Istifanus Ya Tsawata wa Majalisa
Da aka katse Istifanus yana kāre kansa, ya tsawata wa Majalisa cewa su ne masu kashe Almasihunsu.
33 ko 34 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
51 “Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki! 52 An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi 53 ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin mala’iku amma ba ku yi biyayya da ita ba.”
An Jefi Istifanus Har Ya Mutu 34 bayan haihuwar Almasihu
An jefi Istifanus har ya mutu, yana addu'a ga masu kashe shi.
54 Da membobin Sanhedrin suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu. 55 Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah. 56 Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”
57 Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya. 58 Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.
59 Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” 60 Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.
8:1 Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa.
A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage. 2 Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.
Tsanantawa ga Kiristoci Gaba Ɗaya
Tsanantawa ga Kiristoci gaba ɗaya, wadda Shawulu (wanda daga baya aka kira Bulus) ya taka rawar jagoranci a cikinta.
3 Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.
Filibus Ya Yi Wa'azi a Samariya
Filibus dikon, bayan ya bar Urushalima saboda tsanantawa, ya tafi Samariya, inda ya yi wa'azi da mu'ujizai.
5 Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can. 6 Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa. 7 Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa. 8 Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.
9 To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne, 10 dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma” 11 Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa. 12 Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata. 13 Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.
Bitrus da Yohanna Sun Sauko zuwa Samariya
Bitrus da Yohanna sun sauko daga Urushalima zuwa Samariya don su ba sababbin masu bi baiwar Ruhu Mai Tsarki iri-iri.
14 Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna. 15 Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki, 16 domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu. 17 Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.
Bitrus Ya Tsawata wa Siman Mai Sihiri
18 Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi, 19 ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”
20 Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi! 21 Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba. 22 Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka. 23 Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.”
24 Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”