Waƙar Solomon (continued)

1001 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Waƙar Waƙoƙi 6–8

Ƙawaye

1 Ina ƙaunataccenki ya tafi,

yake mafiya kyau cikin mata?

Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi,

don mu taimake ki nemansa.

Ƙaunatacciya

2 Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa,

zuwa inda fangulan kayan yaji suke,

don yă yi kiwo a cikin lambun

don kuma yă tattara furen bi-rana.

3 Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne;

yana kiwo a cikin furen bi-rana.

Ƙaunatacce

4 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza,

kyakkyawa kuma kamar Urushalima,

mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.

5 Ki kau da idanu daga gare ni;

gama suna rinjayata.

Gashinki yana kama da garken awakin

da suke gangarawa daga Gileyad.

6 Haƙoranki suna kama da garken tumakin

da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka.

Kowanne yana tare da ɗan’uwansa;

babu waninsu da yake shi kaɗai.

7 Kumatunki sun yi kamar rumman

da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.

8 Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can,

da ƙwarƙwarai tamanin

da kuma budurwai da suka wuce ƙirge;

9 amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take,

tilo kuwa ga mahaifiyarta,

’yar lele ga wadda ta haife ta.

’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka;

sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.

Ƙawaye

10 Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir?

Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana,

mai daraja kamar taurari a jere?

Ƙaunatacce

11 Na gangara zuwa cikin itatuwan almon

don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari,

don in ga ko inabi sun yi ’ya’ya

ko rumman suna fid da furanni.

12 Kafin in san wani abu,

sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.

Ƙawaye

13 Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya;

ki dawo, ki dawo, don mu dube ki!

Ƙaunatacce

Don me kuke duban Bashulammiya

sai ka ce rawar Mahanayim?

7:1 Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne,

Ya diyar sarki!

Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja,

aikin hannun gwanin sassaƙa.

2 Cibinki kamar kwaf ne

da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba.

Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama

wanda furen bi-rana ya kewaye.

3 Nonanki sun yi kamar bareyi biyu,

tagwayen barewa.

4 Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa.

Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon

kusa da ƙofar Bat Rabbim.

Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon

wadda take duban Damaskus.

5 Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel.

Gashinki ya yi kamar shunayya;

yakan ɗauke hankalin sarki.

6 Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi,

Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!

7 Tsayinki ya yi kamar itacen dabino,

kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace.

8 Na ce, “Zan hau itacen dabino;

zan kama ’ya’yansa.”

Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa,

ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,

9 kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau.

Ƙaunatacciya

Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena,

yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.

10 Ni ta ƙaunataccena ce,

kuma sha’awarsa domina ne.

11 Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari,

bari mu kwana a ƙauye.

12 Bari mu tafi gonar inabi da sassafe

don mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya,

ko furanninsu sun buɗe,

ko rumman sun yi fure,

a can zan nuna maka ƙaunata.

13 Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu,

a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi,

sabo da tsoho,

da na ajiye dominka, ƙaunataccena.

8:1 Da a ce kai ɗan’uwa ne gare ni,

wanda nonon mahaifiyata sun shayar!

Da in na same ka a waje,

na sumbace ka,

babu wanda zai rena ni.

2 Da sai in bi da kai

in kawo ka gidan mahaifiyata,

ita da ta koyar da ni.

Da na ba ka ruwan inabi gaurayayye da kayan yaji ka sha,

zaƙin rumman nawa.

3 Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina,

hannunsa na dama kuma ya rungume ni.

4 ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari.

Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba

sai haka ya zama lalle.

Ƙawaye

5 Wace ce wannan da take haurawa daga hamada

tana dogara a kan ƙaunataccenta?

Ƙaunatacciya

A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke,

a wurin da aka haife ki,

wurin da mahaifiyarki ta haife ki.

6 Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka,

kamar hatimi a hannunka;

gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa,

kishinta yana kamar muguntar kabari,

yana ƙuna kamar wuta mai ci,

kamar gagarumar wuta.

7 Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba,

koguna ba za su iya kwashe ta ba.

In wani zai bayar da

dukan dukiyar gidansa don ƙauna,

za a yi masa dariya ne kawai.

Ƙawaye

8 Muna da ƙanuwa,

nonanta ba su riga sun yi girma ba.

Me za mu yi da ƙanuwarmu

a ranar da za a yi maganar sonta?

9 Da a ce ita katanga ce,

da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta.

Da a ce ita ƙofa ce,

da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul.

Ƙaunatacciya

10 Ni katanga ce

kuma nonaina sun yi kamar hasumiya.

Ta haka na zama idanunsa

kamar wanda yake kawo gamsuwa.

11 Solomon ya kasance da gonar inabi a Ba’al-Hamon;

ya ba da hayar gonar inabi ga ’yan haya.

Kowanne zai biya shekel dubu na azurfa

don ’ya’yan inabin.

12 Amma gonar inabina nawa ne da zan bayar;

shekel dubu naka ne, ya Solomon,

kuma ɗari biyu na waɗanda suke lura da ’ya’yan itatuwansa ne.

Ƙaunatacce

13 Ke da kike zaune a cikin lambu

da ƙawaye suna lura da ke,

bari in ji muryarki!

Ƙaunatacciya

14 Ka zo, ƙaunataccena,

ka zama kamar barewa

ko kuwa kamar ’yar batsiya

a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.