Zefaniya Ya Yi Kira ga Tuba

Zefaniya ya yi kira ga mutanen su tuba, a kusan lokacin gyare-gyaren Yosiya.

624 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zefaniya 1–3

1 Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.

2 “Zan hallaka kome

a fuskar duniya,”

in ji Ubangiji.

3 “Zan hallaka mutane da dabbobi;

zan kuma hallaka tsuntsayen sama

da kifayen teku,

da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.”

“Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,”

in ji Ubangiji.

4 “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda

da kuma dukan mazaunan Urushalima.

Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri,

da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,

5 waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki

don su yi sujada ga rundunar taurari.

Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji

suke kuma rantsuwa da sunan Molek.

6 Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji,

ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”

7 Ku yi shiru a gaban Ubangiji Mai Iko Duka,

gama ranar Ubangiji ta yi kusa.

Ubangiji ya shirya hadaya;

ya kuma tsarkake waɗanda ya gayyato.

8 “A ranar hadayar Ubangiji

zan hukunta sarakuna

da kuma ’ya’yan sarakuna

da duk waɗanda suke sanye

da rigunan ƙasashen waje.

9 A wannan rana zan hukunta

dukan waɗanda suke kauce taka madogarar ƙofa,

waɗanda suke cika haikalin allolinsu

da rikici da ruɗu.

10 “A wannan rana,”

in ji Ubangiji,

“Za a ji kuka daga Ƙofar Kifi,

kururuwa daga Sabon Mazauni,

da kuma amo mai ƙarfi daga tuddai.

11 Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa;

za a hallaka dukan ’yan kasuwanku,

dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace.

12 A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitilu

in kuma hukunta waɗanda ba su kula ba,

waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya,

waɗanda suke tsammani, ‘Ubangiji ba zai yi kome ba

nagari ko mummuna.’

13 Za a washe dukiyarsu,

a rurrushe gidajensu.

Za su gina gidaje

amma ba za su zauna a ciki ba;

za su shuka inabi

amma ba za su sha ruwansa ba.”

14 Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa,

ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri.

Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi,

za a ji kururuwan jarumi a can.

15 Ranan nan za tă zama ranar fushi,

rana ce ta baƙin ciki da azaba,

rana ce ta tashin hankali da lalacewa,

ranar duhu baƙi ƙirin,

ranar gizagizai da baƙin duhu,

16 rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi

gāba da birane masu mafaka,

da kuma kusurwar hasumiyoyi.

17 “Zan kawo baƙin ciki a kan mutane

za su kuma yi tafiya kamar makafi,

domin sun yi wa Ubangiji zunubi.

Za a zubar da jininsu kamar ƙura

kayan cikinsu kuma kamar najasa.

18 Azurfarsu ko zinariyarsu

ba za su iya cetonsu ba

a ranar fushin Ubangiji.”

A cikin zafin kishinsa

za a hallaka dukan duniya

gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya

nan da nan.

2:1 Ku tattaru, ku tattaru,

Ya ku al’umma marar kunya,

2 kafin ƙayyadadden lokacin nan yă zo

ranan nan kuma ta share ku kamar ƙaiƙayi

kuma kafin fushi mai tsanani na Ubangiji yă auko muku,

kafin ranar fushin Ubangiji ta auko muku.

3 Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u,

ku da kuke yin abin da ya umarta.

Ku nemi adalci da tawali’u;

mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji.

4 Za a yashe Gaza

a kuma bar Ashkelon kango.

Da tsakar rana Ashdod za tă zama babu kowa

a kuma tumɓuke Ekron.

5 Taku ta ƙare ku da kuke zama a bakin teku,

Ya ku mutanen Keretawa;

maganar Ubangiji tana gāba da ke,

Ya ke Kan’ana, ƙasar Filistiyawa.

“Zan hallaka ki

kuma babu abin da zai rage.”

6 Ƙasar da take a bakin teku, inda Keretawa suke zaune,

za tă zama wurin da makiyaya da ta garken tumaki.

7 Za tă zama mallakar raguwar gidan Yahuda;

a can za su sami wurin kiwo.

Da yamma za su kwanta

a gidajen Ashkelon.

Ubangiji Allahnsu zai lura da su;

zai maido musu da martabarsu.

8 “Na ji irin zagin da Mowab take yi,

da kuma ba’ar Ammonawa,

waɗanda suka zagi mutanena

suna kuma yi barazana a kan ƙasarsu.

9 Saboda haka, muddin ina raye,”

in ji Ubangiji Maɗaukaki,

Allah na Isra’ila,

“tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom,

Ammonawa kuma kamar Gomorra,

ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri,

ƙasa marar amfani har abada.

Raguwar mutanena za su washe su;

waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.”

10 Wannan ne zai zama sakamakon girmankansu,

saboda zagi da kuma ba’ar da suka yi wa mutanen Ubangiji Maɗaukaki.

11 Ubangiji zai zama abin tsoro a gare su

sa’ad da ya hallaka allolin ƙasar.

Al’ummai a kowane bakin teku za su yi masa sujada,

kowa a ƙasarsa.

