Zaburan Dawuda, Ba a San Kwanakinsu Ba

Zaburan da Dawuda ya rubuta, waɗanda ba a san ranakun rubuta su da yanayin da aka rubuta su ba.

1015 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 40–41

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.

1 Na jira da haƙuri ga Ubangiji;

ya juya wurina ya kuma ji kukata.

2 Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi,

daga laka da taɓo;

ya sa ƙafafuna a kan dutse

ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.

3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina,

waƙar yabo ga Allahna.

Da yawa za su gani su tsorata

su kuma dogara ga Ubangiji.

4 Mai albarka ne mutumin

da ya mai da Ubangiji abin dogararsa,

wanda ba ya kula da masu girman kai,

waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.

5 Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna,

abubuwan banmamakin da ka aikata.

Abubuwan da ka shirya mana.

Ba wanda zai iya faɗa maka su;

a ce zan yi magana in faɗe su,

za su wuce gaban misali a furta.

6 Hadaya da sadaka ba ka sha’awa,

amma kunnuwana ka huda;

hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.

7 Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo,

kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi.

8 Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna;

dokar tana cikin zuciyata.”

9 Na yi shelar adalcinka cikin babban taro;

ba na rufe leɓunana,

kamar yadda ka sani, ya Ubangiji.

10 Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata;

ina maganar amincinka da cetonka.

Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka

a gaban taron jama’arka mai girma ba.

11 Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;

bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.

12 Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni;

zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani.

Sun fi gashin kaina yawa,

har ma na fid da zuciya.

13 Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji;

Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.

14 Bari masu neman raina

su sha kunya su kuma rikice;

bari dukan waɗanda suke neman lalacewata

su koma baya da kunya.

15 Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!”

Su sha mamaki saboda kunyar da za su sha.

16 Amma bari dukan masu nemanka

su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka;

bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce,

“Ubangiji mai girma ne!”

17 Ni dai matalauci ne da mai bukata;

bari Ubangiji yă tuna da ni.

Kai ne taimakona da mai cetona;

Ya Allahna, kada ka jinkirta.

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

41:1 Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi;

Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.

2 Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa;

zai albarkace shi a cikin ƙasar

ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.

3 Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa

ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.

4 Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai;

ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”

5 Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa,

“Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”

6 Duk sa’ad da wani ya zo ganina,

yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi;

sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.

7 Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina;

suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,

8 “Mugun ciwo ya kama shi;

ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”

9 Har abokina na kurkusa,

wanda na amince da shi,

wanda muke cin abinci tare,

ya juya yana gāba da ni.

10 Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,

ka tā da ni, don in sāka musu.

11 Na sani kana jin daɗina,

gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.

12 Cikin mutuncina ka riƙe ni

ka sa ni a gabanka har abada.

13 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,

har abada abadin.

Amin kuma Amin.

Zabura 61

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.

1 Ka ji kukata, ya Allah;

ka saurari addu’ata.

2 Daga iyakar duniya na yi kira gare ka,

na yi kira yayinda zuciyata ta karai;

ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.

3 Gama kai ne mafakata,

hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.

4 Ina marmari in zauna a tentinka har abada

in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela

5 Gama ka ji alkawarina, ya Allah;

ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.

6 Ka ƙara kwanakin ran sarki,

shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.

7 Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada;

ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.

8 Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka

in kuma cika alkawarina kowace rana.