Misalin Mutumin Samariya Nagari
Yesu ya amsa wa wani masanin doka wanda ya yi tambaya game da rai na har abada, ya kuma ba da misalin mutumin Samariya nagari.
Wataƙila a Yahudiya
29 ko 28 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Luka 10:25–37
10:25 Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?”
26 Yesu ya amsa ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”
27 Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ”
28 Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”
29 Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”
30 Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa. 31 Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa. 32 Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa. 33 Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa. 34 Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa. 35 Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’
36 “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?”
37 Masanin dokoki ya amsa ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.”
Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”
Yesu Baƙon Marta da Maryamu Ne
Betani, kusa da Urushalima
Luka 10:38–42
10:38 Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”
41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”
Yesu Ya Sake Ba da Misalin Addu'a
Yesu ya sake ba da misalin addu'a, ya kuma ƙarfafa almajiransa su yi addu'a. Misalin aboki mai nacewa.
Wataƙila a Yahudiya
Luka 11:1–13
11:1 Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”
2 Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce,
“ ‘Ya Uba,
sunanka mai tsarki ne
mulkinka ya zo.
3 Ka ba mu kowace rana abincin yini.
4 Ka gafarta mana zunubanmu,
kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi.
Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”
5 Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku, 6 domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’ 7 Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’ 8 Ina gaya muku, ko da yake ba zai so ya tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.
9 “Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 10 Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.
11 “Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon, 12 ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? 13 In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”