12 “Ku ma, ya Kushawa,

za a kashe ku da takobina.”

13 Zai kuma miƙa hannunsa gāba da arewa

yă kuma hallaka Assuriya,

zai mai da Ninebe kango gaba ɗaya

ta kuma zama busasshiya kamar hamada.

14 Garkuna za su kwanta a can,

da kowace irin halitta,

Mujiyar hamada da bushiya

za su zauna a kan ginshiƙanta.

Kukansu za tă ratsa tagogi,

ɓuraguzai za su tare ƙofofin shiga,

za a kware ginshiƙan al’ul.

15 Birnin da yake harka ke nan

da take zaune lafiya.

Ta ce wa kanta,

“Ni ce, kuma babu kamata.”

Dubi irin kangon da ta zama mana,

mazaunin namun jeji!

Duk wanda ya wuce ta sai ya yi mata tsaki

yana kaɗa kai.

3:1 Taki ta ƙare, ke birnin mai danniya,

mai ’yan tawaye da kuma masu ƙazanta!

2 Ba kya yi wa kowa biyayya,

ba kya kuma yarda da kuskurenki.

Ba kya dogara ga Ubangiji,

ba kya kuma kusatowa kusa da Allahnki.

3 Sarakunanki ruri ne na zakoki,

shugabanninki kyarketan dare ne,

waɗanda ba sa rage kome don safe.

4 Annabawanki mahaukata ne

mutanenki masu cin amana ne.

Firistocinki suna ƙazantar da Wurin Mai Tsarki

suna kuma keta dokoki.

5 Ubangiji da yake cikinki mai adalci ne;

ba ya yin abin da ba daidai ba.

Kowace safiya yakan bayyana dokokinsa a fili,

kowace sabuwar rana kuma ba ya kāsawa,

duk da haka marasa adalci ba sa jin kunya.

6 “Na daddatse al’ummai;

an kuma rurrushe kagararsu.

Na bar titunansu ba kowa,

ba mai ratsawa a ciki.

An ragargaza biranensu;

ba wanda za a bari, babu ko ɗaya.

7 Na ce wa birnin,

‘Tabbatacce za ki ji tsorona

ki kuma yarda da gyara!’

Ta haka ba za a datse wurin zamanki ba,

ba kuwa dukan hukuncena za su hau bisa kansu ba.

Amma har yanzu suna marmari

su yi rashin gaskiya a duk abin da suke yi.

8 Saboda haka ku jira ni,” in ji Ubangiji;

“a ranar da zan tsaya in ba da shaida,

Na yanke shawara in tattara dukan al’ummai,

in tattara mulkoki

in kuma zuba fushina a kansu,

da dukan zafin haushina.

Za a mamaye dukan duniya

da zafin fushina.

9 “Sa’an nan zan tsarkake leɓunan mutanen,

don dukansu su kira bisa ga sunan Ubangiji

su kuma yi masa hidima kafaɗa da kafaɗa.

10 Tun daga ƙetaren rafuffukan Kush

masu yi mini sujada, mutanena da suke a warwatse,

za su kawo mini hadayu.

11 A wannan rana ba za ku sha kunya

saboda laifofin da kuka yi mini,

gama zan ɗauke wa wannan birni

waɗanda suke farin ciki cikin girmankansu.

Ba kuma za ka ƙara yin kallon reni

a tuduna mai tsarki ba.

12 Amma zan zauna a cikinki

masu tawali’u da masu ƙasƙantar da kai,

waɗanda suke dogara ga sunan Ubangiji.

13 Raguwar Isra’ila ba za su ƙara aikata abin da ba daidai ba,

ba za su faɗa ƙarya ba,

ba kuwa za a sami ruɗu a bakunansu ba.

Za su ci su kuma kwanta

kuma babu wanda zai ba su tsoro.”

14 Ki rera, ya Diyar Sihiyona;

ki tā da murya, ya Isra’ila!

Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki,

Ya Diyar Urushalima!

15 Ubangiji ya ɗauke hukuncinki,

ya mai da abokan gābanki baya.

Ubangiji, Sarkin Isra’ila, yana tare da ke;

ba kuma za ki ƙara jin tsoron wani lahani ba.

16 A wannan rana za su cewa Urushalima,

“Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona;

kada ki bar hannuwanki su raunana.

17 Ubangiji Allahnki yana tare da ke,

mai iko ne don ceto.

Zai yi matuƙar farin ciki da ke,

zai rufe ki da ƙaunarsa,

zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”

18 “Zan cire taƙaici daga gare ki

a ƙayyadaddun bukukkuwa;

su kaya ne da kuma zargi a gare ki.

19 A wannan lokaci zan jijji wa

waɗanda suka danne ku;

zan kuɓutar da guragu

in kuma tattara waɗanda suke a warwatse.

Zan sa a yabe su a kuma girmama su

a kowace ƙasar da aka kunyatar da su.

20 A wannan lokaci zan tattara ku;

a wannan lokaci zan kawo ku gida,

zan sa a yabe ku a kuma girmama ku

a cikin dukan mutanen duniya

a sa’ad da na maido da arzikinku

a idanunku,”

in ji Ubangiji.