Sa'o'i Uku na Farko a kan Gicciye

Daga ƙarfe tara na safe har zuwa tsakar rana a Jumma'a (kalmomi uku na Yesu; sojoji suna caca domin rigar Yesu; rubutun da ke kan gicciye; taron jama'a, Majalisa, sojoji, har ma da 'yan fashi biyun da ke kowane gefen Kiristi suna yi wa Yesu ba'a)

30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mattiyu 27:35–44

27:35 Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.

36 Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa.

37 Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce,

Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.

38 An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.

39 Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai, 40 suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”

41 Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa, 42 “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

43 Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”

44 Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.

Markus 15:24–32

15:24 Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.

25 Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi. 26 Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce,

Sarkin Yahudawa.

27 Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.

29 Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, 30 sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”

31 Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa!

32 Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.

Luka 23:34, 38, 35–37, 39–43

23:34 Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

38 Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce,

Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.

35 Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”

36 Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami.

37 Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”

39 Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”

40 Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi? 41 Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”

42 Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.”

43 Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”

Yohanna 19:18, 23–24, 19–22, 25–27

19:18 Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.

23 Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.

24 Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.”

Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce,

“Suka rarraba tufafina a junansu,

suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.”

Abin da sojojin suka yi ke nan.

19 Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne,

Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa.

20 Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik.

21 Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.”

22 Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”

25 To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26 Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27 ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.