Masarautar Isra’ila

Mulkin Yoram a Kan Isra’ila Ya Ci Gaba

Kewaye Samariya da Yaƙi da Yunwar da Ta Faru a Cikinta

Kewaye Samariya da yaƙi, yunwa, da ceto kwatsam.

887 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Sarakuna 6:24–8:6

24 Bayan wani lokaci, Ben-Hadad sarkin Aram ya tattara dukan rundunarsa, ya je ya kewaye Samariya da yaƙi. 25 Aka yi babban yunwa a cikin birnin. Saboda daɗewar wannan kewayewar da aka yi wa birnin, sai yunwa ta ɓarke a birnin, har ana sayar da kan jaki a kan shekel tamanin, kashin kurciya kuma a kan shekel biyar.

26 Yayinda sarkin Isra’ila yake wucewa kusa da katanga, sai wata mace ta yi masa kuka ta ce, “Ka taimake ni, ranka yă daɗe, sarki!”

27 Sai sarki ya amsa ya ce, “In Ubangiji bai taimake ki ba, me zan iya yi? Ina da hatsi ko ruwan inabin da zan ba ki ne?” 28 Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Me ya faru?”

Sai ta amsa ta ce, “Wannan mace ta ce mini, ‘Kawo ɗanki mu ci yau, gobe kuwa mu ci ɗana.’ 29 Saboda haka muka dafa ɗana muka ci. Kashegari na ce mata, ‘Kawo ɗanki mu ci,’ amma ta ɓoye shi.”

30 Da sarki ya ji maganar macen sai ya yage rigunansa. Sa’ad da sarki yake wucewa a kan katangar birnin, sai mutane suka gan yana saye da rigar makoki a ciki. 31 Ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani har ma fiye da haka, idan ban cire kan Elisha ɗan Shafat yau ba!”

32 To, Elisha yana zaune a cikin gidansa, dattawa kuwa suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki ɗan aika yă ci gaba, amma kafin ɗan aikan yă isa, Elisha ya ce wa dattawan, “Kun gani ko? Wannan mai kisa ya aiko a cire mini kai! To, idan ɗan aikan ya iso, sai ku rufe ƙofar da ƙarfi, ku bar shi a waje. Ba da jimawa ba, maigidansa zai bi bayansa?” 33 Yana magana da su ke nan, sai ga ɗan aikan ya gangaro wajensa.

Sarki kuma ya ce, “Wannan bala’in daga wurin Ubangiji ya fito. Don me zan sa zuciya ga Ubangiji kuma?”

7:1 Sai Elisha ya ce, “Ku ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji ya ce, gobe war haka, za a sayar da mudun gari mai laushi a farashin shekel guda, mudu biyu na sha’ir kuma a shekel ɗaya a ƙofar birnin Samariya.”

2 Sai wani hafsa mataimakin sarki ya ce wa mutumin Allah, “Kai, ko da Ubangiji zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba!”

Sai Elisha ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba!”

3 To, akwai waɗansu kutare huɗu a ƙofar gari. Suka ce wa junansu, “Don me za mu zauna a nan sai mun mutu? 4 In muka ce, ‘Za mu shiga cikin birni’ yunwa tana can, za mu kuwa mutu. Idan kuwa muka zauna a nan, za mu mutu. Saboda haka, bari mu ƙetare zuwa sansanin Arameyawa mu miƙa kai. Idan suka bar mu da rai, to; idan kuwa suka kashe mu, shi ke nan.”

5 Da yamma sai suka tashi suka tafi sansanin Arameyawa. Yayinda suka shiga tsakiyar sansanin Arameyawa kuwa, sai suka tarar ba kowa a can, 6 gama Ubangiji ya sa rundunar Arameyawa suka ji motsin kekunan yaƙi, da motsin dawakai, da na babban rundunar sojoji, saboda haka suka ce wa juna; “Duba, sarkin Isra’ila ya ɗauka hayar sarakuna Hittiyawa da sarakunan Masarawa don su yaƙe mu!” 7 Saboda haka suka tashi, suka gudu da yamma, suka bar tentunansu, da dawakansu, da jakunansu. Suka bar sansanin yadda yake, suka gudu don su ceci rayukansu.

8 Da kutaren nan suka kai bakin sansanin, sai suka shiga wani tenti, suka ci, suka sha, suka kwashi azurfa, da zinariya, da riguna, suka tafi, suka ɓoye su. Sa’an nan suka koma, suka shiga wani tenti, sai suka kwashi kaya daga ciki, suka kuma ɓoye su.

