Zamani na 3: Daga Haihuwar Musa zuwa Mutuwarsa

Sashe na 1: Haihuwar Musa da Farkon Rayuwarsa

1571 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Fitowa 2

1 Ana nan, sai wani Balawe ya auri wata Balawiya, 2 ta kuwa yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har watanni uku. 3 Amma da ba tă iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin. 4 ’Yar’uwarsa ta tsaya da ɗan rata tana lura da abin da zai faru da shi.

5 Sai ’yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin tă yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta tă ɗauko mata. 6 Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne.”

7 Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?”

8 Sai ta amsa ta ce, “I, tafi.” Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron. 9 Diyar Fir’auna ta ce mata, “Ɗauki jaririn, ki yi mini renonsa, zan kuwa biya ki.” Saboda haka ta ɗauki yaron, ta yi renonsa. 10 Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.”

11 Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa. 12 Da ya leƙa nan da can bai kuwa ga kowa ba, sai ya kashe mutumin Masar, ya ɓoye shi a yashi. 13 Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?”

14 Mutumin ya ce masa, “Wa ya mai da kai mai mulki da mai hukunci a kanmu? Kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan?” Sai Musa ya tsorata, ya yi tunani ya ce, “To, fa, abin nan da na yi, ya zama sananne.”

15 Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya. 16 To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu. 17 Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.

18 Da ’yan matan suka komo wurin Reyuwel mahaifinsu, sai ya tambaye su ya ce, “Yaya kuka dawo da wuri yau?”

19 Suka amsa suka ce, “Wani mutumin Masar ne ya taimake mu daga hannun waɗansu makiyaya. Har ma ya ɗebo ruwa ya shayar da dabbobin.”

20 Ya tambayi ’yan matansa, “To ina yake? Don me kuka bar shi a can? A gayyace shi, yă zo, yă ci wani abu.”

21 Musa ya yarda yă zauna da mutumin wanda ya ba da ’yarsa Ziffora aure da Musa. 22 Ziffora ta haifi wa Musa ɗa, ya kuma raɗa masa suna Gershom cewa, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa.”

23 Ana nan dai, a kwana a tashi, sai sarkin Masar ya mutu. Isra’ilawa suka yi kuka mai zafi saboda bautarsu mai wuya, sai kukar neman taimakonsu saboda bauta, ya kai wurin Allah. 24 Allah kuwa ya ji kukansu sai ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim da Ishaku da Yaƙub. 25 Sai Allah ya dubi Isra’ilawa, ya kuma damu da su.

Zabura 88

Waƙa ce, Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannot maskil na Heman dangin Ezra.

1 Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni,

dare da rana ina kuka a gabanka.

2 Bari addu’ata ta zo a gabanka;

ka kasa kunne ga kukata.

3 Gama raina yana cike da wahala

rayuwata tana gab da kabari.

4 An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami;

ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.

5 An ware ni tare da matattu,

kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari,

waɗanda ba ka ƙara tunawa,

waɗanda aka yanke daga taimakonka.

6 Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa

cikin zurfafa mafi duhu.

7 Hasalarka tana da nauyi a kaina;

ka turmushe ni da dukan raƙumanka. Sela

8 Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni

ka sa na zama abin ƙyama a gare su.

An kange ni, ba yadda zan kuɓuta

9 idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki.

Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana;

na tā da hannuwana zuwa gare ka.

10 Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne?

Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? Sela

11 Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne,

ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?

12 An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne,

ko ayyukan adalcinka a lahira?

13 Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji;

da safe addu’ata kan zo gabanka.

14 Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni

ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?

15 Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu;

na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.

16 Hasalarka ta sha kaina;

razanarka ta hallaka ni.

17 Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa;

sun mamaye ni ɗungum.

18 Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni;

duhu ne abokina na kurkusa.