Babbar Gwagwarmayar Ikilisiya da Abokan Gabanta

Annabci game da babbar gwagwarmayar da za a yi nan gaba tsakanin ikilisiya da abokan gabanta, da kuma juyowar Yahudawa zuwa ga bangaskiya a kwanakin ƙarshe.

587 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ezekiyel 38–39

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Gog, na ƙasar Magog, babban sarkin Meshek da Tubal; ka yi annabci a kansa 3 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal. 4 Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in fitar da kai tare da dukan sojojinka, dawakanka, mahayan dawakanka saye da makamai, da kuma jama’a mai girma masu riƙe da garkuwoyi manya da ƙanana, dukansu da takuba a zāre. 5 Farisa, Kush da Fut za su kasance tare da su, duka riƙe da garkuwoyi da hulunan kwano, 6 haka ma Gomer da dukan sojojinsa, da Bet Togarma daga can arewa tare da dukan sojojinsa, al’ummai masu yawa tare da kai.

7 “ ‘Ka shirya; ka kintsa, kai da dukan jama’arka da suka taru kewaye da kai, ka kuma zama mai ba su umarni. 8 Bayan kwanaki masu yawa za a kira ka. A shekaru masu zuwa za ka kai hari a ƙasar da ta farfaɗo daga yaƙi, wadda aka tattara mutanenta daga al’ummai masu yawa zuwa duwatsun Isra’ila, dā kango ne sosai. An fitar da su daga al’ummai, yanzu kuwa dukansu suna zama lafiya. 9 Kai da dukan sojojinka da kuma al’ummai masu yawa da suke tare da kai za ku haura, kuna cin gaba kamar hadari; za ku zama kamar girgijen da yake rufewa ƙasa.

10 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, tunani zai shiga cikin zuciyarka za ka kuma ƙirƙiro muguwar dabara. 11 Za ka ce, “Zan kai hari wa ƙasar da ƙauyukanta ba su da katanga; zan fāɗa wa mutanen da suke zamansu kurum cikin salama, dukansu suna zama babu katanga babu ƙofofi ko ƙyamare. 12 Zan washe in kwashe ganima in kuma juye hannuna gāba da kufai da aka sāke zaunar da mutanen da aka tattara daga al’ummai, masu yawan shanu da kayayyaki, masu zama a tsakiyar ƙasa.” 13 Sheba da Dedan da ’yan kasuwar Tarshish da dukan ƙauyukanta za su ce maka, “Ka zo ka kwashe ganima ne? Ka tattara jama’arka don ka yi waso, ka kuma kwashe azurfa da zinariya, ka kwashe shanu da kayayyaki ka kuma ƙwace ganima mai yawa?” ’

14 “Saboda haka ɗan mutum, ka yi annabci ka ce wa Gog, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, sa’ad da mutanena Isra’ila suna zaman lafiya, ba za ka sani ba? 15 Za ka zo daga wurinka a can arewa, kai da al’ummai masu yawa tare da kai, dukansu suna hawan dawakai, jama’a mai yawa, babbar runduna. 16 Za ka ci gaba a kan mutanena Isra’ila kamar yadda girgijen yakan rufe ƙasa. A kwanaki masu zuwa, ya Gog, zan kawo ka, ka yi yaƙi da ƙasata, domin al’ummai su san ni sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinka a gabansu.

17 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba kai ba ne na yi magana da kai a kwanakin dā ta wurin bayina annabawan Isra’ila? A lokacin sun yi annabci shekaru masu yawa cewa zan kawo ka, ka yaƙe su. 18 Ga abin da zai faru a ranar. Sa’ad da Gog ya fāɗa wa ƙasar Isra’ila, fushina mai zafi zai ƙuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 19 Cikin kishina da hasalata mai zafi zan furta cewa a wannan lokaci za a yi babbar girgizar ƙasa a ƙasar Isra’ila. 20 Kifin teku, tsuntsayen sarari, namun jeji, kowace halitta mai rarrafe da kuma dukan mutane a duniya za su yi rawar jiki a gabana. Za a tumɓuke duwatsu, a ragargaza tsaunuka, kuma kowane bango zai fāɗi ƙasa. 21 Zan kira takobi a kan Gog a dukan duwatsuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Kowane takobin mutum zai yi gāba da ɗan’uwansa. 22 Zan yi hukunci a kansa da annoba da kuma zub da jini; zan yi ruwa mai yawa da ƙanƙara da kibiritu mai cin wuta a kansa da a kan sojojinsa da kuma a kan al’ummai masu yawa da suke tare da shi. 23 Ta haka zan nuna girmana da kuma tsarkina, zan sanar da kaina a gaban al’ummai masu yawa. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’

39:1 “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal. 2 Zan juya ka in kuma ja ka. Zan kawo ka daga can arewa in aike ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra’ila. 3 Sa’an nan zan karya bakan da take a hannun hagunka, in sa kibiyoyin da suke a hannun damanka su fāɗi. 4 A kan duwatsun Isra’ila za ka fāɗi, kai da sojojinka da kuma al’ummai da suke tare da kai. Zan bayar da kai ka zama abinci ga tsuntsaye da namun jeji masu cin nama. 5 Za ka mutu a fili, gama haka ni na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 6 Zan aika da wuta a kan Magog da kuma a kan waɗanda suke zama lafiya a bakin teku, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.

