Yaƙe-yaƙen Yehoshafat da Kyakkyawan Gudanar da Mulkinsa (continued)

897 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Tarihi 20:1–26

1 Bayan wannan, Mowabawa da Ammonawa tare da waɗansu Meyunawa suka zo su yaƙi Yehoshafat.

2 Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat, “Ga babban runduna tana zuwa a kanka daga Edom, daga ƙetaren Teku, daga Aram. Ta ma kai Hazazon Tamar” (wato, En Gedi). 3 A firgice, Yehoshafat ya yanke shawara yă nemi nufin Ubangiji, ya kuma yi shelar azumi a dukan Yahuda. 4 Mutanen Yahuda suka taru gaba ɗaya don su nemi taimako daga wurin Ubangiji, tabbatacce suka fito daga kowane garin Yahuda don su neme shi.

5 Sa’an nan Yehoshafat ya miƙe tsaye a taron Yahuda da Urushalima a haikalin Ubangiji a sabon filin 6 ya ce,

“Ya Ubangiji Allah na kakanninmu, ba kai ne Allah wanda yake sama ba? Kana mulki a bisa dukan mulkokin ƙasashe. Iko da girma suna a hannunka, kuma ba wanda zai iya tsayayya da kai. 7 Ya Allahnmu, ba kai ba ne ka kore mazaunan wannan ƙasa a gaban mutanenka Isra’ila ka kuma ba da ita har abada ga zuriyar Ibrahim abokinka? 8 Sun yi zama a cikinta suka kuma yi gina wuri mai tsarki a cikinta domin Sunanka cewa, 9 ‘In masifa ta zo mana, ko takobin hukunci, ko annoba ko yunwa, za mu tsaya a gabanka a gaban wannan haikalin da yake ɗauke da Sunanka, mu kuma yi kuka gare ka cikin azaba, za ka kuwa ji mu, ka cece mu.’

10 “Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra’ilawa su kai musu yaƙi sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra’ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba. 11 Yau ga yadda suke so su biya mu. Su suke so su kore mu daga ƙasar da ka ba mu gādo. 12 Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Gama ba mu da ƙarfin fuskantar wannan babbar rundunar da take so ta yaƙe mu. Ba mu san abin da za mu yi ba, mu dai mun zuba maka ido.”

13 Dukan mazan Yahuda, tare da matansu da yaransu da ƙananansu, suka tsaya a gaban Ubangiji.

14 Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benahiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, wani Balawe kuma zuriyar Asaf, yayinda yake tsaye a cikin taron.

15 Ya ce, “Saurara, Sarki Yehoshafat da dukan waɗanda suke zama a Yahuda da Urushalima! Ga abin da Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku ji tsoro ko ku fid da zuciya saboda wannan babbar runduna. Gama yaƙin ba naku ba ne, amma na Allah. 16 Gobe ku fito ku gangara ku yaƙe su. Za su yi ta haurawa ta Mashigin Ziz, ku kuwa za ku same su a ƙarshen kwari a Hamadan Yeruwel. 17 Ba lalle ba ne ku yi wannan yaƙi. Ku dai, ku ja dāgā, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ba ku, ya Yahuda da Urushalima. Kada ku ji tsoro; kada ku karai. Ku fito don ku fuskance su gobe, Ubangiji kuwa zai kasance tare ku.’ ”

18 Yehoshafat ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada a gaban Ubangiji. 19 Sa’an nan waɗansu Lawiyawa daga Kohatawa da Korayawa suka tashi tsaye suka yabe Ubangiji, Allah na Isra’ila, da babbar murya sosai.

20 Da sassafe suka tashi suka nufi Hamadan Tekowa. Yayinda suka kama hanya, Yehoshafat ya tsaya ya ce, “Ku saurare ni, Yahuda da mutanen Urushalima! Ku amince da Ubangiji Allahnku za a kuwa kafa ku; ku amince da annabawansa za ku kuwa yi nasara.” 21 Bayan suka yi shawara tare da shugabanni, sai ya zaɓi mutanen da za su ja gaban sojoji suna waƙa ga Ubangiji suna yabonsa saboda tsarkinsa suna cewa,

“Ku yi godiya ga Ubangiji,

gama ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

22 Da suka fara waƙa, suna kuma yabo, sai Ubangiji ya kai hari a kan mutanen Ammon da Mowab da Dutsen Seyir, waɗanda suka kawo hari a Yahuda, aka kuwa ci su da yaƙi. 23 Mutanen Ammon da Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka juna.

