Dawuda Har Zuwa Guduwarsa daga Fadar Shawulu (continued)
1063 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Shawulu ya gaya wa ɗansa Yonatan da ma’aikatansa su kashe Dawuda. Amma Yonatan yana son Dawuda sosai. 2 Sai ya gargaɗe shi ya ce, “Mahaifina Shawulu yana neman hanyar da zai kashe ka. Ka kula da kanka gobe da safe, ka tafi wani wuri ka ɓuya. 3 Zan je in tsaya da mahaifina a fili inda kake, zan yi masa magana game da kai. Zan kuma gaya maka abin da na ji.”
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda.
1 A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka.
Yaya za ku ce mini,
“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.
2 Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu;
sun kuma ɗana kibiyoyinsu
don su harbi mutanen kirki a zuciya
daga cikin duhu.
3 Sa’ad da aka tumɓuke tushe,
me adali zai iya yi?”
4 Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki;
Ubangiji yana a kursiyinsa a sama.
Yana kallon ’ya’yan mutane;
idanunsa suna bincike su.
5 Ubangiji yana bincike adalai,
amma ransa yana ƙi mugaye
da masu son rikici.
6 A kan mugaye zai zuba
garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu;
iska mai zafi zai zama rabonsu.
7 Gama Ubangiji mai adalci ne,
yana ƙaunar gaskiya
masu adalci za su ga fuskarsa.
4 Yonatan ya yi magana mai kyau a kan Dawuda a wajen mahaifinsa ya ce, “Kada sarki yă yi wani mummunan abu wa bawansa Dawuda, gama bai yi maka wani abu marar kyau ba. Abin da ya yi ya amfane ka ƙwarai da gaske. 5 Ya yi kasai da ransa sa’ad da ya kashe Bafilistin nan. Ubangiji ya ba wa dukan Isra’ila babban nasara, ka gani, ka kuma yi farin ciki. Don me za ka ci mutuncin amintaccen mutum kamar Dawuda ta wurin kashe shi ba tare da wani dalili ba?”
6 Shawulu ya saurari Yonatan sai ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a kashe Dawuda ba.”
7 Ta haka Yonatan ya kira Dawuda ya gaya masa dukan maganarsu. Ya kawo shi wurin Shawulu, Dawuda kuwa ya zauna tare da Shawulu kamar dā.
8 Wani yaƙi ya sāke tashi, Dawuda kuwa ya fita ya yaƙi Filistiyawa, ya kai musu hari mai tsanani, sai da suka gudu a gabansa.
9 Amma mugun ruhu daga Ubangiji ya sauko wa Shawulu yayinda yana zaune a cikin gidansa da māshi a hannunsa. Yayinda Dawuda yake bugan molo, 10 Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu.
11 Shawulu ya aiki mutane zuwa gidan Dawuda su yi gadin gidan, su kuma kashe Dawuda. Amma Mikal matar Dawuda ta gargaɗe Dawuda, ta ce, “In ba ka gudu a daren nan ba, kashegari za a kashe ka.” 12 Haka kuwa Mikal ta sauko da Dawuda ta taga ya gudu, ya tsere. 13 Sai Mikal ta ɗauki gunki ta kwantar da shi a gādo, ta sa masa gashin akuya a kansa, sai ta rufe da mayafi.
14 Da Shawulu ya aiki mutane su kama Dawuda. Mikal ta ce, “Ba shi da lafiya.”
15 Sai Shawulu ya sāke aiki mutanen su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi a gādonsa domin in kashe shi.” 16 Amma da mutanen suka shiga sai suka ga gunkin a gadon, a wajen kan kuwa akwai gashin akuya.
17 Shawulu ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya gudu ya tsere?”
Mikal ta ce masa, “Ya ce mini, ‘Idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni?’ ”
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi.
1 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah;
ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.
2 Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta
ka kuma cece ni daga masu kisa.
3 Duba yadda suka kwanta suna jirana!
Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni
ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.
4 Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini.
Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!
5 Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,
Allah na Isra’ila,
ka tashi ka hukunta dukan al’ummai;
kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela
6 Sukan dawo da yamma,
suna wage haƙora kamar karnuka,
suna yawo a birni.
7 Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu,
suna tofar da takuba daga leɓunansu,
suna cewa, “Wa zai ji mu?”
8 Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya;
kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.
9 Ya ƙarfina, na dogara gare ka;
kai, ya Allah, kai ne kagarata, 10 Allah mai ƙaunata.
Allah zai sha gabana
zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.
11 Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu,
in ba haka mutanena za su manta.
Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai,
ka kuma kawar da su.
12 Saboda zunuban bakunansu,
saboda maganganun leɓunansu,
bari a kama su cikin fariyarsu.
Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,
13 ka cinye su da hasala,
ka cinye su sarai.
Sa’an nan za a sani a iyakar duniya
cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Sela
14 Sukan dawo da yamma,
suna wage haƙora kamar karnuka,
suna yawo a birni.
15 Suna ta yawo neman abinci
su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba.
16 Amma zan rera game da ƙarfinka,
da safe zan rera game da ƙaunarka;
gama kai ne mafakata,
kagarata a lokacin wahala.
17 Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;
kai, ya Allah, kai ne kagarata,
Allah mai ƙaunata.