Haihuwar Sama’ila

1155 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Sama’ila 1:1–2:21

1 Akwai wani mutum daga Ramatayim, mutumin Zuf daga ƙasar tuddan Efraim, sunansa Elkana, ɗan Yeroham, shi jikan Elihu ɗan Tohu, tattaɓa kunnen Zuf, mutumin Efraim. 2 Yana da mata biyu, ɗaya sunanta Hannatu, ɗayan kuwa ana kiranta Feninna. Ita Feninna tana da ’ya’ya, amma Hannatu ba ta da ’ya’ya.

3 Shekara-shekara wannan mutum yakan haura daga garinsa zuwa Shilo domin yin sujada da miƙa hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki. A can kuwa ’ya’yan Eli maza biyu, Hofni da Finehas su ne firistoci na Ubangiji. 4 Duk sa’ad da rana ta kewayo don Elkana yă miƙa hadaya, yakan ba da kashin nama ga matarsa Feninna da dukan ’ya’yanta maza da mata. 5 Amma Hannatu kuwa sai yă ba ta babban rabo gama yana ƙaunarta ko da yake Ubangiji ya kulle mahaifarta. 6 Saboda Ubangiji ya kulle mahaifarta, sai kishiyarta ta dinga tsokanarta don tă ba ta haushi. 7 Wannan ya ci gaba shekara da shekaru. Duk lokacin da Hannatu ta haura zuwa haikalin Ubangiji, sai kishiyarta tă tsokane ta har tă yi ta kuka tă kuma ƙi cin abinci. 8 Elkana mijinta kuwa yakan ce mata, “Hannatu don me kike kuka? Me ya sa ba za ki ci abinci ba? Don me kika karaya? Ashe, ban fi ’ya’ya goma a gare ki ba?”

9 Wata rana sa’ad da suka gama ci da sha a Shilo, Hannatu ta miƙe tsaye. Eli firist kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar haikalin Ubangiji. 10 A cikin baƙin ciki, Hannatu ta yi kuka mai zafi ta yi addu’a ga Ubangiji. 11 Ta yi ta cewa, “Ya Ubangiji Maɗaukaki. In har ka dubi baƙin cikin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuma manta da baiwarka ba, amma ka ba ta ɗa, ni ma zan miƙa shi ga Ubangiji dukan rayuwarsa, aska kuwa ba za tă taɓa kansa ba.”

12 Yayinda take addu’a ga Ubangiji, Eli ya lura da bakinta. 13 Hannatu tana addu’a a zuci, ba a jin muryarta, sai leɓunanta ne kawai suna motsi. Eli kuwa ya yi tsammani ta bugu ne. 14 Sai ya ce mata, “Har yaushe za ki ci gaba da maye? Ki daina shan ruwan inabi.”

15 Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne. 16 Kada ka yi zato baiwarka ’yar iska ce. Ina addu’a a nan saboda yawan azaba da baƙin cikin da nake ciki.”

17 Eli ya ce, “In haka ne, to, ki sauka lafiya, Allah na Isra’ila kuma yă ba ki abin da kika roƙa daga gare shi.”

18 Ta ce, bari baiwarka tă sami tagomashi a idonka. Sai ta yi tafiyarta ta je ta ci wani abu, fuskarta kuwa ba tă ƙara kasance da baƙin ciki ba.

19 Kashegari da sassafe suka tashi suka yi sujada a gaban Ubangiji, sai suka koma garinsu a Rama. Elkana kuwa ya kwana da matarsa Hannatu, Ubangiji kuma ya tuna da ita. 20 Ana nan sai Hannatu ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Ta ba shi suna Sama’ila; tana cewa, “Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji.”

21 Da shekara ta kewayo, sai Elkana da iyalinsa suka sāke tafi Shilo domin su yi hadaya ga Ubangiji, yă kuma cika alkawarin da ya yi. 22 Hannatu kuwa ba tă bi su ba. Ta gaya wa mijinta cewa, “Sai bayan na yaye yaron, zan kai shi in miƙa shi a gaban Ubangiji, yă kuma kasance a wurin koyaushe.”

23 Elkana mijinta ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi miki kyau. Ki jira har sai bayan kin yaye shi. Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Saboda haka matar ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta har ta yaye shi.