24 Sa’ad da mutanen Yahuda suka zo wurin da yake fuskantar hamada, suka duba ta wajen babban rundunar, sai suka ga gawawwaki birjik a ƙasa; babu wani wanda ya kuɓuta. 25 Sa’ad da Yehoshafat da jama’arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna kwasar ganimar saboda yawanta. 26 A rana ta huɗu sai suka taru a Kwarin Beraka, inda suka yabi Ubangiji. Wannan ne ya sa ake kiransa Kwarin Beraka har wa yau.

Zabura 115

1 Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba

amma ga sunanka yă sami ɗaukaka,

saboda ƙaunarka da amincinka.

2 Me ya sa al’ummai suke cewa,

“Ina Allahnsu?”

3 Allahnmu yana a sama;

yana yin duk abin da ya ga dama.

4 Amma gumakansu azurfa da zinariya ne,

da hannuwan mutane suka yi.

5 Suna da bakuna, amma ba sa magana,

idanu, amma ba sa gani;

6 suna da kunnuwa, amma ba sa ji,

hanci, amma ba sa jin ƙanshi

7 suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome,

ƙafafu, amma ba sa iya tafiya;

ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu.

8 Masu yinsu za su zama kamar su,

haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su.

9 Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji,

shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.

10 Ya gidan Haruna, ku dogara ga Ubangiji,

shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.

11 Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji,

shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.

12 Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu.

Zai albarkace gidan Isra’ila,

zai albarkace gidan Haruna,

13 zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji,

manya da ƙanana duka.

14 Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru,

da ku da ’ya’yanku.

15 Bari Ubangiji yă albarkace ku,

shi Mahalicci sama da ƙasa.

16 Saman sammai na Ubangiji ne,

amma ya ba da duniya ga mutum.

17 Ba matattu ba ne masu yabon Ubangiji,

waɗanda suke gangara zuwa wurin da ake shiru;

18 mu ne masu ɗaukaka Ubangiji,

yanzu da har abada kuma.

Yabi Ubangiji.

Zabura 46

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.

1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza

duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa

duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

4 Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna,

tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.

5 Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba;

Allah zai taimake ta da safe.

6 Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi;

ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.

7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;

Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

8 Zo ku ga ayyukan Ubangiji,

kangon da ya kawo a kan duniya.

9 Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit

ko’ina a duniya.

Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu,

ya ƙone garkuwoyi da wuta.

10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;

za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,

za a ɗaukaka ni cikin duniya.”

11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;

Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

2 Tarihi 20:27–30

27 Sa’an nan Yehoshafat ya jagoranci dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka dawo da farin ciki zuwa Urushalima, gama Ubangiji ya ba su dalilin farin ciki a kan abokan gābansu. 28 Suka shiga Urushalima suka shiga haikalin Ubangiji da kiɗin molaye da sarewa da kuma garayu.

29 Tsoron Allah ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa’ad da suka ji yadda Ubangiji ya yi yaƙi a kan abokan gāban Isra’ila. 30 Mulkin Yehoshafat kuwa ya zauna lafiya, gama Allahnsa ya ba shi hutu a kowane gefe.

2 Tarihi 20:35–37

35 Daga baya, Yehoshafat sarkin Yahuda ya haɗa kai da Ahaziya sarkin Isra’ila, wanda yake da laifin mugunta. 36 Ya yarda da shi su gina jiragen ruwan kasuwanci. Bayan aka gina waɗannan a Eziyon Geber, 37 Eliyezer ɗan Dodabahu na Maresha ya yi annabci a kan Yehoshafat cewa, “Domin ka haɗa kai da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Jiragen ruwan kuwa suka farfashe, ba a kuwa iya sa su je kasuwanci ba.

1 Sarakuna 22:49

49 A lokacin Ahaziya ɗan Ahab ya ce wa Yehoshafat, “Bari mutanena su tafi tare da mutanenka,” amma Yehoshafat ya ƙi.

2 Sarakuna 8:16

16 A shekara ta biyar ta mulkin Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, sa’ad da Yehoshafat yake sarautar Yahuda, Yoram ɗan Yehoshafat, ya fara mulkinsa a matsayin sarkin Yahuda.