Sashe na 14: Mulkin Manasse
Masarautar Yahuda
Bautar Gumaka ta Manasse
698 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Manasse yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara hamsin da biyar a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hefziba. 2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya bi munanan al’adun al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. 3 Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada. 4 Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.” 5 Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari. 6 Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.
7 Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada. 8 Ba zan ƙara sa Isra’ilawa su fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, idan dai za su kula su aikata dukan abin da na umarce su, su kuma kiyaye dukan dokokin da na ba wa bawana Musa yă umarce su.” 9 Amma mutanen ba su kasa kunne ba. Manasse ya ɓad da su, har suka yi muguntar da ta fi ta al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.
10 Ubangiji ya yi magana ta bakin bayinsa annabawa, 11 “Manasse, sarkin Yahuda ya aikata waɗannan ƙazantattun zunubai. Ya aikata mugunta fiye da ta Amoriyawan da suka riga shi, ya kuma sa Yahuda ta bauɗe ta wurin yin zunubi saboda gumakansa. 12 Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, zan jawo wa Urushalima da kuma Yahuda masifar da duk kunnen da ya ji, sai ya kusa suma. 13 Zan auna Urushalima da ma’aunin da na yi amfani da shi a kan Samariya, zan kuma yi amfani da magwajin da na yi amfani da shi a kan gidan Ahab. Zan shafe Urushalima yadda mutum yake wanke kwano yă kife. 14 Zan rabu da ragowar gādona, in kuma miƙa su ga maƙiyansu. Abokan gābansu za su washe suka kuma kwashi ganima daga gare su, 15 domin sun aikata mugunta a idanuna, suka kuma tsokane ni tun daga ranar da kakanninsu suka fito daga Masar, har yă zuwa yau.”
16 Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji.
Ishaya Ya Annabta Zaman Bautar Shebna
15 Ga abin da Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa,
“Je, ka faɗa wa wannan mai hidima,
Shebna, sarkin fada.
16 Mene ne kake yi a nan kuma wa ya ba ka izini
ka haƙa kabari wa kanka a nan,
kana fafe kabarinka a bisa
kana sassaƙa wurin hutunka a dutse?
17 “Ka yi hankali, Ubangiji yana shirin ya kama ka da ƙarfi
ya kuma ɗauke ka, ya kai mai ƙarfi.
18 Zai dunƙule ka kamar ƙwallo
ya jefa ka a cikin ƙasa mai girma.
A can za ka mutu
a can kuma kekunan yaƙinka masu daraja za su kasance,
abin kunya kake ga gidan maigidanka!
19 Zan tumɓuke ka daga makaminka,
za a kuma kore ka daga matsayinka.
20 “A wannan rana zan kira bawana, Eliyakim ɗan Hilkiya. 21 Zan rufe shi da rigarka in kuma yi masa ɗamara in miƙa masa ikonka. Zai zama mahaifi ga waɗanda suke zama a Urushalima da kuma gidan Yahuda. 22 Zan sa mabuɗin gidan Dawuda a kafaɗarsa; abin da ya buɗe ba mai rufewa, kuma abin da ya rufe ba mai buɗewa. 23 Zan kafa shi kamar turke a tsayayyen wuri; zai zama mazaunin daraja domin gidan mahaifinsa. 24 Dukan ɗaukakar iyalinsa za tă rataya a kansa daga ’ya’yansa da zuriyarsa har zuwa dukan ƙananan kayan aikinsa, wato, daga kwanoni har zuwa tuluna.
25 “A ranan nan, in ji Ubangiji Maɗaukaki, turken da aka kafa a tsayayyen wuri zai sumɓule; za a sare shi ya fāɗi, za a kuma datse nauyin da yake rataya a kansa.” Ni Ubangiji na faɗa.