Annabce-annabcen Zakariya na Ƙarshe
457 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Annabci.
Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrak
za tă kuma sauko a kan Damaskus,
gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila
suna a kan Ubangiji,
2 da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita,
da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.
3 Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi;
ta tara azurfa kamar ƙasa,
zinariya kuma kamar tarin shara a tituna.
4 Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta,
zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku,
wuta kuma za tă cinye ta.
5 Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro;
Gaza za tă yi birgima cikin azaba,
haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya.
Gaza za tă rasa sarkinta
za a kuma gudu a bar Ashkelon.
6 Baƙi za su mallaki Ashdod,
kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa.
7 Zan kawar da jini daga bakinsu,
zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu.
Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu,
su kuma zama shugabanni a Yahuda,
Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa.
8 Amma zan kāre gidana
daga sojoji masu kai da kawowa.
Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba,
gama yanzu ina tsaro.
9 Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima!
Ki yi sowa, Diyar Urushalima!
Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki,
mai adalci yana kuma da ceto,
mai tawali’u yana kuma hawan jaki,
yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.
10 Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim,
da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima,
za a kuma karya bakan yaƙi.
Zai yi shelar salama ga al’ummai.
Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku,
daga Kogi kuma zuwa ƙarshen duniya.
11 Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke,
zan ’yantar da ’yan kurkukunki daga rami marar ruwa.
12 Ku koma maɓuya, ya ku ’yan kurkuku masu sa zuciya;
ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu.
13 Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana,
in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya.
Zan tā da ’ya’yanki maza, ya Sihiyona,
gāba da ’ya’yanki, ya Girka,
in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi.
14 Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu;
kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya.
Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho;
zai taho ta cikin guguwa daga kudu,
15 Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su.
Za su hallakar
su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa.
Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi;
za su cika kamar kwanon
da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade.
16 Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana
gama su mutanensa ne da kuma garkensa.
Za su haska a cikin ƙasarsa
kamar lu’ulu’u a rawani.
17 Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa!
Hatsi zai sa samari su yi murna,
sabon ruwan inabi kuma zai sa ’yan mata su yi farin ciki.
10:1 Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara;
Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari.
Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama
yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.
2 Gumaka suna maganganun ruɗu,
masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya,
suna faɗa mafarkan ƙarya
suna ba da ta’aziyyar banza.
Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki
waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.
3 “Ina fushi da makiyayan,
zan kuma hukunta shugabannin;
gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura
da garkensa, wato, gidan Yahuda,
zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.
4 Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito,
daga gare shi za a samu abin kafa tenti,
daga gare shi za a sami bakan yaƙi,
daga gare shi za a sami kowane mai mulki.
5 Tare za su zama kamar mutane masu ƙarfi
suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi.
Domin Ubangiji yana tare da su,
za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.
6 “Zan ƙarfafa gidan Yahuda
in kuma ceci gidan Yusuf.
Zan maido da su
domin ina jin tausayinsu.
Za su zama kamar
ban taɓa ƙinsu ba,
gama ni ne Ubangiji Allahnsu
zan kuma amsa musu.
7 Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi,
zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi.
’Ya’yansu za su gani su yi murna;
zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.
8 Zan ba da alama
in kuma tattara su.
Ba shakka zan fanshe su;
za su yi yawa kamar yadda suke a dā.
9 Ko da yake na warwatsa su cikin mutane,
duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni.
Su da ’ya’yansu za su rayu,
za su kuwa komo.
10 Zan komo da su daga Masar
in kuma tattara su daga Assuriya.
Zan kawo su Gileyad da Lebanon,
har wuri yă kāsa musu.
11 Za su ratsa cikin tekun wahala;
zan kwantar da raƙuman teku
dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe.
Za a ƙasƙantar da Assuriya,
sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.
12 Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji
kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,”
in ji Ubangiji.
11:1 Buɗe ƙofofinki, ya Lebanon,
don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki.
2 Yi kuka, ya itacen fir, gama itacen al’ul ya fāɗi;
itatuwa masu daraja sun lalace!
Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan;
an sassare itatuwan babban kurmi!
3 Ku ji kukan makiyaya;
an ɓata musu wuraren kiwonsu masu ciyayi!
Ku ji rurin zakoki;
an lalatar da jejin Urdun!
4 Ga abin da Ubangiji Allahna ya ce, “Yi kiwon garken tumakin da za a yanka. 5 Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba. 6 Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.”
7 Saboda haka na yi kiwon garken da za a yanka, musamman garken da ake zalunta. Sai na ɗauki sanduna biyu na kira ɗaya Tagomashi, ɗaya kuma Haɗinkai, sai na yi kiwon garken. 8 Cikin wata guda na kawar da makiyayan nan uku.
Garken suka ƙi ni, na kuwa gaji da su 9 na ce, “Ba zan zama makiyayinku ba. Bari masu mutuwa su mutu, masu hallaka kuma su hallaka. Bari waɗanda suka ragu su ci naman juna.”
10 Sai na ɗauki sandana mai suna Tagomashi na karya shi, na janye alkawarin da na yi da dukan al’ummai. 11 An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce.
12 Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin.
13 Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.
14 Sai na karya sandana na biyu mai suna Haɗinkai, ta haka na karya ’yan’uwantakar da take tsakanin Yahuda da Isra’ila.
15 Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na wawan makiyayi. 16 Gama zan tā da makiyayi a ƙasar wanda ba zai kula da ɓatattu, ko yă nemi ƙanana, ko yă warkar da waɗanda suka ji ciwo, ko kuma ciyar da masu lafiya ba, sai dai zai ci naman keɓaɓɓun tumaki, yă farfasa kofatonsu.
17 “Kaito ga banzan makiyayin nan,
wanda ya bar garken!
Bari takobi yă sare hannunsa da idonsa na dama!
Bari hannunsa yă shanye gaba ƙaf,
idonsa na dama kuma yă makance sarai!”