Solomon Ya Shirya Gina Haikali
Shirye-shiryen gina haikali. Mutuwar Shimeyi. Auren Solomon.
1015 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Sai Sarki Solomon ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila.
2 Waɗannan su ne manyan shugabanninsa.
Azariya ɗan Zadok shi ne firist;
3 Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta.
Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu.
4 Benahiya ɗan Yehohiyada, shi ne shugaban mayaƙa.
Zadok da Abiyatar, su ne firistoci.
5 Azariya ɗan Natan, shi ne mai lura da shugabannin yanki.
Zabud ɗan Natan, shi ne firist da kuma mai wa sarki shawara.
6 Ahishar, shi ne sarkin fada.
Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu.
7 Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.
8 Ga sunayensu,
Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim;
9 Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan;
10 Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer);
11 Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon);
12 Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;
13 Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla);
14 Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim;
15 Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon);
16 Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot;
17 Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar;
18 Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin;
19 Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin.
20 Mutanen Yahuda da na Isra’ila sun yi yawa sai ka ce yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka kuma yi farin ciki. 21 Solomon kuwa ya yi mulki a bisa dukan masarautai daga Kogi zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Waɗannan ƙasashe sun yi ta kawo haraji, suka kuma zama bayin Solomon dukan kwanakin ransa.
22 Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci, 23 shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba. 24 Gama ya yi mulki a bisa dukan masarautai yamma da Kogi, daga Tifsa zuwa Gaza, aka kuwa sami zaman lafiya a kowane gefe. 25 A kwanakin da Solomon yake raye, Yahuda da Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba, sun zauna lafiya, kowane mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaurensa.
1 Solomon ya ba da umarni don a gina haikali domin sunan Ubangiji da kuma fada wa kansa. 2 Ya ɗebi mutane dubu saba’in su zama ’yan ɗauko, mutane dubu tamanin su zama masu fasa dutse a tuddai, da kuma mutane dubu uku da ɗari shida su zama masu lura da su.
1 Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa. 2 Solomon ya mayar da wannan saƙo ga Hiram ya ce,
3 “Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. 4 Amma yanzu Ubangiji Allahna ya ba ni hutu a kowane gefe, babu kuma gāba ko masifa. 5 Ina niyya in gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, yadda Ubangiji ya faɗa wa mahaifina Dawuda, sa’ad da ya ce, ‘Ɗanka wanda zai gāje ka, shi zai gina haikali domin Sunana.’
6 “Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.”
7 Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.”
8 Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan,
“Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir. 9 Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.”
10 A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata. 11 Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara. 12 Ubangiji ya ba wa Solomon hikima, kamar yadda ya yi masa alkawari. Dangantakar zaman lafiya ta kasance tsakanin Hiram da Solomon, su biyun suka yi yarjejjeniya.
3 Solomon ya aika wannan saƙo ga Hiram sarkin Taya.
“Ka aika mini gumaguman al’ul kamar yadda ka yi wa mahaifina Dawuda sa’ad da ka aika masa al’ul don yă gina fada yă zauna a ciki. 4 Yanzu ina shirin ginin haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe shi gare shi don ƙona turare mai ƙanshi a gabansa, don kuma ajiyar burodi mai tsarki kullum, da kuma don miƙa hadayun ƙonawa kowace safiya, kowace yamma, da a Asabbatai da Sababbin Wata, da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji Allahnmu. Wannan dawwammamiyar farilla ce don Isra’ila.
5 “Haikalin da zan gina zai zama mai girma, domin Allahnmu ya fi dukan sauran alloli girma. 6 Amma wa zai iya gina haikali dominsa, shi wanda sammai, har ma da sama sammai, ba za su iya riƙe shi ba? To, wane ne ni da zan gina haikali dominsa, in ba dai wurin ƙona hadayu a gabansa ba?
7 “Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanince a aiki da azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanince da aikin sassaƙa, domin yă yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuda da Urushalima, waɗanda mahaifina Dawuda ya tanada.
8 “Ka kuma aika mini al’ul, fir da gumaguman algum daga Lebanon, gama na san cewa mutanenka sun gwanince a yakan katakai a can. Mutanena kuwa za su yi aiki tare da naka 9 don su tanada mini katakai da yawa, domin haikalin da zan gina dole yă zama mai girma da kuma ƙasaitacce. 10 Zan ba wa bayinka masu yankan katakai waɗanda suka yanka katako, garwa niƙaƙƙen alkama dubu ashirin, garwan sha’ir dubu ashirin da randunan ruwan inabi dubu ashirin da kuma randunan man zaitun dubu ashirin.”
11 Hiram sarkin Taya ya amsa ta wurin rubuta wasiƙa zuwa ga Solomon.
“Domin Ubangiji yana ƙaunar mutanensa, ya naɗa ka sarkinsu.”
