Koyarwar Uba game da Hikima (continued)

984 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Karin Magana 6–7

1 Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi,

in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,

2 in maganarka ta taɓa kama ka,

ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,

3 to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka;

da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka,

ka tafi ka ƙasƙantar da kanka;

ka roƙi maƙwabcinka!

4 Ka hana kanka barci,

ko gyangyaɗi a idanunka ma.

5 Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta,

kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.

6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;

ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

7 Ba shi da jagora

ba shugaba ko mai mulki,

8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani

ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?

Yaushe za ku farka daga barcinku?

10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

ɗan naɗin hannuwa don a huta,

11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari

rashi kuma kamar ɗan fashi.

12 Sakare da mutumin banza

wanda yana yawo da magana banza a baki,

13 wanda yake ƙyifce da ido,

yana yi alama da ƙafafunsa

yana kuma nuni da yatsotsinsa,

14 wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa,

kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye

15 Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya;

za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.

16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,

abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

17 duban reni,

harshe mai ƙarya,

hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,

ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,

da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

21 Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;

ka ɗaura su kewaye da wuyanka.

22 Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;

sa’ad da kake barci, za su lura da kai;

sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.

23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,

wannan koyarwa haske ne,

kuma gyare-gyaren horo

hanyar rayuwa ce,

24 suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a

daga sulɓin harshen mace marar aminci.

25 Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka

kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.

26 Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta,

mazinaciya kuma takan farauci ranka.

27 Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa

ba tare da rigunansa sun ƙone ba?

28 Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi

ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?

29 Haka yake da wanda ya kwana da matar wani;

babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.

30 Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata

don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa.

31 Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai

ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.

32 Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;

duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.

33 Dūka da kunya ne za su zama rabonsa,

kuma kunyarsa za tă dawwama.

34 Gama kishi kan tā da hasalar miji,

kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.

35 Ba zai karɓi duk wata biya ba;

zai ƙi cin hanci, kome yawansu.

7:1 Ɗana, ka kiyaye kalmomina

ka kuma ajiye umarnaina a cikinka.

2 Ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu;

ka tsare koyarwata kamar ƙwayar idonka.

3 Ka daure su a yatsotsinka;

ka rubuta su a allon zuciyarka.

4 Ka faɗa wa hikima, “Ke ’yar’uwata ce,”

ka kuma kira fahimi danginka;

5 za su kiyaye ka daga mazinaciya,

daga mace marar aminci da kalmominta masu ɗaukan hankali.

6 A tagar gidana

na leƙa ta labule mai rammuka.

7 Sai na gani a cikin marasa azanci,

na lura a cikin samari,

wani matashi wanda ba shi da hankali.

8 Yana gangarawa a titi kusa da kusurwarta,

yana tafiya a gefen wajen gidanta

9 da magariba, yayinda rana tana fāɗuwa,

yayinda duhun dare yana farawa.

10 Sai ga mace ta fito don ta sadu da shi,

saye da riga kamar karuwa shirye kuma don ta yaudare shi.

11 (Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya,

ƙafafunta ba sa zama a gida;

12 wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali,

tana yawo a kowace kusurwa.)

13 Sai ta kama shi ta rungume shi

da duban soyayya a fuskarta ta ce,

14 “Ina da hadaya ta salama a gida;

yau zan cika alkawarina.

15 Saboda haka na fito don in sadu da kai;

na neme ka na kuma same ka!

16 Na lulluɓe gadona

da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.

17 Na yayyafa turare a gadona

da mur, aloyes da kuma kirfa.

18 Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe;

bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!

19 Mijina ba ya gida;

ya yi tafiya mai nisa.

20 Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi

ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”

21 Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce;

ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.

22 Nan take, ya bi ta

kamar saniyar da za a kai mayanka,

kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo

23 sai da kibiya ta soki hantarsa,

kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko,

ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.

24 Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;

ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.

25 Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta

ko ku kauce zuwa hanyoyinta.

26 Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci;

kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.

27 Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari

mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.