9 Sa’an nan suka ce wa juna, “Ba mu yi abin kirki ba. Wannan rana ce ta albishiri amma muka yi shiru; in kuwa mun bari har gari ya waye, to, fa, wata masifa za tă fāɗo mana. Bari mu tafi nan take mu faɗa a fadan sarki.”

10 Saboda haka suka je suka kira masu tsaron ƙofar birni, suka ce musu, “Mun je sansanin Arameyawa, ga shi kuwa ba mu iske kowa a can ba, babu ko motsin wani, sai dai dawakai da jakuna a daure, tentunan kuwa suna nan yadda suke.” 11 Sai matsaran ƙofar suka sanar da labarin a cikin fada.

12 Sai sarki ya tashi da daren nan ya ce wa hafsoshinsa, “Na san abin da Arameyawan suke shiri! Sun san game da yunwar da muke ciki a nan, domin haka sun bar sansaninsu suka shiga jeji suka ɓuya, suna nufin sa’ad da muka fita daga birni, sai su kama mu da rai, sa’an nan su shiga birnin.”

13 Ɗaya daga cikin fadawan sarki ya ce, “A sa waɗansu mutane su ɗauki dawakai biyar da suka ragu cikin birni, idan ba su tsira ba, za su zama kamar sauran Isra’ilawan da suka riga suka mutu ne. Bari mu aika, mu gani.”

14 Saboda haka suka zaɓi kekunan yaƙi biyu tare da dawakansu, sarki kuwa ya aike su su bi bayan sojojin Arameyawa. Ya umarci masu tuƙinsu ya ce, “Ku je ku bincika abin da ya faru.” 15 Suka bi sawunsu har Urdun, suka ga tufafi da makamai barjat ko’ina a hanya waɗanda Arameyawa suka zubar yayinda suke gudu. Sai ’yan aika suka dawo suka ba wa sarki labari. 16 Sa’an nan jama’a suka fita suka kwashi ganima a sansanin Arameyawa. Aka kuwa sayar da gari mai laushi a farashin shekel guda, mudu biyu na sha’ir kuma a shekel guda, yadda Ubangiji ya faɗi.

17 Sai ya kasance cewa Sarki ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa’ad da sarki ya tafi wurinsa. 18 Haka kuwa ya kasance kamar yadda mutumin Allah ya ce wa sarki, “Gobe war haka, za a sayar da mudun gari shekel guda, mudun sha’ir biyu ma a shekel guda, a ƙofar Samariya.”

19 Hafsan ya riga ya ce wa mutumin Allah, “Kai, ko da Ubangiji zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba!” Mutumin Allah kuwa ya faɗa masa, “Za ka gani da idanunka sai dai ba za ka ci ba!” 20 Haka kuwa ya kasance, gama mutane sun tattake shi a hanyar shiga, har ya mutu.

8:1 To, Elisha ya riga ya ce wa matan da ya tā da ɗanta daga matattu, “Ki kwashe iyalinki ku tafi duk inda za ku tafi na ɗan lokaci, domin Ubangiji ya sa a yi yunwa na shekara bakwai a ƙasar.” 2 Sai macen ta yi kamar yadda mutumin Allah ya faɗa. Ita da iyalinta suka tafi ƙasar Filistiyawa suka zauna shekara bakwai.

3 A ƙarshen shekara bakwai ɗin sai ta dawo daga ƙasar Filistiyawa, ta kuma tafi wajen sarki ta roƙa a mayar mata da gidanta da filinta. 4 Sarki kuwa yana magana da Gehazi bawan mutumin Allah, ya ce masa, “Ba ni labarin dukan abubuwan banmamakin da Elisha ya yi.” 5 A sa’ad da Gehazi yana cikin ba shi labarin yadda Elisha ya tā da matacce ke nan, sai ga macen da aka tā da ɗanta daga matattu ta shigo don tă roƙi sarki yă mayar mata da gidanta da filinta.

Gehazi ya ce, “Ranka yă daɗe, ai, ga macen, ga kuma ɗan da Elisha ya tā da daga matattu.” 6 Sarki ya tambayi macen game da al’amarin, ita kuwa ta faɗa masa.

Sa’an nan ya sa wani hafsa yă dubi damuwarta ya kuma ce masa, “Ka mayar mata kome da yake nata, haɗe da dukan kuɗin da aka samo daga filin, daga ranar da ta bar ƙasar har yă zuwa yanzu.”