Karin Maganar Solomon (continued)

984 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Karin Magana 17–18

1 Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru

da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.

2 Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya,

kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa.

3 Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta,

amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.

4 Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna;

maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.

5 Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne;

duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.

6 Jikoki rawanin tsofaffi ne,

kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.

7 Leɓunan basira ba su dace da wawa ba,

ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!

8 Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi;

ko’ina ya juye, yakan yi nasara.

9 Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne,

amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.

10 Tsawata kan sa mutum ya koyi basira

fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.

11 Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah;

za a aika manzo mutuwa a kansu.

12 Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya

fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.

13 In mutum ya sāka alheri da mugunta,

mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.

14 Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne,

saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.

15 Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci,

Ubangiji ya ƙi su biyu.

16 Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa,

da yake ba shi da sha’awar samun hikima?

17 Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe,

ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.

18 Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani

ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.

19 Duk mai son faɗa yana son zunubi,

duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.

20 Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba;

duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala.

21 Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki

babu farin ciki ga mahaifin wawa.

22 Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,

amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.

23 Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce

don yă lalace yin adalci.

24 Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima,

amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.

25 Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa

da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.

26 Ba shi da kyau a hukunta marar laifi,

ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu.

27 Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi,

mutum mai basira kuma natsattse ne.

28 Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,

da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.

18:1 Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai;

yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai.

2 Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta

amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.

3 Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo,

haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo.

4 Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye,

amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu.

5 Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri

ko ka hana wa marar laifi adalci.

6 Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa,

bakinsa kuma kan gayyaci dūka.

7 Bakin wawa lalatar da kansa yake yi

leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.

8 Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke;

sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.

9 Wanda yake ragwanci a aikinsa

ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.

10 Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;

masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.

11 Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga;

suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.

12 Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,

amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.

13 Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara,

wannan wauta ce da kuma abin kunya.

14 Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo,

amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.

15 Zuciya mai la’akari kan nemi sani;

kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.

16 Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa

yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.

17 Wanda ya fara mai da jawabi yakan zama kamar shi ne mai gaskiya,

sai wani ya fito ya yi masa tambaya tukuna.

18 Jefa ƙuri’a kan daidaita tsakanin masu faɗa

ta kuma ajiye masu faɗan a rabe.

19 Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa,

kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.

20 Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika;

girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.

21 Harshe yana da ikon rai da mutuwa,

kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.

22 Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau

ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

23 Matalauci kan yi roƙo da taushi,

amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.

24 Mutum mai abokai masu yawa kan lalace,

amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.