Annabce-annabcen Mika Sun Goyi Bayan Gyaran Hezekiya

722 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mika 3–5

1 Sa’an nan na ce,

“Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub,

ku masu mulkin gidan Isra’ila.

Ya kamata ku san shari’a,

2 ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta,

ku da kuke feɗe mutanena

kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;

3 ku da kuke cin naman mutanena,

ku feɗe fatar jikinsu

kuke kakkarya ƙasusuwansu,

kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya,

kamar naman da za a sa a dafa.”

4 Sa’an nan za su kira ga Ubangiji,

amma ba zai amsa musu ba.

A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su

saboda irin muguntar da suka yi.

5 Ga abin da Ubangiji ya faɗa,

“Game da annabawa

masu ɓad da mutanena,

in wani ya ciyar da su,

sai su ce akwai ‘salama’

amma in bai ciyar da su ba,

a shirye suke su kai masa hari.

6 Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba,

kuma duhu, ba tare da duba ba.

Rana za tă fāɗi wa annabawa,

yini kuma zai zama musu duhu.

7 Masu gani za su ji kunya,

masu duba kuma za su ji taƙaici.

Dukansu za su rufe fuskokinsu

gama ba amsa daga Allah.”

8 Amma game da ni, ina cike da iko

ta wurin Ruhun Ubangiji

da kuma adalci da ƙarfi,

don a sanar da Yaƙub laifofinsa,

ga Isra’ila kuma zunubinsa.

9 Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub,

ku masu mulkin gidan Isra’ila,

ku da kuke ƙyamar gaskiya,

kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;

10 kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini,

Urushalima kuma ta wurin mugunta.

11 Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne,

firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su,

annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi.

Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa,

“Ba Ubangiji yana tare da mu ba?

Ba bala’in da zai zo mana.”

12 Don haka, saboda ku,

za a nome Sihiyona kamar gona,

Urushalima kuma ta zama tarin juji,

tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.

4:1 A kwanakin ƙarshe

za a kafa dutsen haikalin Ubangiji

yă zama babba a cikin duwatsu.

Za a ɗaga shi sama da tuddai,

mutane kuma za su riƙa ɗunguma zuwa gare shi.

2 Al’ummai da yawa za su zo su ce,

“Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,

zuwa gidan Allah na Yaƙub.

Zai koya mana hanyoyinsa,

don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.”

Doka za tă fita daga Sihiyona,

maganar Ubangiji kuma daga Urushalima.

3 Zai shari’anta tsakanin mutane

yă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa.

Har su mai da takubansu su zama garemani,

māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace.

Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba,

ko a yi horarwa don yaƙi.

4 Kowa zai zauna a tushen kuringar inabinsa

da tushen ɓaurensa,

kuma ba wanda zai tsoratar da su,

gama Ubangiji Maɗaukaki ne ya faɗa.

5 Dukan al’ummai za su iya tafiya

a cikin sunan allolinsu;

mu dai za mu yi tafiya a cikin sunan Ubangiji

Allahnmu har abada abadin.

6 “A wannan rana,” in ji Ubangiji,

“zan tattara guragu;

zan kuma tara masu zaman bauta,

da waɗanda na sa suka damu.

7 Zan mai da guragu su zama raguwa,

waɗanda aka kora, su zama al’umma mai ƙarfi.

Ubangiji zai yi mulkinsu a Dutsen Sihiyona

daga wannan rana da kuma har abada.

8 Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke,

Ya mafaka Diyar Sihiyona,

za a maido miki da mulkinki na dā,

sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”

9 Don me yanzu kike kuka da ƙarfi,

ba ki da sarki ne?

Masu shawararki sun hallaka ne,

da zafi ya cika ki kamar mace mai naƙuda?

10 Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona,

kamar macen da take naƙuda,

don yanzu dole ki bar birni

ki kafa sansani a filin Allah.

Za ki tafi Babilon;

a can za a kuɓutar da ki.

A can ne Ubangiji

zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki.

11 Amma yanzu al’ummai da yawa

suna gāba da ke.

Suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita,

bari mu zuba wa Sihiyona ido.”

12 Amma ba su san

tunanin Ubangiji ba;

ba su fahimci shirinsa ba,

shi da ya tattara su kamar dammuna a masussuka.

13 “Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona,

gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe;

zan ba ki kofatan tagulla

domin ki ragargaje al’ummai masu yawa.”

Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba,

wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya.

5:1 Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa,

gama an kewaye mu da yaƙi.

Za su bugi kumatun mai mulkin

Isra’ila da sandar ƙarfe.

2 “Amma ke, Betlehem ta Efrata,

ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda,

daga cikinki wani zai zo domina

wanda zai yi mulkin Isra’ila,

wanda asalinsa

tun fil azal ne.”

3 Saboda haka za a yashe Isra’ila

har sai wadda take naƙuda ta haihu

sauran ’yan’uwansa kuma sun dawo

su haɗu da Isra’ilawa.

4 Zai tsaya yă yi kiwon garkensa

da ƙarfin Ubangiji,

cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa.

Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa

za tă kai har ƙarshen duniya.

5 Zai kuma zama salamarsu.

Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari

suka tattake kagarunmu,

za mu tā da makiyaya bakwai,

har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.

6 Za su yi mulkin ƙasar Assuriya da takobi,

ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi.

Zai cece mu daga hannun Assuriyawa

sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari

suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.

7 Raguwar Yaƙub za tă kasance

a tsakiyar mutane masu yawa

kamar raɓa daga Ubangiji,

kamar yayyafi a kan ciyawa,

wanda ba ya jiran mutum

ko kuma yă dakata wa ɗan adam.

8 Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai,

a cikin mutane masu yawa,

kamar zaki a cikin sauran namun jeji,

kamar ɗan zaki cikin garken tumaki,

wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu,

ba kuwa wanda zai cece su.

9 Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka,

za a hallaka maƙiyanka duka.

10 “A wannan rana,” in ji Ubangiji

“Zan hallaka dawakanku daga cikinku,

in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.

11 Zan hallaka biranen ƙasarku

in yi rugu-rugu da dukan katangunku.

12 Zan kawar da maitarku,

ba za a ƙara yin sihiri ba.

13 Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa

da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku,

nan gaba ba za ku ƙara rusuna

wa aikin hannuwanku ba.

14 Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku

in kuma rurrushe biranenku.

15 Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala

a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.”