12 Hiram ya ƙara da cewa,
“Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya yi sama da ƙasa! Ya ba Sarki Dawuda ɗa mai hikima, cike da wayo da kuma sani, wanda zai gina haikali domin Ubangiji da kuma fada wa kansa.
13 “Zan aika maka Huram-Abi, wani gwani wanda ya iya aiki, kuma mai hikima, 14 wanda mahaifiyarsa ta fito daga Dan, mahaifinsa kuma daga Taya. An horar da shi a aikin zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, dutse, itace, da kuma shuɗi, shunayya, garura, da lilin mai kyau. Ya gogu a kowane irin zāne-zāne, zai kuma iya yin kowane zānen da aka ba shi. Zai yi aiki tare da masu sana’arka, da kuma tare da waɗanda ranka yă daɗe, Dawuda mahaifinka ya tanada.
15 “Yanzu fa, bari ranka yă daɗe, yă aiko wa bayinsa alkama da sha’ir da kuma man zaitun da ruwan inabin da ka alkawarta, 16 za mu kuwa yanka dukan gumagumai daga Lebanon da kake bukata za mu kuwa yi fitonsu ta teku, su gangara zuwa Yaffa. Za ka iya kwashe su daga can ka haura zuwa Urushalima.”
13 Sarki Solomon ya ɗebi ma’aikata daga dukan Isra’ila, su dubu talatin. 14 Ya riƙa aika su dubu goma-goma zuwa Lebanon kowane wata, saboda su yi wata ɗaya a Lebanon, watanni biyu kuma a gida. Adoniram ne ya lura da aikin gandun. 15 Solomon ya kasance da ’yan ɗauko guda dubu saba’in da masu yankan duwatsu guda dubu tamanin a cikin tuddai, 16 ya kuma kasance da shugabanni dubu uku da ɗari uku waɗanda suke lura da aikin, su ne kuma suke bi da ma’aikatan. 17 Bisa ga umarnin sarki sai suka cire manyan duwatsu masu kyau don a tanada tushen duwatsun da aka gyara domin haikalin daga wurin haƙar duwatsun. 18 Gwanayen Solomon da na Hiram da kuma mutanen Gebal, su suka yanka, suka kuma shirya katako da dutse don ginin haikali.
17 Solomon ya ƙidaya dukan baƙin da suke cikin Isra’ila, bayan ƙidayan da mahaifinsa Dawuda ya yi; aka kuma tarar sun kai 153,600. 18 Ya sa 70,000 a cikinsu su zama ’yan ɗauko, 80,000 kuma su zama masu fasan dutse a tuddai, sa’an nan 3,600 su zama shugabanni masu lura da aiki.
Mutuwar Shimeyi 1011 kafin haihuwar Almasihu
39 Amma bayan shekaru uku, biyu daga cikin bayin Shimeyi suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma’aka, sarkin Gat. Aka faɗa wa Shimeyi cewa, “Bayinka suna a Gat.” 40 Da jin haka, sai ya tashi ya shimfiɗa wa jakinsa abin zama, ya hau, ya tafi Gat wurin Akish domin neman bayinsa. Shimeyi kuwa ya dawo da su gida daga Gat.
41 Da aka faɗa wa Solomon cewa Shimeyi ya bar Urushalima zuwa Gat, har ya dawo. 42 Sai sarki ya aika a kawo Shimeyi, ya ce masa, “Ban sa ka rantse da sunan Ubangiji, na kuma ja maka kunne cewa, ‘A ranar da ka kuskura ka bar nan ka tafi wani wuri, ka tabbata za ka mutu ba’? A lokacin ka ce mini, ‘Abin da ka faɗa yana da kyau. Zan kuwa kiyaye.’ 43 To, me ya sa ba ka kiyaye rantsuwar da ka yi ga Ubangiji, ka kuma yi biyayya da umarnin da na ba ka ba?”
44 Sarki ya ce wa Shimeyi, “Ka sani a zuciyarka dukan muguntar da ka yi wa mahaifina Dawuda. Yanzu Ubangiji zai sāka maka saboda muguntarka. 45 Amma za a yi wa Sarki Solomon albarka, sarautar Dawuda kuma za tă kasance a tsare a gaban Ubangiji har abada.”
46 Sai sarki ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada, yă fita, yă bugi Shimeyi, yă kashe shi. Ya kuwa kashe shi.
Mulki kuwa ya kahu sosai a hannun Solomon.
Auren Solomon
1 Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima. 2 A lokacin dai mutane suna miƙa hadaya a wurare a bisa tuddai, domin ba a riga an gina haikali saboda Sunan Ubangiji ba.