Zaman Bautar Manasse da Mutuwarsa
676 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
11 Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon. 12 Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa. 13 Da ya yi addu’a gare shi, sai Ubangiji ya taɓu da tubansa, ya kuma saurari roƙonsa; saboda haka ya dawo da shi Urushalima da kuma zuwa mulkinsa. Sa’an nan Manasse ya san cewa Ubangiji shi ne Allah.
14 Daga baya ya sāke gina katangar waje na Birnin Dawuda, yamma da maɓulɓular Gihon a cikin kwari, har zuwa mashigin Ƙofar Kifi, ya kuma kewaye tudun Ofel; ya yi ta da tsayi sosai. Ya sa hafsoshin mayaƙa cikin dukan biranen katanga a Yahuda.
15 Ya fid da baƙin alloli, ya kuma fid da siffofi daga haikalin Ubangiji, haka ma dukan bagadan da ya gina a kan tudun haikali da kuma cikin Urushalima, ya zubar da su a bayan birni. 16 Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji ya kuma miƙa hadayun salama da kuma hadayun godiya a bagaden, ya kuma faɗa wa Yahuda su bauta wa Ubangiji, Allah na Isra’ila. 17 Mutane dai suka ci gaba da miƙa hadayu a masujadai kan tudu, amma wa Ubangiji Allahnsu kaɗai.
18 Sauran ayyukan mulkin Manasse, haɗe da addu’arsa ga Allahnsa da kuma kalmomin da mai duba ya yi masa cikin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, suna a rubuce cikin tarihin sarakunan Isra’ila. 19 Addu’arsa da yadda Allah ya taɓu ta wurin tubansa, da kuma dukan zunubansa da rashin biyayyarsa, da wuraren da ya gina masujadan kan tudu ya kuma kafa ginshiƙan Ashera da gumaka kafin ya ƙasƙantar da kansa, duka suna a rubuce cikin tarihin mai duba. 20 Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a fadansa. Sai Amon ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
17 Game da sauran ayyukan mulkin Manasse, da duk abin da ya yi, har da zunubin da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 18 Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a lambun fadansa, lambun Uzza. Sai Amon ɗansa ya gāje shi.
1 Manasse yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyar. 2 Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji, yana bin ayyukan banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. 3 Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada. 4 Ya gina bagadai cikin haikalin Ubangiji, waɗanda Ubangiji ya ce, “Sunana zai kasance cikin Urushalima har abada.” 5 Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari. 6 Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.
7 Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon, “Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada. 8 Ba zan ƙara bari ƙafafun Isra’ilawa su bar ƙasar da na ba wa kakanninku ba, in dai suka yi hankali ga yin kome da na umarce su game da duka dokoki, ƙa’idodi da kuma farillai da na bayar ta wurin Musa.” 9 Amma Manasse ya sa Yahuda da mutanen Urushalima suka kauce, har suka aikata mugunta fiye da al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.
10 Ubangiji ya yi magana da Manasse da mutanensa, amma ba su kula ba.
Tsoffin Ƙasashen Ƙabilu Goma 678 kafin haihuwar Almasihu
Halin lardunan da ƙabilu goma suka mallaka a dā.
24 Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu. 25 Sa’ad da suka fara zama a can, ba su bauta wa Ubangiji ba; saboda haka ya aika da zakoki a tsakaninsu suka karkashe waɗansu mutane. 26 Sai aka faɗa wa sarkin Assuriya cewa, “Mutanen da ka kwashe ka zaunar a garuruwan Samariya fa ba su san abin da allahn ƙasar yake bukata ba. Saboda haka allahn ƙasar ya tura zakoki a cikinsu, waɗanda suke karkashe su, domin mutanen ba su san abin da yake bukata ba.”
27 Sai sarkin Assuriya ya ba da umarni cewa, “A sami wani daga cikin firistocin da aka kwaso zuwa bauta daga Samariya, yă koma yă zauna a can, yă koya wa mutanen abin da allahn ƙasar yake bukata.” 28 Saboda haka ɗaya daga cikin firistocin da aka kawo bauta daga Samariya ya dawo ya zauna a Betel, ya koya musu yadda za su yi sujada ga Ubangiji.
29 Duk da haka, jama’ar kowace ƙasa, suka ƙera tasu alloli a garuruwa masu yawa inda suke zaune, suka sa su a masujadan da mutanen Samariya suka gina a kan tuddai. 30 Mutane daga Babilon suka ƙera Sukkot Benot, mutane daga Kut suka ƙera Nergal, mutane daga Hamat suka ƙera Ashima; 31 Awwiyawa suka ƙera Nibhaz da Tartak, Sefarfayawa kuwa suka ƙone ’ya’yansu a wuta a matsayi hadayu ga Adrammelek da Anammelek allolin Sefarfayim. 32 Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka zaɓi mutanensu su yi musu hidima a matsayin firistoci a masujadan da suke kan tuddai. 33 Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma sun bauta wa allolinsu bisa ga al’adun ƙasashen da suka fito.
34 Har yă zuwa yau, sun nace da ayyukansu na dā. Ba sa yin wa Ubangiji sujada, ba sa kuma bin dokoki da farillansa, dokoki da umarnan da Ubangiji ya ba wa zuriyar Yaƙub, wadda ya ba wa suna Isra’ila. 35 Da Ubangiji ya ƙulla alkawari da Isra’ilawa, ya dokace su cewa, “Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada ko ku durƙusa a gabansu ku bauta musu, ko ku miƙa musu hadaya. 36 Amma Ubangiji wanda ya fito da ku daga Masar da iko mai girma da hannu mai ƙarfi, shi ne za ku yi masa sujada. Gare shi za ku durƙusa ku kuma miƙa masa hadayu. 37 Dole kullum ku mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da farillan, dokoki da umarnan da ya rubuta muku. Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada. 38 Kada ku manta da alkawarin da na ƙulla da ku, kada ku yi sujada ga waɗansu alloli. 39 Maimakon haka, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada; shi ne zai cece ku daga hannun abokan gābanku.”
40 Amma ba su saurara ba, suka nace da ayyukansu na dā. 41 Ko ma yayinda mutanen nan suke yi wa Ubangiji sujada, ba su daina bauta wa gumakansu ba. Har yă zuwa yau, ’ya’yansu da jikokinsu sun ci gaba da bin gurbin kakanninsu.