Irmiya Ya Tsauta wa Mutanen Saboda Ja da Baya

Irmiya ya tsauta wa mutanen saboda ja da bayansu bayan gyare-gyaren Yosiya.

612 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Irmiya 3:6–25

6 A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can. 7 Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani. 8 Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina. 9 Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace. 10 Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji.

11 Ubangiji ya ce mini, “Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci. 12 Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa,

“ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji,

‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba,

gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji,

‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.

13 Ki dai yarda da laifinki

kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye,

kin watsar da alheranki ga baƙin alloli

a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa,

ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ”

in ji Ubangiji.

14 “Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. 15 Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi. 16 A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. 17 A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba. 18 A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.

19 “Ni kaina na faɗa,

“ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza

in ba ki ƙasa mai daɗi,

gādo mafi kyau da wata al’umma.’

Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’

ba za ki ƙara rabuwa da bina ba.

20 Amma kamar mace marar aminci ga mijinta,

haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,”

in ji Ubangiji.

21 An ji kuka a filayen tuddai,

kuka da roƙon mutanen Isra’ila,

domin sun lalace hanyoyinsu

sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.

22 “Ku komo, mutane marasa bangaskiya;

zan warkar da ku daga ja da bayanku.”

“I, za mu zo wurinka,

gama kai ne Ubangiji Allahnmu.

23 Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai

da duwatsu banza ne;

tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne

akwai ceton Isra’ila.

24 Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu

amfanin wahalar kakanninmu

garkunan tumakinsu da na awakinsu,

yaransu maza da mata.

25 Bari mu kwanta mu sha kunya,

bari kuma kunyarmu ta rufe mu.

Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi,

da mu da kakanninmu;

daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau

ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba.”

Irmiya Ya Hango Baƙin Cikin Zaman Bauta

Irmiya, a matsayinsa na annabi, ya bayyana tun da wuri baƙin cikin zaman bautar da ke zuwa.

Irmiya 4

1 “In za ka komo, ya Isra’ila,

ka komo gare ni,”

in ji Ubangiji.

“In ka kau da gumakanka masu banƙyama daga gabana

ba ka ƙara karkace ba,

2 kuma in cikin gaskiya da adalci

ka rantse, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’

to al’ummai za su sami albarka ta wurinsa

kuma a cikinsa za su ɗaukaka.”

3 Ga abin da Ubangiji yana ce wa mutanen Yahuda da kuma na Urushalima.

“Ku nome ƙasarku

kuma kada ku yi shuka cikin ƙayayyuwa.

4 Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangiji

ku yi wa zukatanku kaciya,

ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima,

in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wuta

saboda muguntar da kuka aikata

za tă ci ba wanda zai kashe ta.

5 “Ku yi shela a Yahuda ku kuma furta a Urushalima ku ce,

‘Ku busa ƙaho a ko’ina a ƙasar!’

Ku tā da murya da ƙarfi ku ce,

‘Ku tattaru!

Bari mu gudu zuwa birane masu katanga!’

6 Ku tā da tuta don zuwa Sihiyona!

Ku gudu ku nemi mafaka ba tare da jinkiri ba!

Gama ina kawowa masifa daga arewa,

mummunan hallaka kuwa.”

7 Zaki ya fito daga ruƙuƙinsa;

mai hallakarwar al’ummai ya kama hanya.

Ya bar wurinsa

don yă lalace ƙasarku.

Garuruwanku za su zama kufai

babu mazauna.

8 Saboda haka ku yafa tufafin makoki,

ku yi makoki da kuka,

gama fushin Ubangiji

bai juye daga gare mu ba.

9 “A wannan rana,” in ji Ubangiji,

“sarki da shugabanni za su fid da zuciya,

firistoci za su razana,

annabawa kuma za su yi mamaki.”

10 Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka, yaya ka ruɗi mutanen nan da kuma Urushalima gaba ɗaya haka ta wurin cewa, ‘Za ku zauna lafiya,’ sa’ad da takobi yana a maƙogwaronmu.”

11 A lokacin za a faɗa wa mutanen nan da kuma Urushalima cewa, “Iska mai zafi daga tuddan hamada za tă hura zuwa wajen mutanena, amma ba don ta sheƙe ko ta rairaye; ba; 12 iska mafificin ƙarfi da ta fito daga gare ni. Yanzu na zartar da hukuncina a kansu.”

13 Duba! Yana zuwa kamar gizagizai,

kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa,

dawakansa sun fi gaggafa sauri.

Kaiton mu! Mun shiga uku!

14 Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki ki sami ceto.

Har yaushe za ki zauna riƙe da mugayen tunani?

15 Murya ta shela daga Dan,

tana furtawa masifa daga tuddan Efraim.

16 “A faɗa wa al’ummai wannan,

a furta wannan game Urushalima.

‘Sojoji masu ƙawanya suna zuwa daga ƙasa mai nisa,

suna tā da kirarin yaƙi a kan biranen Yahuda.

17 Sun kewaye ta kamar masu gadin fili,

domin ta yi mini tawaye,’ ”

in ji Ubangiji.

18 “Halinki da ayyukanki

sun kawo wannan a kanki.

Hukuncinki ke nan.

Yana da ɗaci!

Ya soke ki har zuciyarki!”

19 Azabana, azabana!

Ina birgima cikin zafi.

Azabana, azabar zuciyata!

Zuciyata yana bugu a cikina,

Ba zan yi shiru ba.

Gama na ji karan ƙaho;

na ji kirarin yaƙi.

20 Masifa kan masifa;

dukan ƙasar ta zama kufai.

Cikin ɗan lokaci aka rurrushe tentuna nawa,

mafakata ba zato.

21 Har yaushe zan dubi tutar yaƙi

in kuma ji karar ƙaho?

22 “Mutanena wawaye ne;

ba su san ni ba.

Su ’ya’ya ne marasa azanci;

ba su da fahimi.

Suna da dabarar aikata mugunta;

ba su san yadda za su aikata alheri ba.”

23 Na dubi duniya,

na ga cewa marar siffa ce babu kome;

sammai kuma,

haskensu ya tafi.

24 Na dubi duwatsu,

sai na ga suna makyarkyata;

dukan tuddai kuwa suna lilo.

25 Na duba, sai na ga ba kowa;

kowane tsuntsu a sarari da ya tsere.

26 Na duba, sai na ga ƙasa mai amfani ta zama hamada;

dukan garuruwanta sun zama kufai

a gaban Ubangiji, a gaban zafin fushinsa.

27 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Dukan ƙasar za tă zama kufai,

ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba.

28 Saboda haka duniya za tă yi kuka

sammai a bisa kuma za su yi duhu,

domin na yi magana kuma ba zan fasa ba,

na yanke shawara ba kuwa zan janye ba.”

29 Da jin motsin mahayan dawakai da maharba

kowane gari ya ruga da gudu.

Waɗansu suka shiga kurmi;

waɗansu suka hau cikin duwatsu.

Dukan garuruwan sun fashe tas;

babu wani da yake zama a ciki.

30 Me kike yi, ya wadda aka ragargaza?

Me ya sa kika sanya mulufi

kika sa kayan adon zinariya?

Me ya sa kika sa wa idanunki tozali?

Kin yi kwalliyarki a banza.

Masoyanki sun bar ki;

suna neman ranki.

31 Na ji kuka kamar na mace mai naƙuda,

nishi kamar na wadda take haihuwa ɗanta na fari,

kukan Diyar Sihiyona tana haki, da ƙyar take numfashi,

tana miƙa hannuwanta tana cewa,

“Wayyo ni kaina! Na suma;

an ba da raina ga masu kisana.”