Dawuda Har Zuwa Guduwarsa daga Fadar Shawulu

1063 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Sama’ila 18:5–9

5 Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu.

6 Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa. 7 Suna rawa suna cewa,

“Shawulu ya kashe dubbansa,

Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”

8 Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?” 9 Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda.

1 Sama’ila 16:14–23

14 To, fa, Ruhun Ubangiji ya riga ya rabu da Shawulu, sai mugun ruhu daga Ubangiji ya soma ba shi wahala.

15 Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala. 16 Ranka yă daɗe, muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo wanda ya iya kiɗan molo, domin duk sa’ad da mugun ruhun nan daga Allah ya tashi, sai yă kaɗa molon don hankalinka yă kwanta.”

17 Saboda haka Shawulu ya ce wa ma’aikatansa, “Ku nemo wanda ya iya kiɗan molo sosai ku kawo mini.”

18 Ɗaya daga cikin bayin ya ce, “Na san wani yaro, ɗan Yesse na Betlehem, ya iya kiɗan molo, yana da hikima, shi kuma ya iya yaƙi. Ya iya magana, ga shi kuma kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”

19 Sai Shawulu ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka Dawuda wanda yake kiwon tumaki.” 20 Saboda haka Yesse ya ɗauki jaki tare da burodi da ruwan inabi da ɗan ƙarami bunsuru ya ba wa ɗansa Dawuda yă kai wa Shawulu.

21 Dawuda ya isa wurin Shawulu ya shiga hidimarsa. Shawulu kuwa ya so shi ƙwarai da gaske. Dawuda ya zama ɗaya daga cikin masu sanya sulke. 22 Sa’an nan Shawulu ya aika saƙo wurin Yesse cewa, “Ka bar Dawuda yă yi mini hidima domin ina jin daɗinsa ƙwarai.”

23 Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi.

1 Sama’ila 18:10–30

10 Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa. 11 Da ƙarfi yana magana da kansa yana cewa, “Zan kafe Dawuda da bango.” Amma Dawuda ya bauɗe masa sau biyu.

12 Shawulu ya ji tsoron Dawuda don Ubangiji yana tare da shi, amma Ubangiji ya riga ya bar Shawulu. 13 Saboda haka Shawulu bai yarda Dawuda yă zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban sojoji dubu. Dawuda kuwa ya riƙa bi da su yana kaiwa yana kuma da tare da su.

14 A kome da Dawuda ya yi yakan yi nasara gama Ubangiji yana tare da shi. 15 Da Shawulu ya ga yadda yake cin nasara, sai ya ji tsoronsa. 16 Amma dukan Isra’ila da Yahuda suka ƙaunaci Dawuda gama yana bin da su a yaƙe-yaƙensu.

17 Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”

18 Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Wane ni, wa ya san iyayena ko kabilar iyayena a Isra’ila da zan zama surukin sarki?” 19 Da lokaci ya kai da Merab ’yar Shawulu za tă yi aure da Dawuda, sai aka aurar da ita wa Adriyel na Mehola.

20 Mikal ’yar Shawulu kuwa tana ƙaunar Dawuda sosai. Da aka gaya wa Shawulu labarin, sai ya yi farin ciki, ya yi tunani ya ce, 21 “Zan ba shi ita tă zama masa tarko, da haka Filistiyawa za su same shi.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Yanzu kana da dama sau na biyu ka zama surukina.”

22 Sai Shawulu ya umarci ma’aikatansa cewa, “Ku yi magana da Dawuda asirce ku ce, ‘Duba, sarki yana farin ciki da kai, dukan ma’aikatansa kuma suna sonka, ka yarda ka zama surukinsa.’ ”

23 Suka sāke yi wa Dawuda wannan magana amma Dawuda ya ce, “Kuna tsammani abu mai sauƙi ne mutum yă zama surukin sarki? Ni talaka ne, kuma ba sananne ba.”

24 Da ma’aikatan Shawulu suka gaya masa abin da Dawuda ya faɗa. 25 Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa.

26 Da ma’aikatan suka gaya wa Dawuda waɗannan abubuwa, sai ya yi murna don zai zama surukin sarki. Amma kafin lokacin yă cika, 27 Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da ’yarsa Mikal aure ga Dawuda.

28 Da Shawulu ya gane Ubangiji yana tare da Dawuda, ’yarsa Mikal kuma tana ƙaunarsa, 29 sai Shawulu ya ƙara jin tsoron Dawuda har ya zama maƙiyinsa a dukan sauran rayuwarsa.

30 Manyan sojojin Filistiyawa suka yi ta fita suna yaƙi da Isra’ilawa, amma kullum Dawuda yakan sami nasara fiye da sauran manyan sojojin Shawulu. Ta haka ya yi suna ƙwarai.