24 Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo. 25 Bayan an yanka bijimin, sai suka kawo yaron wurin Eli. 26 Sai ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ba ka gane ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana addu’a ga Ubangiji. 27 Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi. 28 Saboda haka, na ba da shi ga Ubangiji muddin ransa, zai zama na Ubangiji.” A can kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.

2:1 Sai Hannatu ta yi addu’a ta ce,

“Zuciyata tana farin ciki a cikin Ubangiji;

a cikin Ubangiji an sa ina jin daɗi ƙwarai.

Na buɗe bakina na yi wa abokan gābana dariya.

Kai! Ina murna domin ka cece ni!

2 “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji

babu wani, in ban da kai;

babu wani dutse kamar Allahnmu.

3 “Ka daina maganganu na girman kai

ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai;

gama Ubangiji Allah ne masani

daga gare shi kuma ana auna ayyuka.

4 “An kakkarya bakkuna masu yaƙi,

amma su da ka raunana an ba su makaman ƙarfi.

5 Waɗanda a dā suna da abinci sosai; yanzu suna ƙodago saboda abinci,

masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa.

Ita da take bakararriya, ta haifi ’ya’ya bakwai

amma ita da tana da ’ya’ya da yawa, ta zama mai baƙin ciki.

6 “Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar

yana kai ga kabari, yă kuma tā da.

7 Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya;

yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka.

8 Yakan tā da matalauci daga ƙura,

yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka;

yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki;

yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka.

“Harsashin duniya na Ubangiji ne;

a bisansu ne ya kafa duniya.

9 Zai kiyaye ƙafafun masu tsarki,

amma mugaye za su lalace cikin duhu.

“Ba bisa ga ƙarfi mutum ba ne mutum ke nasara;

10 waɗanda suke gāba da Ubangiji za su hallaka.

Zai yi musu tsawa daga sama,

Ubangiji zai hukunta dukan duniya.

“Zai ba wa sarkinsa ƙarfi,

yă kuma ɗaukaka shafaffensa.”

11 Sa’an nan, Elkana ya koma gida a Rama amma yaron ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli firist.

12 ’Ya’yan Eli firist, mutane ne masu mugunta. Ba su ɗauki Ubangiji a bakin kome ba. 13 Al’ada ce ga firistoci da mutane cewa in wani ya miƙa hadaya, yayinda nama yake kan wuta, bawan firist zai zo da babban cokali mai yatsu, 14 zai soka cokali mai yatsun a tukunyar, ko butar da ake dafan naman. Duk abin da cokali mai yatsun ya cako daga tukunyar, ya zama na firist. Haka aka yi ta yi wa Isra’ilawan da suka zo miƙa hadaya a Shilo. 15 Tun ma kafin a ƙona kitse, bawan firist yakan zo yă ce wa mutumin da yake miƙa hadaya, “Ka ba wa firist nama domin yă gasa, ba zai karɓi dafaffen nama daga wurinka ba, sai ɗanye.”

16 In kuwa mutumin ya ce masa, “Bari kitse yă ƙone tukuna, sa’an nan ka ɗiba duk abin da kake so.” Sai bawan yă ce masa, “A’a, ka ba ni yanzu, in ka ƙi kuwa zan ɗiba ƙarfi da yaji.”

17 Wannan zunubin samarin ya yi muni ƙwarai a gaban Ubangiji, domin sun wulaƙanta hadayar Ubangiji, ƙwarai da gaske.

18 Amma yaron nan Sama’ila, yana hidima a gaban Ubangiji yana sanye da efod na lilin. 19 Kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka ’yar taguwa ta kai masa sa’ad da ita da mijinta suka je miƙa hadaya ta shekara. 20 Eli yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, yă ce, Ubangiji yă ba ka waɗansu ’ya’ya ta wurin matan nan, maimakon wanda ta roƙa daga Ubangiji, ta kuma ba da shi ga Ubangiji. Bayan haka sai su koma gida. 21 Hannatu kuwa ta sami alfarma daga Ubangiji. Ta yi ciki. Ana cikin haka Sama’ila kuwa sai girma yake ta yi a gaban Ubangiji.