An Annabta Wahalar Urushalima da Halakarta

595 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ezekiyel 3:22–5:17

22 Hannun Ubangiji ya kasance a kaina a can, ya kuma ce mini, “Tashi ka fita zuwa fili, a can kuwa zan yi maka magana.” 23 Saboda haka na tashi da tafi fili. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tsaya a can, kamar ɗaukakar da na gani kusa da Kogin Kebar, sai na fāɗi rubda ciki.

24 Sai Ruhu ya sauko a kaina ya kuma ɗaga ni na tsaya a ƙafafuna. Ya yi mini magana ya ce, “Ka fita, ka rufe kanka a cikin gida. 25 Kuma kai, ɗan mutum, za su ɗaura ka da igiyoyi; za a daure ka yadda ba za ka iya fita a cikin mutane ba. 26 Zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka yi shiru ka kuma kāsa tsawata musu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne. 27 Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na ’yan tawaye.

4:1 “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki tubalin yumɓu, ka ajiye shi a gabanka ka kuma zāna birnin Urushalima a kansa. 2 Sa’an nan ka yi mata ƙawanya. Ka kafa mata katangar ƙawanya, ka gina katangar da ɗan tudu ka kewaye ta da dundurusai. 3 Sa’an nan ka ɗauki kwanon ƙarfe, ka shirya shi kamar katangar ƙarfe tsakaninka da birnin ka kuma zuba mata ido. Za tă kasance a ƙarƙashin ƙawanya, kai kuwa za ka yi mata ƙawanya. Wannan zai zama alama ga gidan Isra’ila.

4 “Sa’an nan ka kwanta a hagunka ka kuma sa zunubin gidan Isra’ila a kanka. Za ka ɗauki zunubinsu na waɗansu kwanakin da kake kwance a gefenka. 5 Na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun zunubinsu. Saboda haka cikin kwana 390 za ka ɗauki zunubin gidan Isra’ila.

6 “Bayan ka gama haka, ka sāke kwantawa, a wannan lokaci a gefen damarka, ka kuma ɗauki zunubin gidan Yahuda. Na ɗora maka kwanaki 40, kwana guda a madadin shekara guda. 7 Ka juya fuskarka wajen ƙawanyar Urushalima da hannunka a buɗe ka yi annabci a kanta. 8 Zan ɗaura ka da igiyoyi don kada ka juya daga wannan gefe zuwa wani gefe sai ka gama kwanakin ƙawanyarka.

9 “Ka ɗauki alkama da sha’ir, wake da acca, gero da maiwa; ka sa su a tulun ajiya ka kuma yi amfani da su don yin burodi wa kanka. Za ka ci shi a kwanaki 390 da za ka kwanta a gefenka. 10 Ka auna shekel ashirin na abinci don kowace rana ka kuma ci shi a ƙayyadadden lokaci. 11 Haka ma ka auna kashi ɗaya bisa shida na garwan ruwa ka sha shi a ƙayyadadden lokaci. 12 Ka ci abinci yadda za ka ci ƙosai sha’ir, ka gasa shi a gaban mutane, ka yi amfani da najasar mutane kamar itacen wuta.” 13 Ubangiji ya ce, “Ta haka mutanen Isra’ila za su ci ƙazantaccen abinci a cikin al’ummai inda zan kore su in kai.”

14 Sai na ce, “Ba haka ba ne, Ubangiji Mai Iko Duka! Ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Daga ƙuruciyata har zuwa yanzu ban taɓa cin wani abin da aka samu ya mutu ko abin da namun jeji suka kashe ba. Ba nama marar tsabtan da ya taɓa shiga bakina.”

15 Sai ya ce, “To da kyau, zan bari ka gasa burodin a kan kashin shanu a maimakon najasar mutane.”

16 Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, zan yanke tanadin abinci a Urushalima. Mutane za su auna abincin da za su ci da tsoro su kuma auna ruwan da za su sha cikin fargaba, 17 domin abinci da ruwa za su kāsa. Za su damu da ganin juna za su kuma lalace saboda zunubinsu.

5:1 “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki takobi mai kaifi ka kuma yi amfani da shi kamar rezan mai aski don askin kanka da gemunka. Sa’an nan ka ɗauki ma’auni ka kuma raba gashin. 2 Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre. 3 Amma ka ɗibi gashi kaɗan ka daure a shafin rigarka. 4 Har yanzu, ka ɗibi kaɗan na waɗannan ka zuba su cikin wuta su kuma ƙone. Wuta zai bazu daga nan zuwa dukan gidan Isra’ila.

5 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Urushalima ce wannan, wadda na kafa a tsakiyar al’ummai, da ƙasashe kewaye da ita a ko’ina. 6 Duk da haka cikin muguntarta ta yi tayarwa a kan dokokina da ƙa’idodina fiye da al’ummai da ƙasashe kewaye da ita. Ta ƙi dokokina ba tă kuwa bi ƙa’idodina ba.

7 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce kin yi ƙin ji fiye da al’umman da suke kewaye da ke ba ki kuma bi ƙa’idodina ko ki kiyaye dokokina ba. Ba ki ma dace da matsayin al’umman da suke kewaye da ke ba.

8 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Ni kaina ina gāba da ke, Urushalima, kuma zan hukunta ki a gaban al’ummai. 9 Saboda dukan gumakan banƙyamarki, zan yi abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan ƙara yinsa ba. 10 Saboda haka a cikinki ubanni za su ci ’ya’yansu, ’ya’ya kuma za su ci ubanninsu. Zan hukunta ki zan kuma watsar da dukan waɗanda suke tsira da suke naki a iska. 11 Saboda haka muddin ina a raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin kin ƙazantar da wuri mai tsarkina da dukan mugayen siffofinki da kuma ayyukanki masu banƙyama, ni kaina zan janye alherina; ba zan ji tausayinki ko in haƙura da ke ba. 12 Kashi ɗaya bisa uku na mutanenki za su mutu da annoba ko su mutu da yunwa a cikinki; kashi ɗaya bisa uku takobi ne zai kashe su a waje da katangarki; kashi ɗaya bisa uku kuma zan watsar a iska in kuma fafare su da takobin da aka zāre.

13 “Sa’an nan ne fushina zai huce hasalata a kanki kuma ta lafa, in kuma wartsake. Kuma sa’ad da na zuba fushina a kansu, a sa’an nan ne za su san cewa Ni Ubangiji na yi magana a cikin fushin kishina a kansu.

14 “Zan mai da ki kufai da kuma abin dariya a cikin al’ummai kewaye da ke, a gaban dukan waɗanda suke wucewa. 15 Za ki zama abin dariya da abin ba’a, kashedi da abin banrazana ga al’ummai kewaye da ke sa’ad da na hukunta ki cikin fushi da cikin hasala da kuma tsawatawa mai zafi. Ni Ubangiji na faɗa. 16 Sa’ad da na harbe ki da mugayen kibiyoyina da kuma kibiyoyi masu hallakarwa na yunwa, zan yi harbi don in kashe ki. Zan kawo ƙarin yunwa a kanki in kuma yanke tanadin abincinki. 17 Zan aika da yunwa da namun jeji a kanki, za su kuma bar ku ba ’ya’ya. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki, zan kuma kawo takobi a kanki. Ni Ubangiji na faɗa.”