Mutuwar Samson

Mutuwar Samson, tare da wasu al’amura.

1117 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mahukunta 16

1 Wata rana Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa. Ya shiga wurinta ya kwana. 2 Aka gaya wa mutanen Gaza, “Ai, Samson yana a nan!” Saboda haka suka zo suka kewaye wurin suka yi kwanto dukan dare a bakin ƙofar birni. A daren nan ba su motsa nan da can ba, suna cewa, “Gari yana wayewa za mu kashe shi.”

3 Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakiyar dare. Sa’an nan ya tashi ya kama ƙofofin birnin, tare da madogarai biyunsu, ya tumɓuke, ya aza su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a fuskantar Hebron.

4 Bayan ɗan lokaci, sai ya shiga ƙaunar wata mace, mai suna Delila a Kwarin Sorek. 5 Sai shugabannin Filistiyawa suka tafi wurinta suka ce, “Ki yi ƙoƙari ki ga ko za ki rarrashe shi yă nuna miki asirin ƙarfinsa da yadda za mu iya shan ƙarfinsa don mu ɗaura shi mu yi nasara a kansa. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu ɗari ɗaya na azurfa.”

6 Saboda haka Delila ta ce wa Samson, “Ka faɗa miki asirin ƙarfinka da yadda za a ɗaura ka a yi nasara a kanka.”

7 Samson ya ce mata, “In wani ya ɗaura ni da sababbin igiyoyin da ba su bushe ba, zan zama marar ƙarfi kamar kowa.”

8 Sa’an nan shugabannin Filistiyawa suka kawo mata sababbin igiyoyi guda bakwai da ba su bushe ba, sai ta daure shi da su. 9 Da mutane a ɓoye a cikin ɗaki tare da ita, sai ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Da jin haka sai ya tsintsinke igiyoyin kamar zaren da ya yi kusa da harshen wuta. Saboda haka asirin ƙarfinsa bai tonu ba.

10 Sa’an nan Delila ta ce wa Samson, “Ka mai da ni wawiya; ka ruɗe ni. Yanzu, ka gaya mini yadda za a daure ka.”

11 Ya ce, “In wani ya ɗaura ni sosai da sababbin igiyoyin da ba a taɓa amfani da su ba, zan zama marar ƙarfi kamar kowa.”

12 Saboda haka Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi ta ɗaura shi da su. Sa’an nan, tare da mutane a ɓoye a ɗakin, ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Amma sai ya tsintsinke su kamar zare.

13 Sa’an nan Delila ta ce, “Har yanzu, ka mai da shashasha, kana mai da ni wawiya kana kuma yin mini ƙarya. Ka gaya mini yadda za a daure ka mana.”

Ya ce mata, “In kin yi kitson gashin kaina guda bakwai kika ɗaura su da zare kika buga su da akwasha, zan rasa ƙarfi in zama kamar kowa.” Saboda haka yayinda yake barci, sai Delila ta yi kitson gashin kansa guda bakwai ta ɗinka su da zare, 14 ta kuma ɗaura su da akwasha.

Ta sāke yin ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka.” Ya tashi daga barcinsa ya tumɓuke akwashan tare da zaren da aka ɗaura gashin kansa da su.

15 Sa’an nan ta ce masa, “Yaya kake cewa kana sona alhali ba ka yarda da ni ba? Wannan shi ne sau na uku kana mai da ni wawiya kuma ba ka nuna mini asirin ƙarfinka ba.” 16 Da irin wannan fitina ta tsokane shi kwana da kwanaki har sai da ya gaji kamar zai mutu.

17 Saboda haka sai ya faɗa mata kome ya ce, “Ba a taɓa sa reza a kaina ba, domin ni Naziri ne keɓaɓɓe ga Allah tun haihuwa. In kuwa an aske kaina, ƙarfina zai rabu da ni, sai in zama kamar kowa.”

18 Da Delila ta gane ya gaya mata kome yanzu, sai ta aika saƙo zuwa ga shugabannin Filistiyawa ta ce, “Ku ƙara zuwa sau ɗayan nan, ai, ya gaya mini kome.” Saboda haka shugabannin Filistiyawa suka dawo tare da azurfa a hannuwansu. 19 Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.

20 Sa’an nan ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!”

Sai ya farka daga barci yana tsammani cewa, “Zan fita kamar dā in miƙe jikina.” Amma bai san cewa Ubangiji ya rabu da shi ba.

21 Sa’an nan Filistiyawa suka fizge shi, suka ƙwaƙule idanunsa suka gangara da shi zuwa Gaza. Da suka daure shi da sarƙoƙin tagulla, sai aka sa shi yana niƙa a kurkuku. 22 Amma gashi kansa ya fara tohuwa kuma bayan an aske shi.

23 To, sai Filistiyawa suka taru don su miƙa hadaya ga Dagon allahnsu su kuma yi biki cewa, “Allahnmu ya bashe abokin gābanmu Samson a hannuwanmu.”

