An Annabta Wahalar Urushalima da Halakarta (continued)

595 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ezekiyel 6–7

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Ɗan mutum, ka kafa idonka a kan duwatsun Isra’ila; ka yi annabci a kansu 3 ka ce, ‘Ya ku duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa duwatsu da tuddai, ga rafuffuka da kuma kwaruruka. Ina shirin kawo takobi a kanku, kuma zan hallaka masujadanku. 4 Za a ragargaza bagadanku a kuma farfasa bagadanku na ƙone turare; zan kuma kashe mutanenku a gaban gumakanku. 5 Zan shimfiɗa gawawwakin Isra’ilawa a gaban gumakansu, in kuma watsar da ƙasusuwanku kewaye da bagadanku. 6 Duk inda kuke zama, garuruwa za su zama kango, za a kuma ragargaza masujadai, saboda bagadanku su rurrushe su zama kango, a kuma farfasa gumakanku su lalace, za a rurrushe bagadan ƙone turarenku, a kuma shafe dukan abin da kuka yi. 7 Za a kashe mutanenku a cikinku, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

8 “ ‘Amma zan bar waɗansu, gama waɗansunku za su tsere wa takobi sa’ad da aka watsar da ku a cikin ƙasashe da al’ummai. 9 Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata. 10 Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji; ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.

11 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ku tafa hannuwanku tare ku kuma taka ƙafafunku ku yi ihu ku ce, “Kaito!” Saboda dukan mugaye da kuma abubuwan banƙyama na gidan Isra’ila, gama za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba. 12 Wanda yake da nisa zai mutu da annoba, shi da yake kusa kuma zai mutu ta takobi, wanda kuma ya tsira aka kuma bari zai mutu da yunwa. Ta haka zan aukar da fushina a kansu. 13 Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakin mutanensu suna kwance a kusa da gumakansu da kewaye da bagadansu, a kowane kan tudu mai tsawo da kuma a kan dukan kan duwatsu, a ƙarƙashin kowane inuwar itace da kuma kowane oak mai ganye, wuraren da suke ƙone turare masu ƙanshi wa dukan gumakansu. 14 Zan kuma miƙa hannuna a kansu in mai da ƙasarsu kango daga hamadan Dibila, a duk inda suke zama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

7:1 Maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa, 2 “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila,

“ ‘Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo

a kan kusurwoyi huɗu na ƙasar.

3 Ƙarshe yanzu yana a kanki.

Zan fashe fushina a kanki.

Zan shari’anta ki bisa ga halinki

in sāka miki kuma saboda dukan ayyukan banƙyamar da kika yi.

4 Ba zan dube ki da tausayi;

ko in ƙyale ki ba.

Tabbatacce zan sāka miki saboda halinki

da kuma ayyukanki masu banƙyama a cikinki.

Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji.’

5 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,

“ ‘Masifa! Masifar da ba a taɓa gani ba

tana zuwa.

6 Ƙarshe ya zo!

Ƙarshe ya zo!

Ya farka a kanki.

Ga shi, ya zo!

7 Ƙaddara ta auko miki,

ya ke wadda ke zama cikin ƙasar.

Lokaci ya yi, rana ta gabato;

akwai fargaba, ba farin ciki ba, a kan duwatsu.

8 Ina gab da fasa hasalata a kanki

in kuma aukar da fushina a kanki;

zan shari’anta ke bisa ga halinki

in kuma sāka miki saboda dukan ayyukanki masu banƙyama.

9 Ba zan dube ki da tausayi

ko in ƙyale ke ba;

zan sāka miki bisa ga halinki

da kuma ayyukan masu banƙyama a cikinki.

Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji wanda yake bugunki.

10 “ ‘Ga shi ranar ta zo!

Ta iso!

Ƙaddararki ta keto,

sandar ta yi toho,

girman kai ya yi fure!

11 Rikici ya yi girma ya zama

sandar da za a hukunta mugunta;

babu wani daga cikin mutanen da za a bari,

babu wani dukiyarsu da za a bari,

babu wani abin amfani.

12 Lokaci ya yi!

Ranar ta gabato!

Kada mai saya ya yi farin ciki

ko kuwa mai sayarwa ya yi baƙin ciki,

gama hasala tana a kan dukan jama’a.

13 Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba

muddin dukansu suna da rai, gama ba za a sauya wahayin da ya shafi dukan jama’a ba.

Saboda zunubansu, babu ɗayansu da zai adana ransa.

14 “ ‘Ko da yake suna busa ƙaho suna kuma shirya kome,

ba wanda zai tafi yaƙi, gama hasalata tana a kan dukan jama’a.

15 A waje takobi ne,

a ciki annoba ne da yunwa;

waɗanda suke fili za su mutu ta wurin takobi,

waɗanda kuma suke cikin birni yunwa da annoba za su cinye su.

16 Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu,

suna kuka kamar kurciyoyin kwaruruka,

kowanne saboda zunubansa.

17 Kowane hannu zai raunana,

kowace gwiwa kuma za tă zama marar ƙarfi kamar ruwa.

18 Za su sa tufafin makoki su kuma rufu da fargaba.

Fuskokinsu kuma za su rufu da kunya a kuma aske kawunansu.

19 “ ‘Za su zubar da azurfarsu a tituna,

zinariyarsu kuma za tă zama ƙazantacciyar aba.

Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu

a ranar hasalar Ubangiji ba.

Ba za su ƙosar da yunwansu ko su cika cikinsu da shi ba,

gama su ne sanadin tuntuɓensu cikin zunubi.

20 Sun yi fariya kyan kayan adonsu

suka kuma yi amfani da su don su yi gumakansu masu banƙyama,

da ƙazantattun abubuwa.

21 Zan ba da su duka kamar ganima ga baƙi

da kuma kamar abin da aka washe ga mugayen duniya,

za su kuma ƙazantar da su.

22 Zan juye fuskata daga gare su,

za su kuwa ƙazantar da wurina mai daraja;

’yan fashi za su shiga

su kuma ƙazantar da shi.

23 “ ‘Ka shirya sarƙoƙi,

domin ƙasar ta cika da alhakin jini,

birnin kuma ya cika da rikici.

24 Zan kawo al’ummai mafi mugunta su mallaki gidajenku;

zan kawo ƙarshen fariyar masu ƙarfi,

Wurare Masu Tsarkinsu za su ƙazantu.

25 Sa’ad da wahala ta zo,

za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.

26 Masifa a kan masifa za su zo,

jita-jita kuma a kan jita-jita.

Za su yi ƙoƙarin samun wahayi daga annabi;

koyarwar doka ta wurin firist

za tă ɓace,

kamar yadda shawarar dattawa za tă ɓace.

27 Sarki zai yi makoki, yerima zai fid da zuciya,

hannuwan mutanen ƙasar kuma za su yi rawa.

Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su bisa ga ma’auninsu.

Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”