7 “ ‘Zan sanar da sunana mai tsarki a cikin mutanena Isra’ila. Ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, kuma al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji Mai Tsarki ne a cikin Isra’ila. 8 Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ranar da na yi magana ke nan.

9 “ ‘Sa’an nan waɗanda suke zama a garuruwan Isra’ila za su fita su tattara makamai su hura wuta da su su kuma ƙone su, manya da ƙanana garkuwoyi, bakkuna da kibiyoyi, kulake da māsu. Shekara bakwai za su yi amfani da su don hura wuta. 10 Ba za su yi wahalar zuwa jeji don neman itacen hura wuta ba, domin za su yi amfani da makamai don hura wuta. Za su kuma washe waɗanda suka washe su ganima, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

11 “ ‘A ranar zan yi wa Gog makabarta a cikin Isra’ila, a kwarin waɗanda suke tafiya wajen gabashin Teku. Za tă tare hanyar matafiya, domin za a binne Gog da dukan mutanensa a can. Ta haka za a kira wurin Kwarin Haman Gog.

12 “ ‘Watanni bakwai gidan Isra’ila zai yi ta binne su don a tsarkake ƙasar. 13 Dukan mutanen ƙasar za su binne su, kuma ranar da za a ɗaukaka ni za tă zama ranar tuni a gare su, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

14 “ ‘Za a ɗauki mutane kullum don tsabtacce ƙasar. Waɗansu za su ratsa ƙasar, ƙari da waɗannan, waɗansu za su binne gawawwakin da suka ragu a ƙasar. A ƙarshen watanni bakwai ɗin za su fara bincikensu. 15 Yayinda suke ratsa ƙasar, in waninsu ya ga ƙashin mutum, zai kafa shi kamar alama a gefe sai masu haƙa kabari sun binne shi a Kwarin Haman Gog. 16 Akwai wani garin da ake kira Hamona zai kasance a can. Ta haka za su tsabtacce ƙasar.’

17 “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan namun jeji, ‘Ku taru ku kuma zo wuri ɗaya daga ko’ina don hadayar da nake shirya muku, babbar hadaya a kan duwatsun Isra’ila. A can za ku ci nama ku kuma sha jini. 18 Za ku ci naman manyan mutane ku kuma sha jinin sarakunan duniya sai ka ce an yanka raguna da ’yan tumaki, awaki da bijimai, dukansu turkakkun dabbobi daga Bashan. 19 A hadayar da nake shirya muku, za ku ci kitse sai kun ƙoshi ku kuma sha jini sai kun bugu. 20 A teburina za ku ci iya ƙoshiyarku da naman jama’a da kuma mahaya, manyan mutane da sojoji na kowane iri,’ in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

21 “Zan nuna ɗaukakata a cikin al’ummai, kuma dukan al’ummai za su ga hukuncin da zan yi da kuma hannu mai nauyin da zan ɗora a kansu. 22 Daga wannan rana zuwa gaba gidan Isra’ila zai san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu. 23 Al’ummai kuma za su san cewa mutanen Isra’ila sun tafi zaman bauta saboda zunubinsu, domin sun yi rashin aminci gare ni. Saboda haka na kawar da fuskata daga gare su na miƙa su ga abokan gābansu, suka kuwa mutu ta takobi. 24 Na yi da su gwargwadon rashin tsabtarsu da laifofinsu, na kuma kawar da fuskata daga gare su.

25 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan komo da Yaƙub daga zaman bauta zan kuma yi wa dukan Isra’ila jinƙai, zan kuma yi kishi saboda sunana mai tsarki. 26 Za su manta da kunyar da suka sha da dukan rashin amincin da suka nuna mini sa’ad da suke zama lafiya a ƙasarsu inda ba wanda zai tsorata su. 27 Sa’ad da na komo da su daga al’ummai na kuma tattara su daga ƙasashen abokan gābansu, zan nuna kaina mai tsarki ta wurinsu a gaban al’ummai masu yawa. 28 Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, gama ko da yake na tura su zaman bauta a cikin al’ummai, zan tattara su zuwa ƙasarsu, ba tare da barin wani a baya ba. 29 Ba zan ƙara kawar da fuskata daga gare su, gama zan zuba Ruhuna a kan gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”