Bildad Ya Amsa wa Ayuba

2130 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ayuba 18

1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

2 “Yaushe za ka gama maganganun nan?

Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.

3 Don me muke kamar shanu a wurinka,

ka ɗauke mu mutanen wofi?

4 Kai da ka yayyage kanka don haushi,

za a yashe duniya saboda kai ne?

Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?

5 “An kashe fitilar mugu;

harshen wutarsa ya daina ci.

6 Wutar cikin tentinsa ta zama duhu;

fitilar da take kusa da shi ta mutu.

7 Ƙarfin takawarsa ya ragu;

dabararsa ta ja fāɗuwarsa.

8 Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga,

yana ta yawo a cikin ragar.

9 Tarko ya kama ɗiɗɗigensa;

tarko ya riƙe shi kam.

10 An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa;

an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.

11 Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe

yana bin shi duk inda ya je.

12 Masifa tana jiransa;

bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.

13 Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa;

ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.

14 An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa

aka sa shi tsoro sosai.

15 Wuta ta cinye tentinsa;

farar wuta ta rufe wurin da yake zama.

16 Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa

rassansa sun mutu a sama.

17 An manta da shi a duniya;

ba wanda yake ƙara tunawa da shi.

18 An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu,

an kore shi daga duniya.

19 Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa,

ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.

20 Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi;

tsoro ya kama mutanen gabas.

21 Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake,

haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”

Ayuba Ya Koka Saboda Zaluncin Abokansa

Ayuba 19

1 Sai Ayuba ya amsa,

2 “Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba

ku kuma murƙushe ni da maganganunku?

3 Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni,

kuna kai mini hari na rashin kunya.

4 In gaskiya ne na yi laifi,

kuskurena ya rage nawa.

5 In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina

kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne,

6 sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba

ya kewaye ni da ragarsa.

7 “Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba;

ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba.

8 Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba;

ya rufe hanyata da duhu.

9 Ya cire darajar da nake da ita,

ya kuma cire rawani daga kaina.

10 Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare;

ya tuge begen da nake da shi kamar itace.

11 Yana jin haushina

ya lissafta ni cikin maƙiyansa.

12 Rundunarsa ta zo da ƙarfi;

suka kafa sansani kewaye da ni,

suka zagaye tentina.

13 “Ya raba ni da ’yan’uwana maza;

abokaina sun zama baƙi gare ni.

14 Dangina sun tafi;

abokaina na kurkusa sun manta da ni.

15 Waɗanda sukan ziyarce ni,

da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.

16 Na kira bawana, amma bai amsa ba,

ko da yake na roƙe shi da bakina.

17 Numfashina yana ɓata wa matata rai;

’yan’uwana sun ƙi ni.

18 Har ’yan yara suna rena ni;

in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.

19 Duk abokaina sun yashe ni;

waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.

20 Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi,

da ƙyar na tsira.

21 “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina,

gama hannun Allah ya sauko a kaina.

22 Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi?

Ba ku gaji da yagar fatata ba?

23 “Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna,

da an rubuta su a littafi,

24 a rubuta su da ƙarfe a kan dutse

don su dawwama har abada!

25 Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai,

kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.

26 Kuma bayan an hallaka fatata,

duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.

27 Zan gan shi da kaina

da idanuna, Ni, ba wani ba ne.

Zuciyata ta cika da wannan tunani!

28 “In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini,

tun da shi ne tushen damuwa,’

29 sai ku ma ku ji tsoron takobin;

gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi,

sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”