Yesu Ya Yi Annabcin Gicciye Shi Nan da Kwana Biyu

Yesu ya yi annabcin cewa za a gicciye shi nan da kwana biyu (a Juma'a ta Yahudawa).

Wataƙila a Betani da yammacin Talata (farkon Laraba ta Yahudawa). Shugabannin da ke Urushalima suna ƙulla makircin kashe shi

30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mattiyu 26:1–5

26:1 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa, 2 “Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”

3 Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas,

4 suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.

5 Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”

Markus 14:1–2

14:1 To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.

2 Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”

Luka 22:1–2

22:1 Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa,

2 manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane.

Maryamu ta Betani Ta Shafe Yesu da Mai Domin Binnewarsa

A wurin liyafa a gidan Siman kuturu, Maryamu ta Betani ta shafe Yesu da mai domin binnewarsa.

A Betani (yammacin Talata, Laraba ta Yahudawa)

Mattiyu 26:6–13

26:6 Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, 7 wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.

8 Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!

9 Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”

10 Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.

11 Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.

12 Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata.

13 Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

Markus 14:3–9

14:3 Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.

4 Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka?

5 Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”

6 Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.

7 Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.

8 Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata.

9 Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”

Yohanna 12:2–8

12:2 A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi. 3 Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.

4 Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce,

5 “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.”

6 Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki.

7 Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata.

8 Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.”