Mamayar Farko ta Sennakerib

713 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Tarihi 32:1–8

1 Bayan dukan abin da Hezekiya ya yi cikin aminci, sai Sennakerib sarkin Assuriya ya zo ya yaƙi Yahuda. Ya yi kwanto wa biranen katanga, yana zato zai ci su da yaƙi wa kansa. 2 Sa’ad da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo yana kuma niyya yă yaƙi Urushalima, 3 sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi. 4 Sai babban taro suka haɗu suka datse dukan maɓulɓulai da rafuffukan da suke gudu cikin ƙasar. Suka ce “Me zai sa sarakunan Assuriya su zo su sami ruwa barkatai?” 5 Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.

6 Ya naɗa manyan hafsoshi a kan mutane, ya tattara su a gabansa a fili a ƙofar birni, ya kuma ƙarfafa su da waɗannan kalmomi. 7 “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Assuriya, da mayaƙan nan masu yawa da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su. 8 Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.

Hezekiya Ya Miƙa Wuya, An Kuma Ci Ashdod da Yaƙi

2 Sarakuna 18:13–16

13 A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su. 14 Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda. 15 Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki.

16 A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.

Ishaya 20

1 A shekarar da babban shugaban yaƙin da Sargon sarkin Assuriya ya aika, ya zo Ashdod ya kuma fāɗa mata ya kuma ci ta da yaƙi, 2 a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.

3 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush, 4 haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar. 5 Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya. 6 A wannan rana mutanen da suke zama a bakin teku za su ce, ‘Dubi abin da ya faru da waɗanda muka dogara a kai, waɗanda muka gudu muka je don neman taimako da ceto daga sarkin Assuriya! Yaya za mu tsira?’ ”

Kira na Annabci ga Urushalima

Kira na annabci ga Urushalima yayin da sojojin Sennakerib suke a ƙasar.

Ishaya 29

1 Kaitonki, Ariyel, Ariyel

birnin da Dawuda ya zauna!

Ƙara shekara ga shekara

a kuma bar shagulgulanki su yi ta kewayewa.

2 Duk da haka zan yi wa Ariyel kwanto

za tă kuma yi kuka da makoki,

za tă zama mini kamar bagaden jini.

3 Zan kafa sansani kewaye da ke duka;

zan kewaye ki da hasumiyoyi

in tasar miki da ayyukan kwantona na yaƙi.

4 Za a ƙasƙantar da ke, za ki ƙi yin magana daga ƙasa;

maganarki za tă yi ƙasa-ƙasa daga ƙura.

Muryarki za tă zama kamar fatalwa daga ƙasa;

daga ƙura maganarki zai fito ƙasa-ƙasa.

5 Amma abokan gābanki masu yawa za su zama kamar ƙura mai laushi,

sojojinsu masu firgitarwa za su yi ta tashi kamar yayin da iska ta hura.

Farat ɗaya, cikin ɗan lokaci,

6 Ubangiji Maɗaukaki zai zo

da tsawa da rawar ƙasa da ƙara mai girma,

da hadarin iska da guguwa da harshe na wuta mai ci.

7 Sa’an nan sojojin dukan al’umman da suka yi yaƙi da Ariyel,

da suka fāɗa mata da kagararta suka kuma yi mata kwanto,

za su zama kamar yadda yake da mafarki,

wahayi da dare,

8 kamar sa’ad da mai yunwa yana mafarki cewa yana cin abinci,

amma sai ya farka, yunwan tana nan;

kamar sa’ad da mai ƙishirwa yana mafarki cewa yana shan ruwa,

amma sai ya farka yana suma, da ƙishinsa.

Haka zai zama da sojoji na dukan al’ummai

da suka yi yaƙi da Dutsen Sihiyona.

9 Ku firgita ku kuma yi mamaki,

ku makance kanku ku kuma zama a makance;

ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba,

ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba.

10 Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi,

Ya rufe idanunku (annabawa);

ya rufe kawunanku (masu duba).

11 Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.” 12 Ko kuwa in kun ba da littafin ga wani wanda ba zai iya karantawa ba, kuka kuma ce, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ban iya karatu ba.”

13 Ubangiji ya ce,

“Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu

suka kuma girmama ni da leɓunansu,

amma zukatansu suna nesa daga gare ni.

Sujadar da suke mini

cike take da dokokin da mutane suka koyar.

14 Saboda haka zan firgita waɗannan mutane sau ɗaya

da abubuwan banmamaki a kan abubuwan banmamaki;

hikimar masu hikima za tă lalace,

azancin masu azanci zai ɓace.”

15 Kaiton waɗanda suke zuwa manyan zurfafa

don su ɓoye shirye-shiryensu daga Ubangiji,

waɗanda suke aikinsu cikin duhu su yi tunani,

“Wa yake ganinmu? Wa zai sani?”

16 Kuna birkitar abubuwa,

sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu!

Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi,

“Ba shi ne ya yi ni ba”?

Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane,

“Ba ka san kome ba”?

17 Cikin ɗan lokaci, za a mai da Lebanon gona mai taƙi

kuma gona mai taƙi za tă zama kamar kurmi?

18 A wannan rana kurame za su ji maganganun littafi,

daga duruduru da duhu kuma

idanun makafi za su gani.

19 Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji;

mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

20 Masu zalunci za su ƙare,

masu ba’a za su ɓace,

kuma dukan waɗanda suke da ido don mugunta za su hallaka,

21 waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi,

waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a

da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci.

22 Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub,

“Ba za a ƙara kunyata Yaƙub ba;

fuskokinsu kuma ba za su ƙara yanƙwanewa ba.

23 Sa’ad da suka ga ’ya’yansu a tsakiyarsu,

aikin hannuwansu,

za su kiyaye sunana da tsarki;

za su san tsarkin Mai Tsarkin nan na Yaƙub,

za su kuma ji tsoron Allah na Isra’ila.

24 Su da suke marasa azanci a ruhu za su sami fahimtar;

waɗanda suke gunaguni za su yarda da koyarwa.”