Zaburan Wahala, Galibi Daga Zaman Bauta

Zaburan da aka rubuta a lokacin wahaloli da ƙuncin ikilisiya, galibi a lokacin zaman bauta a Babilon.

539 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 137

1 A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka

sa’ad da muka tuna da Sihiyona.

2 A can a kan rassan itatuwa

muka rataye garayunmu,

3 gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi,

masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki;

suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”

4 Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji

a baƙuwar ƙasa?

5 In na manta da ke, ya Urushalima,

bari hannuna na dama manta da iyawarsa.

6 Bari harshena yă manne wa rufin bakina

in ban tuna da ke ba,

in ban so Urushalima

farin cikin mafi girma ba.

7 Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi

a ranar da Urushalima ta fāɗi.

Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta,

A ragargaza ta har tushenta!”

8 Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka,

mai farin ciki ne wanda ya sāka miki

saboda abin da kika yi mana,

9 shi da ya ƙwace jariranki

ya fyaɗa su a kan duwatsu.

Zabura 130

Waƙar haurawa.

1 Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

2 Ya Ubangiji, ka ji muryata.

Bari kunnuwanka su saurara

ga kukata ta neman jinƙai.

3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,

Ya Ubangiji, wa zai tsaya?

4 Amma tare da kai akwai gafartawa,

saboda haka ake tsoronka.

5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira,

kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

6 Raina na jiran Ubangiji

fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,

fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.

7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,

gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa

kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.

8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila

daga dukan zunubansu.

Zabura 80

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Lilin Alkawari.” Na Asaf. Zabura ce.

1 Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila,

kai da ka bishe Yusuf kamar garke.

Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi,

ka haskaka 2 a gaban Efraim, Benyamin da Manasse.

Ka tā da ƙarfinka;

ka zo ka cece mu.

3 Ka mai da mu, ya Allah;

ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu,

za mu kuwa cetu.

4 Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,

har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna

a kan addu’o’in mutanenka?

5 Ka ciyar da su da burodin hawaye;

ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.

6 Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu,

kuma abokan gābanmu suna mana ba’a.

7 Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki;

ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu

za mu kuwa cetu.

8 Ka fitar da inabi daga Masar;

ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.

9 Ka gyara wuri saboda shi,

ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.

10 Aka rufe duwatsu da inuwarsa,

manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.

11 Ya miƙe rassansa zuwa Teku

tohonsa har zuwa Kogi.

12 Me ya sa ka rurrushe bangayensa

don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?

13 Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi

halittun gonaki kuma suna cinsa.

14 Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki!

Ka duba daga sama ka gani!

Ka lura da wannan inabi,

15 saiwar da hannun damarka ya dasa,

ɗan da ka renar wa kanka.

16 An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta;

a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.

17 Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka,

ɗan mutum da ka renar wa kanka.

18 Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba;

ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.

19 Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki;

ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu,

za mu kuwa cetu.

Zabura 77

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Na Asaf. Zabura ce.

1 Na yi kuka ga Allah don taimako;

na yi kuka ga Allah don yă ji ni.

2 Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji;

da dare na miƙa hannuwa ba gajiya

raina kuma ya ƙi yă ta’azantu.

3 Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi;

na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. Sela

4 ka hana idanuna rufewa;

na damu ƙwarai har ba na iya magana.

5 Na yi tunani kwanakin da suka wuce,

shekarun da suka wuce da daɗewa;

6 na tuna da waƙoƙina da dare.

Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani.

7 “Ubangiji zai ƙi ne har abada?

Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?

8 Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada?

Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?

9 Allah ya manta yă yi jinƙai?

Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sela

10 Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan,

shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.”

11 Zan tuna da ayyukan Ubangiji;

I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā.

12 Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka

in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.

13 Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne.

Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu?

14 Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai;

ka nuna ikonka a cikin mutane.

15 Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka,

zuriyar Yaƙub da Yusuf. Sela

16 Ruwaye sun gan ka, ya Allah,

ruwaye sun gan ka suka firgita;

zurfafan gaske sun girgiza.

17 Gizagizai sun sauko da ruwa,

sararin sama suka buga tsawa;

kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya.

18 Aka ji tsawanka a cikin guguwa,

walƙiyarka ta haskaka duniya;

duniya ta yi rawar jiki ta girgiza.

19 Hanyarka ta bi ta cikin teku,

hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye,

duk da haka ba a ga sawunka ba.

20 Ka bi da mutanenka kamar garke

ta hannun Musa da Haruna.