Masarautar Isra’ila

Shalmaneser Ya Mamaye Masarautar Hosheya

Ci gaban labarin mulkin Hosheya, sarkin Isra’ila. Shalmaneser ya mamaye ƙasashen Hosheya.

wajen 725 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Sarakuna 17:3–4

3 Shalmaneser sarkin Assuriya ya kawo wa Hosheya wanda dā abokin tarayyarsa ne, hari har Hosheya ya biya shi haraji. 4 Amma sarkin Assuriya ya gane cewa Hosheya mai cin amana ne, gama ya aika da wakilai wurin So sarkin Masar, ya kuma daina aika wa sarkin Assuriya haraji yadda ya saba yi kowace shekara. Saboda haka Shalmaneser ya kama shi ya sa a kurkuku.

Hosiya Ya Annabta Zaman Bautar Ƙabilu Goma 725 kafin haihuwar Almasihu

Hosiya ya annabta zaman bautar ƙabilu goma, ya kuma roƙi mutanen su tuba.

Hosiya 7–8

1 a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila,

zunuban Efraim za su tonu

za a kuma bayyana laifofin Samariya.

Suna ruɗu,

ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje,

’yan fashi sukan yi fashi a tituna;

2 amma ba su gane

cewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba.

Zunubansu sun kewaye su;

kullum suna a gabana.

3 “Suna faranta wa sarki zuciya da muguntarsu,

shugabanni kuma da ƙarairayinsu.

4 Dukansu mazinata ne

suna ƙuna kamar matoya

wadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wuta

daga cuɗe kullu har kumburinsa.

5 A ranar bikin sarkinmu

shugabanni sukan bugu da ruwan inabi,

yă yi cuɗanya da masu ba’a.

6 Zukatansu suna kamar matoya;

sukan kusace shi da wayo.

Muguwar aniyarsu takan yi ta ci dukan dare;

da safe sai ta ƙuna kamar harshen wuta.

7 Dukansu suna da zafi kamar matoya;

suna kashe masu mulkinsu.

Dukan sarakunansu sukan fāɗi,

kuma babu waninsu da yake kira gare ni.

8 “Efraim yana cuɗanya da al’ummai;

Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba.

9 Baƙi sun tsotse ƙarfinsa,

amma bai gane ba.

Gashi kansa ya cika da furfura,

amma bai lura ba.

10 Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa,

amma duk da haka

bai dawo ga Ubangiji Allahnsa

ko yă neme shi ba.

11 “Efraim yana kama da kurciya,

marar wayo, marar hankali,

yanzu yana kira ga Masar,

yanzu yana juyewa ga Assuriya.

12 Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu;

zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama.

Sa’ad da na ji suna tafiya tare,

zan kama su.

13 Kaitonsu,

domin sun kauce daga gare ni!

Hallaka za tă aukar musu,

domin sun tayar mini!

Na ƙudura in cece su

amma suna faɗar ƙarya a kaina.

14 Ba sa yin mini kuka da zuciyarsu

amma suna ihu a kan gadajensu.

Sukan taru wurin ɗaya don hatsi da ruwan inabi

amma su juya mini baya.

15 Na horar da su na kuma ƙarfafa su,

amma sun ƙulla mini maƙarƙashiya.

16 Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka;

suna kama da tanƙwararren baka.

Za a kashe shugabanninsu da takobi

saboda banzan maganganunsu.

Saboda wannan za a wulaƙanta su

a ƙasar Masar.

8:1 “Ka sa kakaki a leɓunanka!

Gaggafa tana a bisan gidan Ubangiji

domin mutane sun tā da alkawarina

suka kuma tayar wa dokata.

2 Isra’ila ta yi mini kuka,

‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’

3 Amma Isra’ila sun ƙi abin da yake mai kyau;

abokin gāba zai fafare su.

4 Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba;

sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba.

Da azurfa da zinariya

sun ƙera gumaka wa kansu

wanda zai kai zuwa ga hallakarsu.

5 Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya!

Fushina yana ƙuna a kansu.

Sai yaushe za su rabu da gumaka?

6 Su daga Isra’ila ne!

Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi;

gunki ne ba Allah ba.

Za a farfashe shi kucu-kucu,

waccan maraƙin Samariya.

7 “Gama sun shuka iska

don haka za su girbe guguwa.

Hatsin da yake tsaye ba shi da kai,

ba zai yi tsaba ba.

Ko da ya yi tsaba ma,

baƙi ne za su ci.

8 An haɗiye Isra’ila;

yanzu tana cikin al’ummai

kamar abin da ba shi da amfani.

9 Gama sun haura zuwa Assuriya

kamar jakin jejin da yake yawo shi kaɗai.

Efraim ya sayar da kansa ga maza.

10 Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai,

yanzu zan tattara su wuri ɗaya.

Za su fara lalacewa

a ƙarƙashi danniyar babban sarki.

11 “Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi,

waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.

12 Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata,

amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne.

13 Suna miƙa hadayun da aka ba ni

su kuma ci nama,

amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu.

Yanzu zai tuna da muguntarsu

yă kuma hukunta zunubansu.

Za su koma Masar.

14 Isra’ila ya manta da Mahaliccinsa

ya kuma gina fadodi;

Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa.

Amma zan aiko da wuta a bisa biranensu

da zai cinye kagaransu.”