ku kashe dukan mazan da suke cikinsa da takobi. 14 Game da mata, yara, dabbobi da kuma sauran abubuwan da suke cikin birnin, za ku iya kwasa waɗannan a matsayin ganima wa kanku. Za ku kuma yi amfani da ganimar da Ubangiji Allahnku ya ba ku daga abokan gābanku. 15 Haka za ku yi da dukan biranen da suke nesa da ku, waɗanda kuma ba na al’ummai da suke kusa ba.

16 Amma fa, a cikin biranen al’ummai da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kada ku bar wani abu mai numfashi da rai. 17 Ku hallaka su ƙaƙaf, wato, Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa, yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku. 18 In ba haka ba, za su koya muku ku bi dukan abubuwan banƙyaman da suke yi, ta yin sujada wa allolinsu, ta haka kuwa ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.

19 Sa’ad da kuka yi wa birni ƙawanya kuka daɗe, kuka yi ta yaƙi don ku ci shi, kada ku sassare itatuwansa da gatari, domin za ku ci ’ya’yansu. Kada ku sassare su. Gama itatuwan da suke cikin gonaki, ba mutane ne da za ku yi musu ƙawanya? 20 Amma fa, za ku iya sassare itatuwan da kuka sani ba sa ba da ’ya’ya, ku kuma yi amfani da su don ayyukan gina ƙawanyar, sai an ci birnin da yaƙi.