Ƙaura da Akwatin Alkawari (continued)

1045 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 106

1 Yabi Ubangiji.

Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;

ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

2 Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji

ko yă furta cikakken yabonsa?

3 Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci,

waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai.

4 Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka,

ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su,

5 don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka,

don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka

in kuma shiga gādonka cikin yin yabo.

6 Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi;

mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.

7 Sa’ad da kakanninmu suke a Masar,

ba su damu da mu’ujizanka ba;

ba su tuna yawan alheranka ba,

suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.

8 Duk da haka ya cece su saboda sunansa,

don yă sanar da ikonsa mai girma.

9 Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe;

ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.

10 Ya cece su daga hannun maƙiyi;

daga hannun abokin gāba ya fanshe su.

11 Ruwaye suka rufe abokan gābansu;

babu ko ɗaya da ya tsira.

12 Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa

suka kuma rera yabonsa.

13 Amma nan da nan suka manta abin da ya yi

ba su kuwa jira shawararsa ba.

14 A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su

a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.

15 Sai ya ba su abin da suka roƙa,

amma ya aika musu da muguwar cuta.

16 A sansani suka ji kishin Musa

da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.

17 Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan

ta binne iyalin Abiram.

18 Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu;

harshen wuta ya cinye mugaye.

19 A Horeb suka yi ɗan maraƙi

suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada.

20 Suka sauke Ɗaukakarsu

saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa.

21 Suka manta da Allahn da ya cece su,

wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar,

22 mu’ujizai a ƙasar Ham

ayyukan banrazana a Jan Teku.

23 Don haka ya ce zai hallaka su,

amma Musa, zaɓaɓɓensa,

ya yi godo a gabansa

don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.

24 Sai suka rena ƙasa mai ni’ima;

ba su gaskata alkawarinsa ba.

25 Suka yi gunaguni a tentunansu

ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.

26 Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu

cewa zai sa su mutu a cikin hamada,

27 ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai

ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe.

28 Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor

suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai;

29 suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu,

sai annoba ta ɓarke a cikinsu.

30 Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki,

sai annobar ta daina.

31 An ayana masa wannan a matsayin adalci

har zamanai marar matuƙa masu zuwa.

32 A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi,

sai wahala ta zo wa Musa saboda su;

33 saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah,

har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa.

34 Ba su hallakar da mutanen

yadda Ubangiji ya umarce su ba,

35 amma suka yi cuɗanya da al’ummai

suka ɗauki al’adunsu.

36 Suka yi wa gumakansu sujada,

waɗanda suka zama tarko gare su.

37 Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya

’yan matansu kuma ga aljanu.

38 Suka zub da jini marar laifi,

jinin ’ya’yansu maza da mata,

waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana,

ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.

39 Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi;

ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.

40 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa

ya ji ƙyamar gādonsa.

41 Ya miƙa su ga al’ummai,

maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.

42 Abokan gābansu suka danne su

suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.

43 Sau da yawa ya cece su,

amma sun nace su yi tawaye

suka kuma lalace cikin zunubinsu.

44 Amma ya lura da wahalarsu

sa’ad da ya ji kukansu;

45 saboda su ya tuna da alkawarinsa

kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.

46 Ya sa aka ji tausayinsu

a wurin dukan waɗanda suka kame su.

47 Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu,

ka kuma tattara mu daga al’ummai,

don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya

mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.

48 Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,

daga madawwami zuwa madawwami.

Bari dukan mutane su ce, “Amin!”

Yabo ga Ubangiji.

2 Sama’ila 6:20–23

20 Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal ’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa ’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!”

21 Dawuda ya ce wa Mikal, “Na yi rawana domin in girmama Ubangiji ne, wanda ya zaɓe ni a maimakon mahaifinki ko wani daga cikin dukan gidansa, shi ne kuma ya sa ni sarki a kan Isra’ila, mutanen Ubangiji, zan yi biki a gaban Ubangiji. 22 Zan ma mai da kaina abin reni fiye da haka, za a kuma zama abin reni a gare ki. Amma waɗannan bayi ’yan matan da kika yi magana a kai, za su gan ni da martaba.”

23 Mikal ’yar Shawulu kuwa ba tă haifi ɗa ba har mutuwarta.

1 Tarihi 13:5–14

5 Saboda haka Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa, daga Kogin Shihor a Masar zuwa Lebo Hamat, don su kawo akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim. 6 Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan.

7 Suka ɗauki akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab a kan sabon keken shanu, Uzza da Ahiyo ne suke lura da shi. 8 Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi shagali da dukan ƙarfinsu a gaban Allah, tare da waƙoƙi da garayu, molaye, ganguna, kuge da ƙahoni.

9 Sa’ad da suka kai masussukar Kidon, Uzza ya miƙa hannunsa don yă gyara akwatin alkawarin, gama shanun sun yi tuntuɓe. 10 Sai fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Uzza, ya kuma buge shi domin ya sa hannunsa a kan akwatin alkawarin. Sai ya mutu a can a gaban Allah.

11 Ran Dawuda ya ɓace domin Ubangiji ya husata a kan Uzza, kuma har wa yau ana ce da wannan wuri Ferez Uzza.

12 Dawuda ya ji tsoron Allah a wannan rana ya kuma yi tambaya, “Yaya zan taɓa kawo akwatin alkawarin Allah gare ni?” 13 Don haka bai ɗauki akwatin alkawarin ya kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka, ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat. 14 Akwatin Alkawarin Allah ya zauna tare da iyalin Obed-Edom a gidansa wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkaci gidan Obed-Edom da kome da yake da shi.