Zaburan Wahala, Galibi Daga Zaman Bauta (continued)

Zaburan da aka rubuta a lokacin wahaloli da ƙuncin ikilisiya, galibi a lokacin zaman bauta a Babilon.

539 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 92–93

Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.

1 Yana da kyau a yabi Ubangiji

a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,

2 don a yi shelar ƙaunarka da safe

amincinka kuma da dare,

3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma

da kuma ƙarar garaya.

4 Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji;

na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.

5 Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji,

tunaninka da zurfi suke ƙwarai!

6 Mutum marar azanci ba zai sani ba,

wawa ba zai gane ba,

7 cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa

kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka,

za a hallaka su har abada.

8 Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.

9 Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji,

tabbatacce abokan gābanka za su hallaka;

za a watsar da dukan masu aikata mugunta.

10 Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna;

an zubo mai masu kyau a kaina.

11 Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana;

kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.

12 Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino,

za su yi girma kama al’ul na Lebanon;

13 da aka daddasa a gidan Ubangiji,

za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.

14 Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu,

za su kasance ɗanye kuma kore shar,

15 suna shela cewa, “Ubangiji adali ne;

shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”

93:1 Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka;

Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi.

An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.

2 An kafa kursiyin tun da daɗewa;

kana nan tun fil azal.

3 Tekuna sun taso, ya Ubangiji,

tekuna sun ta da muryarsu;

tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.

4 Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye,

mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku,

Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.

5 Ƙa’idodinka suna nan daram;

tsarki ya yi wa gidanka ado

har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.

Zabura 123

Waƙar haurawa.

1 Na tā da idanuna gare ka,

gare ka da kursiyinka yake cikin sama.

2 Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu,

kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta,

haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu,

sai ya nuna mana jinƙansa.

3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,

gama mun jimre da reni mai yawa.

4 Mun jimre da wulaƙanci

daga masu girman kai,

reni mai yawa daga masu fariya.