Akwatin Alkawari Ya Bar Gidan Obed-Edom

Ƙaura da akwatin alkawari a karo na biyu, daga gidan Obed-Edom.

1045 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Tarihi 15:1–14

1 Bayan Dawuda ya yi gine-gine wa kansa a Birnin Dawuda, sai ya shirya wuri domin akwatin alkawarin Allah, ya kuma kafa tenti dominsa. 2 Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.”

3 Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa.

4 Ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya da kuma Lawiyawa.

5 Daga zuriyar Kohat,

Uriyel shugaba da dangi 120;

6 daga zuriyar Merari

Asahiya shugaba da dangi 220;

7 daga zuriyar Gershom,

Yowel shugaba da dangi 130;

8 daga zuriyar Elizafan,

Shemahiya shugaba da dangi 200;

9 daga zuriyar Hebron,

Eliyel shugaba da dangi 80;

10 daga zuriyar Uzziyel,

Amminadab shugaba da dangi 112.

11 Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa. 12 Ya ce musu, “Ku ne kawunan iyalan Lawiyawa; ku da ’yan’uwanku Lawiyawa, sai ku tsarkake kanku ku hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila, zuwa wurin da na shirya dominsa. 13 Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.” 14 Saboda haka firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu don su hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila.

Zaburar da Aka Rubuta Kafin Ƙaura da Akwatin Alkawari a Karo na Biyu

Zaburar da aka rubuta yayin da ake shirye-shiryen ƙaura da akwatin alkawari a karo na biyu.

Zabura 132

Waƙar haurawa.

1 Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda

da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.

2 Ya yi rantsuwa ga Ubangiji

ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,

3 “Ba zan shiga gidana

ko in kwanta a gado ba,

4 ba zan ba wa idanuna barci ba,

ba gyangyaɗi wa idanuna,

5 sai na sami wuri wa Ubangiji,

mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”

6 Mun ji haka a Efrata,

muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar,

7 “Bari mu tafi wurin zamansa;

bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa,

8 ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka,

kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.

9 Bari a suturta firistocinka da adalci;

bari tsarkakanka su rera don farin ciki.”

10 Saboda Dawuda bawanka,

kada ka ƙi shafaffenka.

11 Ubangiji ya rantse wa Dawuda

tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa,

“Ɗaya daga cikin zuriyarka

zan sa a kan kursiyinka,

12 in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari

da farillan da na koya musu,

to ’ya’yansu maza za su zauna

a kan kursiyinka har abada abadin.”

13 Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona,

ya so ta zama mazauninsa,

14 “Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin;

a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,

15 zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa;

matalautanta za su ƙoshi da abinci.

16 Zan suturta firistocinta da ceto,

tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.

17 “A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda

in kuma kafa fitila saboda shafaffena.

18 Zan suturta abokan gābansa da kunya,

amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”

2 Sama’ila 6:12–19

12 To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, “Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah.” Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki. 13 Sa’ad da waɗanda suke ɗaukan akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai yă yi hadayar bijimi da saniya mai ƙiba. 14 Dawuda, sanye da efod lilin, ya yi ta rawa a gaban Ubangiji da dukan ƙarfinsa, 15 yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni.

16 Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal ’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.

17 Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, aka ajiye shi a inda aka shirya masa a cikin tentin da Dawuda ya shirya dominsa. Dawuda kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama a gaban Ubangiji. 18 Bayan ya gama yin hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki. 19 Sa’an nan ya rarraba abinci, da ƙosai, dabino, da waina ga kowane mutum a cikin dukan jama’ar Isra’ila, maza da mata. Dukan mutane kuwa suka watse zuwa gidajensu.

1 Tarihi 15:15–29

15 Sai Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah da sanduna a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.

16 Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa ’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna.

17 Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berekiya daga cikin ’yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kushahiya. 18 Tare da su kuma ’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya, Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel, matsaran ƙofofi.

19 Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla. 20 Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot. 21 Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit. 22 Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.

23 Berekiya da Elkana, ne za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin. 24 Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.

25 Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki. 26 Domin Allah ya taimaki Lawiyawan da suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, aka miƙa hadayar bijimai bakwai da raguna bakwai. 27 To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin. 28 Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.

29 Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal ’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.