Ishaya Ya Annabta Hallakar Mowab
726 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Abin da Allah ya yi magana a kan Mowab shi ne,
An lalatar da Ar a Mowab,
an hallaka ta da dare!
An lalatar da Kir a Mowab,
an hallaka ta da dare!
2 Dibon ya haura zuwa haikalinta,
zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka;
Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba.
An aske kowane kai
an kuma yanke kowane gemu.
3 A tituna sun sa tsummoki a jikunansu;
a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa
dukansu sai makoki suke yi,
sun kwanta suna kuka.
4 Heshbon da Eleyale sun yi kuka da ƙarfi,
aka ji muryoyinsu ko’ina har zuwa Yahaz.
Saboda haka mayaƙan Mowab suka yi kuka da ƙarfi,
har zuciyarsu ta karai.
5 Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab;
mutanenta sun gudu har zuwa Zowar,
har zuwa Eglat Shelishiya.
Sun haura zuwa Luhit,
suna tafe suna kuka;
a kan hanyar zuwa Horonayim
suna makoki saboda hallakawarsu.
6 Ruwayen Nimrim sun ƙafe
ciyayin kuma sun bushe;
tsire-tsire duk sun ɓace
babu sauran ɗanyen abu.
7 Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye
sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su.
8 Ƙugin kukansu ya kai ko’ina a iyakar Mowab;
kururuwarsu ta kai har zuwa Eglayim,
makokinsu ya kai har zuwa Beyer-Elim.
9 Ruwayen Dimon sun cika da jini,
amma zan yi ƙari a kan Dimon,
zan kawo zaki a kan masu gudu na Mowab
da kuma a kan waɗanda suka ragu a ƙasar.
16:1 Ku aiko da raguna a matsayin haraji
ga mai mulkin ƙasar,
daga Sela a hamada,
zuwa dutsen Diyar Sihiyona.
2 Kamar tsuntsaye masu firiya
da aka kora daga sheƙa,
haka matan Mowab suke
a kogunan Arnon.
3 “Ku ba mu shawara,
ku yanke shawara.
Ku mai da inuwarku kamar dare,
a tsakar rana.
Ku ɓoye masu gudun hijira,
kada ku bashe masu neman mafaka.
4 Ku bar Mowabawa masu gudun hijira su zauna tare da ku;
ku zama mafakarsu daga mai neman hallaka su.”
Mai danniya zai zo ga ƙarshe
hallaka kuma za tă daina;
masu lalatar da ƙasa za su kare
5 Da ƙauna za a kafa kursiyi;
da aminci mutum zai zauna a kansa,
wani daga gidan Dawuda,
wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya
ya hanzarta yin adalci.
6 Mun ji fariyar Mowab,
mun ji yawan fariyarta da girmankanta,
fariyarta da reninta,
amma taƙamarsu ta banza ce.
7 Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi,
za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab.
Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki
saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset.
8 Gonakin Heshbon sun bushe,
inabin Sibma ma haka.
Masu mulkin al’ummai
sun tattake inabi mafi kyau,
waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer
suka bazu ta wajen hamada.
Tohonsu sun buɗu
suka kai har teku.
9 Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka,
saboda inabin Sibma.
Ya Heshbon, ya Eleyale,
na cika ku da hawaye!
Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna
da kuma girbinku sun ɓace.
10 An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya;
babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi;
babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi,
gama na kawo ƙarshen yin sowa.
11 Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya,
na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset.
12 Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu,
tana gajiyar da kanta ne kawai;
sa’ad da ta tafi wurin tsafinta don tă yi addu’a,
babu wani amfani.
13 Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab. 14 Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta, ’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”