Irmiya Ya Yi Annabci a Kan Masar

587 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Irmiya 43:8–13

8 A Tafanes maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa, 9 “Yayinda Yahudawa suna kallo, ka ɗauki waɗansu manyan duwatsu tare da kai ka kuma binne su cikin yumɓu a tubalin dakalin ƙofar shiga fadar Fir’auna a Tafanes. 10 Sa’an nan ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, zan aika wa bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon, zan kuma sa kursiyinsa a kan waɗannan duwatsun da na binne a nan; zai fadada bukkar mulkinsa a bisansu. 11 Zai zo ya yaƙi Masar, ya kawo mutuwa ga waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa, zaman bauta ga waɗanda aka ƙaddara musu zaman bauta, da kuma takobi ga waɗanda aka ƙaddara su mutu ta takobi. 12 Zai sa wuta wa haikalan allolin Masar; zai ƙone haikalansu yă kuma kwashe allolinsu bayi. Kamar yadda makiyayi yakan yafa mayafinsa kewaye da shi, haka zai yafa Masar kewaye da kansa ya kuma tashi a wurin babu abin da ya same shi. 13 A can cikin haikalin rana a Masar zai rushe al’amudan duwatsu yă kuma ƙone haikalan allolin Masar.’ ”

Irmiya 46:13–28

13 Ga saƙon da Ubangiji ya yi wa Irmiya annabi game da zuwan Nebukadnezzar sarkin Babilon don yă yaƙi Masar.

14 “Ka yi shelar wannan a Masar, ka kuma furta shi a Migdol;

ka yi shelarsa kuma a Memfis da Tafanes.

‘Ku ɗauki matsayinku ku kuma shirya,

gama takobi na cin waɗanda suke kewaye da ku.’

15 Me zai sa a wulaƙanta jarumawanka haka?

Ba za su iya tsayawa ba, gama Ubangiji zai ture su ƙasa.

16 Za su yi ta tuntuɓe;

za su fāɗi akan juna.

Za su ce, ‘Mu tashi, mu koma

zuwa wurin mutanenmu da kuma ƙasashenmu,

daga takobin masu danniya.’

17 A can za su tā da murya su ce,

‘Fir’auna sarkin Masar mai yawan surutu ne kawai;

ya bar zarafi ya wuce masa.’

18 “Muddin ina raye,” in ji Sarki,

wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki,

“wani zai ɓullo wanda yake kamar Tabor a cikin duwatsu,

kamar Karmel kusa da teku.

19 Ku tattara kayanku don shirin zuwa zaman bauta,

ku da kuke zama a Masar,

gama Memfis za tă zama kufai

ta zama kango, babu mazauna.

20 “Masar kyakkyawar karsana ce,

amma bobuwa tana zuwa a kanta daga arewa.

21 Sojojin da ta yi hayarsu a cikinta

suna kamar ’yan maruƙa masu kitse.

Su ma za su juya su kuma gudu gaba ɗaya,

ba za su iya tsayawa ba,

gama ranar masifa tana zuwa a kansu,

lokacin da za su sha hukunci.

22 Masar za tă yi huci kamar macijin da yake gudu

yayinda abokin gāba yana matsowa da ƙarfi;

za su fāɗo mata gatura

kamar mutanen da suke saran itatuwa.

23 Za su sari kurminta,” in ji Ubangiji,

“ko da yake yana maƙare da itatuwa.

Sun fi fāra yawa,

ba su ƙidayuwa.

24 Za a kunyatar da Diyar Masar,

da aka bashe ga mutanen arewa.”

25 Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ina gab da kawo hukunci a kan allahn Amon na Tebes, a kan Fir’auna, a kan Masar da allolinta da sarakunanta, da kuma a kan waɗanda suka dogara ga Fir’auna. 26 Zan ba da su ga waɗanda suke neman ransu, ga Nebukadnezzar sarkin Babilon da fadawansa. Amma daga baya, Masar za tă kasance da mazauna kamar dā,” in ji Ubangiji.

27 “Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana;

kada ka karai, ya Isra’ila.

Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nisa,

zuriyarka daga ƙasar bautarsu.

Yaƙub zai sāke kasance cikin salama, rai kwance,

babu kuma wanda zai sa ya ji tsoro.

28 Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana,

gama ina tare da kai,” in ji Ubangiji.

“Ko da na hallaka dukan al’ummai sarai

inda na kora ka, ba zan hallaka ka sarai ba.

Zan hore ka amma da adalci kaɗai;

ba zan bar ka ba hukunci ba.”

Annabce-annabcen Ƙarshe na Irmiya a Kan Masu Bautar Gumaka

Annabce-annabcen ƙarshe na Irmiya a kan Yahudawan da suke bautar gumaka, da kuma a kan Masar.

Irmiya 44

1 Wannan maganata zo wa Irmiya game da dukan Yahudawa masu zama a Masar ta Ƙasa, a Migdol, Tafanes da Memfis, da kuma a Masar ta Bisa. 2 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa kun ga masifa mai girmar da na kawo a kan Urushalima da kuma a kan dukan garuruwan Yahuda. A yau sun zama hamada da kuma kango 3 saboda muguntar da suka aikata. Sun tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙone turare da kuma ta wurin bauta wa waɗansu allolin da su ko ku ko kakanninku ba su taɓa sani ba. 4 Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’ 5 Amma ba su saurara ko su kasa kunne ba; ba su juye daga muguntarsu ko su daina ƙone turare wa waɗansu alloli ba. 6 Saboda haka, fushina mai ƙuna ya fāɗo a kan garuruwan Yahuda da kuma titunan Urushalima na kuma mai da su kufai da suke a yau.

