Ayuba Ya Bayyana Rashin Laifinsa

2130 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ayuba 16–17

1 Sai Ayuba ya amsa,

2 “Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan;

dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!

3 Dogayen surutanku ba sa ƙare ne?

Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?

4 Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi

in da kuna cikin halin da nake;

zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi,

in kaɗa muku kaina.

5 Amma bakina zai ƙarfafa ku;

ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku.

6 “Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi;

in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.

7 Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni;

ka ɓata gidana gaba ɗaya.

8 Ka daure ni, ya kuma zama shaida;

yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.

9 Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa

yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni;

ya zura mini ido.

10 Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni;

suka yi mini ba’a

suka haɗu suka tayar mini.

11 Allah ya bashe ni ga mugayen mutane,

ya jefa ni hannun mugaye.

12 Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai;

amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya;

ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;

13 maharbansa sun kewaye ni.

Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata

har jini ya zuba a ƙasa.

14 Ya ji mini rauni a kai a kai

ya auko mini kamar mai yaƙi.

15 “Ina makoki saye da tsummoki

na ɓoye fuskata a cikin ƙura.

16 Fuskata ta yi ja don kuka

idanuna sun kukumbura;

17 duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba

kuma addu’ata mai tsabta ce.

18 “Ya duniya, kada ki ɓoye jinina;

bari yă yi kuka a madadina!

19 Ko yanzu haka shaidata tana sama;

wanda zai tsaya mini yana sama.

20 Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne

yayinda nake kuka ga Allah;

21 a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah

kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.

22 “Shekaru kaɗan suka rage

in kama hanyar da ba a komawa.

17:1 Na karaya,

kwanakina sun kusa ƙarewa,

kabari yana jirana.

2 Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni;

idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.

3 “Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari.

Wane ne zai kāre ni?

4 Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba,

saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.

5 In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada

’ya’yansa za su makance.

6 “Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai

wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska.

7 Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki;

jikina ya zama kamar inuwa kawai

8 Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro;

marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah.

9 Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu,

waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.

10 “Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa!

Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku.

11 Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci

haka kuma abubuwan da zuciyata take so.

12 Mutanen nan sun juya rana ta zama dare.

A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’

13 In kabari ne begen da nake da shi kaɗai,

in na shimfiɗa gadona a cikin duhu,

14 In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’

tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’

15 To, ina begena yake?

Wane ne zai iya ganin wani bege domina?

16 Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne?

Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?”