An Keɓe Lawiyawa
1490 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Yi magana da Haruna, ka ce masa, ‘Sa’ad da za ka shisshirya fitilun nan bakwai, ka shirya su yadda za su fuskanci gaba domin haskensu yă haskaka ta gaba.’ ”
3 Haka kuwa Haruna ya yi; ya shisshirya fitilun yadda za su fuskanci gaba a kan wurin ajiye fitilan, kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa. 4 Ga yadda aka yi wurin ajiye fitilan. An ƙera shi da zinariya daga gindinsa har zuwa sama inda ya buɗu. Aka ƙera wurin ajiye fitilan yadda Ubangiji ya nuna wa Musa.
5 Ubangiji ya ce wa Musa, 6 “Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su. 7 Ga yadda za ka tsarkake su, ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa; ka sa su aske jikunansu duka su kuma wanke tufafinsu, ta haka za su tsarkake kansu. 8 Ka sa su ɗauki ɗan bijimi tare da lallausan garin hadaya, kwaɓaɓɓe da mai; sa’an nan, kai kuma ka ɗauki ɗan bijimi na biyu na hadaya don zunubi. 9 Ka kawo Lawiyawa a gaban Tentin Sujada, ka kuma kira taron Isra’ilawa duka. 10 Za ka kawo Lawiyawa a gaban Ubangiji, Isra’ilawa kuma za su ɗibiya musu hannuwansu. 11 Haruna zai miƙa Lawiyawa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa daga Isra’ilawa, saboda a shirya su domin aikin Ubangiji.
12 “Bayan Lawiyawa sun ɗibiya hannuwansu a kan bijiman, sai ka yi amfani da ɗaya a matsayin hadaya don zunubi ga Ubangiji, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa, don yin kafara saboda Lawiyawa. 13 Ka kuma sa Lawiyawa su tsaya a gaban Haruna da ’ya’yansa, sai ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. 14 Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, Lawiyawa za su zama nawa.
15 “Bayan ka tsarkake Lawiyawa, ka kuma miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, sai su zo su yi aikinsu a Tentin Sujada. 16 Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato, dukan ’ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa. 17 Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe ’ya’yan fari a Masar, na keɓe ’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina. 18 Na kuma ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari maza a Isra’ila. 19 Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da ’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.”
20 Musa, Haruna da kuma dukan taron Isra’ilawa, suka yi da Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarci Musa. 21 Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma wanke tufafinsu. Sai Haruna ya miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, ya kuma yi kafara saboda su don yă tsarkake su. 22 Bayan haka, sai Lawiyawa suka zo don su yi aikinsu a Tentin Sujada, a ƙarƙashin Haruna da ’ya’yansa. Suka yi da Lawiyawa kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
23 Ubangiji ya ce wa Musa, 24 “Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada, 25 amma in suka kai shekaru hamsin da haihuwa, dole su huta daga wannan aiki na yau da kullum, su kuma daina aiki. 26 Za su iya taimakon ’yan’uwansu cikin tafiyar da ayyuka a Tentin Sujada, amma su kansu ba za su yi aikin ba. Haka fa za ka ba wa Lawiyawa aikinsu.”
Amfani da Kakakan Azurfa
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Ka ƙera kakaki guda biyu na azurfa, ka kuma yi amfani da su don kira taron jama’a wuri ɗaya, don kuma ka riƙa sanar da su lokacin tashi daga sansani. 3 Sa’ad da aka busa su biyu, dukan jama’a za su taru a gabanka a ƙofar Tentin Sujada. 4 In ɗaya ne kaɗai aka busa, sai shugabannin kabilan Isra’ila, su taru a gabanka. 5 Sa’ad da aka ji karar busar kakaki, sai sansanin da yake a gabashi, su kama hanya. 6 A kara ta biyu, sansanin da yake a kudanci, su kama hanya. Busan kakaki zai zama alama ta kama hanya. 7 In don a tara jama’a ne, sai a busa kakaki, amma ba da irin alama ɗaya ba.
8 “’Ya’yan Haruna, firistoci ne, za su busa kakaki. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla gare ku da kuma tsararraki masu zuwa. 9 Duk lokacin da za ku tafi yaƙi a ƙasarku, in akwai waɗansu da suke matsa muku, za ku yi amfani da waɗannan kakaki ta wurin hura su, alama ce, cewa za a je yaƙi. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, yă cece ku daga maƙiyanku. 10 Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
Yadda Girgije Ya Jagoranci Mutane
15 A ranar da aka kafa Tenti na Alkawari, sai girgije ya rufe shi. Daga yamma har safe, girgijen da yake bisa tabanakul ya yi kama da wuta. 16 Haka ya ci gaba da kasancewa; girgijen ya rufe shi, da dare kuma sai ya yi kamar wuta. 17 Duk sa’ad da aka ɗaga girgijen daga Tentin, sai Isra’ilawa su kama hanya; duk inda girgijen ya tsaya, a nan Isra’ilawa za su yi sansani. 18 Da umarnin Ubangiji, Isra’ilawa suke tashi. Da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana tsaye a bisa tabanakul, sukan yi ta zamansu a sansanoni. 19 Sa’ad da girgijen ya ci gaba da kasancewa a bisan tabanakul na dogon lokaci, Isra’ilawa sukan bi umarnin Ubangiji, ba kuwa za su tashi ba. 20 Wani lokaci girgijen yakan yi ’yan kwanaki ne kawai a bisa tabanakul; da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani da umarninsa kuma su tashi. 21 Wani lokaci girgijen yakan zauna daga yamma har safiya ne kawai, sa’ad da kuma aka ɗaga shi da safe, sai su kama hanya. Ko da rana, ko da dare, duk sa’ad da aka ɗaga girgijen, sai su ma su tashi. 22 Ko girgijen ya yi kwana biyu a bisa tabanakul, ko wata guda, ko shekara, Isra’ilawa za su zauna a sansani ba kuwa za su tashi ba; amma sa’ad da aka ɗaga shi, sai su kuma su tashi. 23 Da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani, da umarninsa kuma sukan tashi. Sukan bi umarnin Ubangiji, bisa ga umarninsa ta wurin Musa.