7 “To, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa don me kuka kawo irin masifa mai girma haka a kanku ta wurin warewa daga Yahuda maza da mata, yara da jarirai, kun kuma bar kanku babu raguwa? 8 Me ya sa kuka tsokane ni in yi fushi saboda abin da hannuwanku suka yi, kuna ƙone turare wa waɗansu alloli a Masar, inda kuka zo don ku zauna? Za ku hallakar da kanku ku kuma mai da kanku abin la’ana da abin zargi da abin ba’a a cikin dukan al’umman duniya. 9 Kun manta mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakuna da sarauniyoyin Yahuda da mugayen ayyukanku, da na matanku a cikin Yahuda da kan titunan Urushalima? 10 Har yă zuwa yau ba su ƙasƙantar da kansu ko su nuna bangirma, ko su kiyaye dokata da ƙa’idodin da na sa a gabanku da kakanninku ba.

11 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa na ƙudura in aukar muku da masifa in kuma hallaka dukan Yahuda. 12 Zan ɗauke raguwar Yahuda waɗanda suka ƙudurta su je Masar su zauna a can. Duk za su hallaka a Masar; za su mutu ta wurin takobi ko su mutu da yunwa. Daga ƙarami zuwa babba, za su mutu ta wurin takobi ko yunwa. Za su zama abin zarge da abin tsoro, abin la’ana da abin ba’a. 13 Zan hukunta waɗanda suke zama a Masar da takobi, yunwa da annoba, yadda na hukunta Urushalima. 14 Babu wani daga raguwar Yahuda wanda ya tafi Masar da zai kuɓuta ko ya tsira har ya komo zuwa ƙasar Yahuda, wadda za su yi marmari su komo su zauna; babu wani da zai komo sai dai ’yan gudun hijira.”

15 Sai dukan mazan da suka san cewa matansu suna ƙone turare wa waɗansu alloli, tare da dukan matan da suke a nan babban taro, da kuma dukan mutanen da suke zama a Masar ta Ƙasa da ta Bisa, suka ce wa Irmiya, 16 “Ba za mu saurari saƙon da ka yi mana magana a sunan Ubangiji ba! 17 Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa. 18 Amma tun da muka daina ƙone turare ga Sarauniyar Sama da kuma miƙa mata hadayun sha, muka rasa kome muna ta mutuwa ta wurin takobi da yunwa.”

19 Matan suka ƙara da cewa, “Sa’ad da muka ƙone turare ga Sarauniyar Sama muka kuma miƙa mata hadayun sha, mazanmu ba su san muna yin waina kamar siffarta muna kuma miƙa mata hadayun sha ba?”

20 Sai Irmiya ya ce wa dukan mutanen, maza da mata, waɗanda suke ba shi amsa, 21 “Ubangiji bai tuna ya kuma yi tunani game da turaren da aka ƙone a garuruwan Yahuda da kan titunan Urushalima wanda ku da kakanninku, sarakunanku da fadawanku da mutanen ƙasar ba ne? 22 Sa’ad da Ubangiji bai iya jurewa da mugayen ayyukanku da kuma abubuwa banƙyama da kuka aikata ba, sai ƙasarku ta zama abin la’ana da kufai babu mazauna yadda yake a yau. 23 Domin kun ƙone turare kuka kuma yi wa Ubangiji zunubi ba ku kuma yi masa biyayya ko ku kiyaye dokarsa ko ƙa’idodinsa ko farillansa ba, wannan masifa ta aukar muku, yadda yanzu kuka gani.”

24 Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane, har da mata, “Ku saurari maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda a Masar. 25 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku da matanku kun nuna ta wurin ayyukanku abin da kuka yi alkawari sa’ad da kuka ce, ‘Lalle za mu yi abin da muka yi alkawari na ƙone turare da kuma miƙa hadayun sha ga Sarauniyar Sama.’

“To, sai ku ci gaba, ku aikata abin da kuka yi alkawari! Ku cika alkawarinku! 26 Amma ku ji maganar Ubangiji, dukan Yahudawan da suke zama a Masar, ‘Na rantse da sunana,’ in ji Ubangiji, ‘cewa babu wani daga Yahuda wanda yake zama a ko’ina a Masar zai ƙara kira bisa sunana ko ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji Mai Iko Duka yana raye.” 27 Gama ina lura da su don lahani, ba alheri ba; mutanen Yahuda da suke a Masar za su hallaka ta wurin takobi da yunwa sai dukansu sun hallaka. 28 Waɗanda suka kuɓuta wa takobi suka komo zuwa ƙasar Yahuda daga Masar za su zama kima kawai. Sa’an nan dukan raguwar Yahuda waɗanda suka zo don su yi zama a Masar za su san maganar wane ne za tă tabbata, tawa ko tasu.

29 “ ‘Wannan zai zama alama a gare ku cewa zan hukunta ku a wannan wuri,’ in ji Ubangiji, ‘saboda ku san cewa barazanata ta lahani a kanku tabbatacce za tă cika.’ 30 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan bayar da Fir’auna Hofra sarkin Masar ga abokan gābansa waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, abokin gāban da ya nemi ransa.’ ”

An Ba da Labarin Yadda Nebukadnezzar Ya Kai Yahudawan Bauta a Lokuta Daban-daban

Taƙaitaccen bayanin kai Yahudawan bauta da Nebukadnezzar ya yi a lokuta dabam-dabam.

Irmiya 52:28–30

28 Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta.

A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa 3,023;

29 a shekara ta goma sha takwas ta sarautar Nebukadnezzar,

ya tafi da Yahudawa daga Urushalima 832;

30 a shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa,

Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa 745.

Jimillarsu duka 4,600 ne.