Zaburan Wahala, Galibi Daga Zaman Bauta (continued)

Zaburan da aka rubuta a lokacin wahaloli da ƙuncin ikilisiya, galibi a lokacin zaman bauta a Babilon.

539 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 26–27

Ta Dawuda.

1 Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji,

gama na yi rayuwa marar zargi;

Na dogara ga Ubangiji

ba tare da kaucewa ba.

2 Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni,

ka bincike zuciyata da tunanina;

3 gama ƙaunarka kullum tana a gabana,

kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.

4 Ba na zama tare da masu ruɗu,

ko in yi tarayya da masu riya;

5 na ƙi jinin taron masu aikata mugunta

na ƙi in zauna tare da mugaye.

6 Na wanke hannuwana cikin rashin laifi,

ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,

7 ina shelar yabonka da ƙarfi

ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.

8 Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji,

wurin da ɗaukakarka ke zaune.

9 Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi

raina tare da masu son yin kisankai

10 waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu,

waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.

11 Amma na yi rayuwa marar zargi;

ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.

12 Ƙafafuna suna tsaye daram;

cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.

Ta Dawuda.

27:1 Ubangiji ne haskena da cetona,

wa zan ji tsoro?

Ubangiji ne mafakar raina,

wane ne zan ji tsoro?

2 Sa’ad da mugaye suka tasar mini

don su cinye ni,

sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari,

sun yi tuntuɓe suka fāɗi.

3 Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni,

zuciyata ba za tă ji tsoro ba;

ko da yake ya ɓarke a kaina,

duk da haka zan ƙarfafa.

4 Abu guda na roƙi Ubangiji,

wannan shi ne na nema,

cewa in zauna a gidan Ubangiji

dukan kwanakin raina,

in dubi kyan Ubangiji

in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

5 Gama a lokacin wahala,

zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa;

zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa

ya kuma sa ni can a bisa dutse.

6 Sa’an nan kaina zai ɗaukaka

a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni;

a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki;

zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.

7 Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji;

ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini.

8 Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!”

Fuskarka, Ubangiji, zan nema.

9 Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni,

kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi;

kai ne ka kasance mai taimakona.

Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni,

Ya Allah Mai cetona.

10 Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni,

Ubangiji zai karɓe ni.

11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji;

ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya

saboda masu danne ni.

12 Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina,

gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina,

suna numfasa tashin hankali.

13 Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa

zan ga alherin Ubangiji;

a ƙasar masu rai.

14 Ka dogara ga Ubangiji,

ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya

ka kuma dogara ga Ubangiji.

Zabura 36

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji.

1 Akwai magana a cikin zuciyata

game da zunubin mugu.

Babu tsoron Allah

a idanunsa.

2 Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne

wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.

3 Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu;

ya daina zama mai hikima da yin alheri.

4 Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta;

yakan sa kansa ga aikata zunubi

kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.

5 Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai,

amincinka har sararin sammai.

6 Adalcinka yana kama da manyan duwatsu,

hukuncinka kamar zurfi mai girma.

Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.

7 Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa!

Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.

8 Suna biki a yalwar gidanka;

kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.

9 Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai

cikin haskenka mukan ga haske.

10 Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka,

adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.

11 Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini,

ko hannun mugu ya kore ni.

12 Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi,

a zube, ba za su kuwa iya tashi ba!