Sashe na 4: Abubuwan da Suka Faru a Babilon Har Zuwa Komowa

Abubuwan da suka faru a Babilon, daga halakar Urushalima zuwa dawowa daga zaman bauta.

Ezekiyel Ya Ji Labarin Faɗuwar Urushalima

Da aka gaya wa Ezekiyel labarin halakar Urushalima, ya yi annabcin cewa Yahudiya za ta zama kufai sarai, da kuma hukunce-hukuncen Allah a kan al'ummomin da ke kewaye waɗanda suke abokan gāban Yahudawa.

587 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ezekiyel 33:21–33

21 A shekara ta goma sha biyu ta zaman bautanmu, a wata na goma a rana ta biyar, wani mutumin da ya gudu daga Urushalima ya zo wurina ya ce, “Birnin ya fāɗi!” 22 To a yamman da ya wuce kafin mutumin ya iso, hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma buɗe bakina kafin mutumin ya iso wurina da safe. Sai bakina ya buɗu ban kuma yi shiru ba.

23 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 24 “Ɗan mutum, mutanen da suke zama a waɗannan kufai a ƙasar Isra’ila suna cewa, ‘Ibrahim mutum ɗaya ne kaɗai, duk da haka Ibrahim ya mallaki ƙasar. Amma mu da muke da yawa; lalle an ba mu ƙasar ta zama mallakarmu.’ 25 Saboda haka ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kun ci nama da jini a cikinsa kuka kuma bauta wa gumakanku kuka zub da jini, kuna gani za ku mallaki ƙasar? 26 Kun dogara ga takobinku, kuka aikata abubuwan banƙyama, kowannenku kuma ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa. Kuna gani za ku mallaki ƙasar?’

27 “Ka faɗa musu wannan, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa muddin ina raye, waɗanda aka rage a kufai za su fāɗi ga takobi, waɗanda suke bayan gari kuwa namun jeji za su cinye su, waɗanda suke a mafaka da kogwannin duwatsu annoba za tă kashe su. 28 Zan mai da ƙasar kango, kuma fariyar ƙarfinta zai ƙare, duwatsun Isra’ila za su zama kufai don kada wani ya ratsa su. 29 Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na mai da ƙasar kango saboda dukan abubuwan banƙyamar da suka yi.’

30 “Game da kai kuma, ɗan mutum, mutanen ƙasarka suna magana da juna game da kai a katanga da kuma ƙofofin gidaje, suna ce wa juna, ‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.’ 31 Mutanena sukan zo wurinka, yadda suka saba su zauna a gabanka don su saurari maganarka, amma ba sa aiki da abin da suka ji. Da bakunansu suna nuna ƙauna, amma zukatansu cike da haɗama suke don ƙazamar riba. 32 Tabbatacce, gare su ba ka fi mai waƙar ƙauna da murya mai daɗi kana kuma yin kiɗa sosai ba, gama sukan ji maganarka amma ba sa amfani da ita.

33 “Sa’ad da dukan wannan ya cika kuma zai cika ɗin, sa’an nan za su sani akwai annabi a tsakiyarsu.”

Ezekiyel 25

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa ka kuma yi annabci a kansu. 3 Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun ce “Yauwa” a kan wuri mai tsarkina sa’ad da aka ƙazantar da shi da kuma a kan ƙasar Isra’ila sa’ad da aka mai da ita kufai da lokacin da aka kai mutanen Yahuda bautar talala, 4 saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku. 5 Zan mai da Rabba wurin kiwo don raƙuma, Ammon kuma wurin hutu don tumaki. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. 6 Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun tafa hannuwanku kuka kuma buga ƙafafunku, kuna farin ciki don nuna dukan ƙiyayyarku a kan ƙasar Isra’ila, 7 saboda haka zan miƙa hannuna gāba da ku in kuma ba da ku ganima ga al’ummai. Zan datse ku daga al’ummai in kuma kore ku daga ƙasashe. Zan hallaka ku, za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

8 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,” 9 saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab, farawa daga garuruwan da suke kan iyaka, Bet-Yeshimot, Ba’al-Meyon da Kiriyatayim, darajar ƙasar. 10 Zan ba da Mowabawa tare da Ammonawa ga mutanen Gabas abin mallaka, don kada a ƙara tuna da Ammonawa a cikin al’ummai; 11 zan hukunta Mowabawa. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

12 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Edom ya ɗauki wa kanta fansa a kan gida Yahuda, ta yi babban laifi ta wurin yin haka, 13 saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan miƙa hannuna a kan Edom in kashe mutanenta da dabbobinsu. Zan sa ta zama kufai, kuma tun daga Teman har zuwa Dedan za a kashe su da takobi. 14 Zan ɗau fansa a kan Edom ta hannun mutanena Isra’ila, za su kuwa hukunta Edom bisa ga fushina da hasalata; za su san sakayyata, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

15 “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Filistiyawa sun yi sakayya, suka ɗauki fansa da mugunta a zukatansu, da kuma daɗaɗɗen ƙiyayya sun nemi su hallaka Yahuda, 16 saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da miƙa hannuna a kan Filistiyawa, zan kuwa datse Keretawa in kuma hallaka waɗanda suka rage a bakin teku. 17 Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani cikin hasalata. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na ɗauki fansa a kansu.’ ”