Sashe na 4: Mulkin Yehoshafat

Masarautar Yahuda

Hawan Yehoshafat Karagar Mulki da Kyakkyawan Mulkinsa

914 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Sarakuna 22:41–44

41 Yehoshafat ɗan Asa ya zama sarkin Yahuda a shekara ta huɗu ta Ahab sarkin Isra’ila. 42 Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa, Azuba ’yar Shilhi. 43 A cikin kome ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa, bai kuma kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Amma bai rurrushe masujadai da suke kan tuddai ba, mutane kuwa suka ci gaba da miƙa hadayu suna kuma ƙone turare a can. 44 Yehoshafat kuma ya zauna lafiya da sarkin Isra’ila.

1 Sarakuna 22:46–47

46 Ya kawar da karuwai maza na masujadai da suke kan tuddai waɗanda suka rage tun mulkin mahaifinsa Asa. 47 Babu sarki a lokacin Edom, saboda haka sai mataimaki ya yi mulki.

2 Tarihi 17:2–19

2 Ya kafa mayaƙa a dukan biranen katangar Yahuda, ya kuma sa runduna a Yahuda da kuma a garuruwan Efraim da mahaifinsa Asa ya ci da yaƙi.

3 Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat domin a shekarunsa na farko-farko ya yi tafiya a hanyoyin da kakansa Dawuda ya bi. Bai nemi shawarar Ba’al ba 4 amma ya nemi Allah na kakansa ya kuma bi umarnansa a maimakon ayyukan da Isra’ila ke yi. 5 Ubangiji ya kafa mulkin a ƙarƙashin ikonsa; dukan Yahuda kuwa suka kawo kyautai wa Yehoshafat, ta haka ya yi arziki sosai da kuma girma. 6 Zuciyarsa ta duƙufa ga hanyoyin Ubangiji, bugu da ƙari, ya kawar masujadan kan tudu da ginshiƙan Ashera daga Yahuda.

7 A shekara ta uku ta mulkinsa, ya aiki ma’aikatansa Ben-Hayil, Obadiya, Zakariya, Netanel da Mikahiya su yi koyarwa a garuruwan Yahuda. 8 Tare da su akwai waɗansu Lawiyawa, Shemahiya, Netaniya, Zebadiya, Asahel, Shemiramot, Yehonatan, Adoniya, Tobiya da Tob Adoniya, da kuma firistoci Elishama da Yehoram. 9 Suka yi koyarwa a dukan Yahuda, suna ɗauke da Littafin Dokar Ubangiji tare da su; suka tafi ko’ina a dukan garuruwan Yahuda suka koyar da mutane.

10 Tsoron Ubangiji ya kama dukan masarautun ƙasashen da suke kewaye da Yahuda, har ba su yi yaƙi da Yehoshafat ba. 11 Waɗansu Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa a matsayin haraji, Larabawa kuwa suka kawo masa garkuna, raguna dubu bakwai da ɗari bakwai da kuma awaki dubu bakwai da ɗari bakwai.

12 Yehoshafat ya yi ta ƙaruwa a ƙarfi; ya gina katanga da biranen ajiya a Yahuda 13 da kuma tanade-tanade masu yawa a garuruwan Yahuda. Ya kuma ajiye gogaggu mayaƙa a Urushalima. 14 Ɗaukar da aka yi musu bisa ga iyalai yana kamar haka.

Daga Yahuda, shugaban ƙungiya 1,000.

Adna ne shugaba, tare da jarumawa 300,000;

15 biye da shi, Yehohanan shi ne shugaba, yana da sojoji 280,000;

16 biye da shi, Amasiya ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa da yardar rai don hidimar Ubangiji, yana da sojoji 200,000.

17 Daga Benyamin,

Eliyada, jarumi soja, yana da sojoji 200,000 riƙe da baka da garkuwoyi;

18 biye da shi, Yehozabad, yana da sojoji 18,000 shiryayyu don yaƙi.

19 Waɗannan su ne suka yi wa sarki hidima, ban da waɗanda aka sa a biranen katanga ko’ina a Yahuda.

Yaƙe-yaƙen Yehoshafat da Kyakkyawan Gudanar da Mulkinsa 897 kafin haihuwar Almasihu

2 Tarihi 18:1–2

1 Yanzu fa Yehoshafat ya wadace ƙwarai yana kuma da girma, ya kuma haɗa kansa da Ahab ta wurin aure. 2 Bayan ’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.

2 Tarihi 19:1–7

1 Sa’ad da Yehoshafat sarkin Yahuda ya dawo zuwa fadansa a Urushalima lafiya, 2 Yehu mai duba, ɗan Hanani, ya fita don yă tarye shi, ya kuma ce wa sarki, “Ya yi kyau ke nan da ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci waɗanda suke ƙin Ubangiji? Da yake ka yi haka fushin Ubangiji yana a kanka 3 Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da ginshiƙan Ashera a ƙasar, ka kuma sa zuciyarka a kan neman Allah.”

4 Yehoshafat ya zauna a Urushalima, ya kuma fita yana shiga cikin mutane daga Beyersheba zuwa ƙasar tudun Efraim ya kuma juyar da su ga Ubangiji Allah na kakanninsu. 5 Ya naɗa alƙalai a kowanne daga cikin biranen katanga na Yahuda a ƙasar. 6 Ya faɗa musu, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a. 7 Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”

Zabura 82

Zabura ta Asaf.

1 Allah yana shugabanta cikin babban taro;

yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.

2 “Har yaushe za ku kāre marasa adalci

ku kuma goyi bayan mugaye? Sela

3 Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu;

ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata;

ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

5 “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba.

Suna yawo cikin duhu;

an girgiza dukan tussan duniya.

6 “Na ce, ‘Ku “alloli” ne;

dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.

7 Amma za ku mutu kamar mutum kurum;

za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”

8 Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya,

gama dukan al’ummai gādonka ne.

2 Tarihi 19:8–11

8 A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna. 9 Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku. 10 Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba.

11 “Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al’amuran da suke na wajen Ubangiji, Zebadiya ɗan Ishmayel kuwa, shugabanku a kan dukan al’amuran da suka shafi sarki, Lawiyawa kuma za su zama a matsayin manya a gabanku. Ku yi abubuwa da ƙarfin hali, bari kuma Ubangiji yă kasance tare da masu yin gaskiya.”