24 Sa’ad da mutane suka gan shi, sai suka yabi allahnsu, suna cewa,

“Allahnmu ya bashe abokin gābanmu

a hannunmu,

wanda ya lalace ƙasarmu

ya kuma raɓanya kisan mutanenmu.”

25 Yayinda suke cikin farin ciki, sai suka yi ihu, suka ce, “Fito mana da Samson yă yi mana wasa.” Saboda haka aka zo da Samson daga kurkuku, shi kuwa ya yi wasa a gabansu.

Sa’ad da suka tsai da shi a tsakanin ginshiƙai, 26 sai Samson ya ce wa bawan da ya riƙe hannunsa, “Ka kai ni inda zan taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da wannan haikali, don in jingina a kai.” 27 To, haikalin ya cika da mutane maza da mata; dukan shugabannin Filistiyawa kuwa suna a can, a bisan rufin kuwa akwai mutum wajen dubu uku maza da mata suna kallon Samson yana wasa. 28 Sa’an nan Samson ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ya Allah ka tuna da ni, ka ƙarfafa ni sau ɗaya nan kaɗai, ka bar ni da bugu ɗaya kawai in ɗauki fansa a kan Filistiyawa domin idanuna.” 29 Sa’an nan Samson ya kai hannuwansa ga ginshiƙan waɗanda haikalin yake a kai, ya jingina jikinsa, hannunsa dama yana a ɗaya, hannun hagu kuma na ɗayan, 30 Samson ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Sa’an nan da dukan ƙarfinsa ya tura haikali ya fāɗa a kan shugabanni da dukan mutanen da suke ciki. Ta haka ya kashe mutane da yawa fiye da yayinda yake da rai.

31 Sa’an nan ’yan’uwansa da dukan dangin mahaifinsa suka gangaro don su ɗauke shi. Suka kawo shi suka binne tsakanin Zora da Eshtawol a kabarin Manowa mahaifinsa. Ya yi mulkin Isra’ila shekara ashirin.

Mahukunta 15:20

20 Samson kuwa ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin a zamanin Filistiyawa.

Mutuwar Eli 1116 kafin haihuwar Almasihu

1 Sama’ila 4

1 Duk sa’ad da Sama’ila ya yi magana dukan Isra’ila sukan saurare shi.

Isra’ilawa suka fita yaƙi da Filistiyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani a Ebenezer, Filistiyawa kuma a Afek. 2 Filistiyawa suka tunƙuro mayaƙansu domin su sadu da Isra’ilawa, yaƙi kuwa ya yi tsanani har Isra’ilawa suka sha kashi a hannun Filistiyawa. Filistiyawa suka kashe Isra’ilawa kusan mutum dubu huɗu a bakin dāgā. 3 Lokacin da mayaƙan suka komo sansani, dattawan Isra’ilawa suka yi tambaya suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa muka sha ɗibga a hannun Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo. Domin yă tafi tare da mu yă ba mu nasara kan abokan gābanmu.”

4 Saboda haka mutanen suka aika waɗansu maza zuwa Shilo, suka kuwa tafi suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Maɗaukaki wanda yake zaune tsakanin Kerubobi. ’Ya’yan Eli biyun nan Hofni da Finehas suna wurin tare da akwatin alkawarin Ubangiji.

5 Da aka shigo da akwatin alkawarin Ubangiji a cikin sansani, sai Isra’ilawa suka tā da babbar murya har ƙasa ta jijjiga. 6 Da jin wannan, Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Me ke kawo wannan ihu mai ƙarfi haka a sansanin Isra’ilawa?”

Da suka gane cewa akwatin alkawarin Ubangiji ne ya shiga sansanin, 7 sai Filistiyawa suka ji tsoro, suka ce, “Wani allah ya shiga cikin sansanin. Mun shiga uku! Ba a taɓa yin wani abu haka ba. 8 Kaiton mu! Wa zai kuɓutar da mu daga hannun waɗannan manyan alloli? Su ne allolin da suka buga Masarawa da irin annoba masu yawa a jeji. 9 Ku yi ƙarfin hali, ku yi mazantaka, ku Filistiyawa, domin kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suke a gare ku. Ku yi mazantaka, ku yi yaƙi.”

10 Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin. 11 Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe ’ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas.

12 A wannan rana wani mutumin Benyamin ya ruga da bakin dāgā ya shigo Shilo, taguwarsa a yage, kansa kuma a rufe da ƙasa. 13 Da ya iso sai ga Eli zaune a kujera kusa da hanya yana kallo, domin tsoron da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shigo a garin ya ba da labarin abin da ya faru sai dukan gari ya ruɗe da ihu.

14 Eli ya ji ihun ya yi tambaya ya ce, mene ne dalilin wannan ihu?

Mutumin ya rugo wurin Eli, 15 wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani.

16 Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.”

Eli ya ce, “Me ya faru da ’ya’yana?”

17 Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

18 Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.

19 Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta. 20 Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.

21 Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta. 22 Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”