Yahuda Ya Yi Cinikin Cin Amanar Yesu

Yahuda, wanda tsautawar Yesu a wurin liyafar ta ɓata masa rai, ya yi ciniki da shugabanni domin ya ci amanarsa.

Daren Talata a Urushalima

30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mattiyu 26:14–16

26:14 Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci

15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.

16 Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.

Markus 14:10–11

14:10 Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su.

11 Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.

Luka 22:3–6

22:3 Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun.

4 Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su.

5 Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi.

6 Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, sa’ad da taro ba sa nan tare da shi.

Shirya Abincin Bikin Ƙetarewa a Gidan Aboki

Shirya abincin Bikin Ƙetarewa a gidan wani aboki (mai yiwuwa gidan mahaifin Yohanna Markus da mahaifiyarsa).

Urushalima, Alhamis da rana. (Ranar Shiri)

Mattiyu 26:17–19

26:17 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”

18 Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ”

19 Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.

Markus 14:12–16

14:12 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”

13 Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.

14 Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’

15 Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”

16 Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.

Luka 22:7–13

22:7 Sai ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato, ranar hadayar ɗan ragon kafara na Bikin Ƙetarewa.

8 Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewar da za mu ci.”

9 Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu yi shirin?”

10 Ya amsa ya ce, “Sa’ad da kuka shiga cikin gari, za ku sadu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga.

11 Ku ce wa maigidan, Malam ya aike mu mu ce maka, ‘Ina ɗakin baƙi, inda ni da almajiraina za mu ci abincin Bikin Ƙetarewa?’

12 Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. Nan za ku yi shirin.”

13 Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.

Yesu Ya Ci Abincin Bikin Ƙetarewa tare da Sha Biyun

Yesu ya ci abincin Bikin Ƙetarewa tare da manzanni goma sha biyu, ya kuma tsawata musu saboda kishinsu.

Urushalima, Alhamis da yamma bayan faɗuwar rana (farkon Juma'a ta Yahudawa)

Mattiyu 26:20

26:20 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.

Markus 14:17

14:17 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun.

Luka 22:14–16, 24–30

22:14 Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci.

15 Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala. 16 Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cinsa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.”

24 Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma. 25 Yesu ya ce musu, “Sarakunan Al’ummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane. 26 Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima. 27 Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku. 28 Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha. 29 Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku. 30 Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.