An Sake Gina Ganuwar Urushalima (continued)
445 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Sa’ad da magana ta zo kunnen Sanballat, da Tobiya, da Geshem mutumin Arab da kuma sauran abokan gābanmu cewa na sāke gina katangar har babu sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake har zuwa lokacin ban sa ƙofofi a ƙyamare ba 2 Sanballat da Geshem suka aika mini wannan saƙo cewa, “Ka zo, mu sadu a wani ƙauye a filin Ono.”
Amma makirci ne suke yi don su cuce ni; 3 saboda haka sai na aika musu da wannan amsa, na ce, “Ina cikin babban aiki, ba zan kuwa iya gangarawa ba. Don me zan bar aikin yă tsaya don in gangara zuwa wurinku?” 4 Suka yi ta aiko mini da wannan saƙo har sau huɗu, ni kuwa na yi ta ba su amsa irin ta dā.
5 Sai sau na biya, Sanballat ya aiki mataimakinsa gare ni da irin saƙo guda, kuma a hannunsa akwai wasiƙar da ba a yimƙe ba 6 wadda aka rubuta cewa,
“An ba da labari cikin al’ummai, kuma Geshem ya ce gaskiya ne, cewa kai da Yahudawa kun shirya tawaye, saboda haka kuke sāke ginin katangar. Ban da haka ma, bisa ga waɗannan rahotanni kana shirin zaman sarkinsu 7 har ma ka naɗa annabawa su yi wannan shela game da kai a Urushalima, su ce, ‘Akwai sarki a Yahuda!’ To, wannan rahoto zai koma wurin sarki; saboda haka ka zo, mu tattauna wannan batu.”
8 Sai na aika masa wannan amsa, na ce, “Babu wani abu haka da yake faruwa; ka dai ƙaga wannan daga tunaninka ne.”
9 Suka dai yi ƙoƙari su tsoratar da mu, suna cewa, “Hannuwansu za su rasa ƙarfin yin aiki, ba kuwa za su ƙare aikin ba.”
Amma na yi addu’a na ce, “Yanzu, ya Allah, ka ƙarfafa hannuwana.”
10 Wata rana na tafi gidan Shemahiya ɗan Delahiya, ɗan Mehetabel, wanda aka hana fita a gidansa. Ya ce mini, “Mu sadu gobe a gidan Allah, a cikin haikali, mu kuma kulle ƙofofin haikali, gama mutane suna zuwa su kashe ka, tabbatacce za su zo da dare su kashe ka.”
11 Amma na ce, “Ya kamata mutum kamar ni yă gudu? Ko kuwa ya kamata wani kamar ni yă shiga cikin haikali don yă ceci ransa? Ba zan tafi ba!” 12 Na gane cewa Allah bai aike shi ba, ya yi annabci a kaina domin Tobiya da Sanballat sun yi hayarsa ne. 13 An yi hayarsa don yă sa in ji tsoro in yi zunubi ta yin haka, sa’an nan za su ba ni mugun suna, su wofinta ni.
14 Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat, saboda abin da suka yi; ka kuma tuna da annabiya Nowadiya da sauran annabawa waɗanda suke ƙoƙari su tsorata ni.
15 Cikin kwana hamsin da biyu aka gama gina katangar, a ranar ashirin da biyar ga watan Elul. 16 Sa’ad da dukan abokan gābanmu suka ji haka, dukan al’umman da suke kewaye da mu suka ji tsoro, suka rasa ƙarfin halinsu, domin sun gane cewa wannan aiki an yi shi da taimakon Allahnmu ne.
17 A waɗannan kwanaki, manyan garin Yahuda suka yi ta aika wasiƙu masu yawa zuwa ga Tobiya, shi kuma ya yi ta aika musu da amsoshi. 18 Gama mutane da yawa a cikin Yahuda sun rantse wa Tobiya za su goyi bayansa, domin ya auri ’yar Shekaniya, ɗan Ara. Ɗansa kuma, wato, Yehohanan, ya auri ’yar Meshullam, ɗan Berekiya. 19 Ban da haka ma, mutanen sun yi ta ba ni labarin ayyuka masu kyau da Tobiya ya yi, sa’an nan kuma suna faɗa masa duk abin da na faɗa. Tobiya kuwa ya aika wasiƙu don yă tsorata ni.
An Keɓe Ganuwar Urushalima
27 A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo. 28 Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa, 29 daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.
30 Sa’ad da firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu da tsarki, sai suka tsarkake mutane, ƙofofi da kuma katanga.
31 Sai na sa shugabannin Yahuda suka haura zuwa bisan katangar. Na kuma sa manyan ƙungiyoyi biyu na mawaƙa su miƙa godiya. Ɗaya ya haura zuwa bisan katangar zuwa dama, wajen Ƙofar Juji. 32 Hoshahiya da rabin shugabannin Yahuda kuwa suka bi su, 33 tare da Azariya, Ezra, Meshullam, 34 Yahuda, Benyamin, Shemahiya, Irmiya, 35 da waɗansu firistoci kuma da ƙahoni, da kuma Zakariya ɗan Yonatan, ɗan Shemahiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mikahiya, ɗan Zakkur, ɗan Asaf, 36 da ’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon. 37 A Ƙofar Maɓuɓɓuga suka ci gaba kai tsaye suka haura matakalan Birnin Dawuda a kan hawa zuwa katangar suka wuce a bisa gidan Dawuda zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.
38 Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi, 39 bisa Ƙofar Efraim, Ƙofar Yeshana, Ƙofar Kifi, Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiya ɗari, har zuwa Ƙofar Tumaki. A Ƙofar Matsara suka tsaya.
40 Ƙungiyoyin mawaƙa biyu da suka yi godiya suka ɗauki wurarensu a gidan Allah, haka ma ni, tare da rabin shugabanni, 41 da kuma firistoci, Eliyakim, Ma’asehiya, Miniyamin, Mikahiya, Eliyohenai, Zakariya da Hananiya tare da ƙahoninsu, 42 haka ma Ma’asehiya, Shemahiya, Eleyazar, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam da Ezer. Mawaƙan suka rera waƙoƙi a ƙarƙashin kulawar Yezrahiya. 43 A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa.
Nehemiya Ya Koma Farisa
1 Bayan an sāke gina katangar na kuma sa ƙofofi a wurarensu, sai aka naɗa masu tsaro, da mawaƙa, da Lawiyawa. 2 Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane. 3 Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.”
4 Birnin Urushalima kuwa tana da fāɗi da girma, amma mutanen da suke zama a cikinta kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje da yawa ba tukuna.