Annabce-annabce a Kan Zedekiya da Annabawan Ƙarya (continued)

Annabce-annabce dabam-dabam na hukunci a kan Zedekiya, annabawan ƙarya, Urushalima, da al’ummomin Yahudawa.

594 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ezekiyel 18–19

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Me ku mutane kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa,

“ ‘Ubanni sun ci ’ya’yan inabi masu tsami,

haƙoran ’ya’ya kuwa sun mutu’?

3 “Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba za ku ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba. 4 Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.

5 “A ce akwai mai adalci

wanda yake aikata abin da yake daidai da kuma gaskiya;

6 ba ya cin abinci a duwatsun tsafi

ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila.

Ba ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa

ko ya kwana da mace lokacin al’adarta ba.

7 Ba ya cin zalin wani,

amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa.

Ba ya yi fashi

amma yakan ba wa mayunwata abinci

ya kuma tanada wa marasa tufafi riga.

8 Ba ya ba da bashi da ruwa

ko ya karɓa ƙarin riba.

Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta

yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum.

9 Yana bin ƙa’idodina

yana kuma kiyaye dokokina da aminci.

Wannan mutumin adali ne;

tabbatacce zai rayu,

in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

10 “A ce yana da ɗa wanda yana kisa ko yana yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa 11 (ko da yake mahaifin bai yi ko ɗaya daga cikinsu ba).

“Yakan ci abinci a duwatsun tsafi.

Yakan ƙazantar da matar maƙwabci.

12 Yakan ci zalin matalauta da mabukata.

Yakan yi fashi.

Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa.

Ya dogara ga gumaka.

Yana aikata ayyukan banƙyama.

13 Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa.

Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.

14 “Amma a ce wannan ɗa yana da ɗa wanda ya ga dukan zunuban da mahaifinsa yake aikata, kuma ko da yake ya gan su, bai yi ko ɗaya daga cikin irin abubuwan nan ba, wato,

15 “Bai ci abinci a duwatsun tsafi ba

ko ya dogara ga gumakan gidan Isra’ila.

Bai ƙazantar da matar maƙwabcinsa ba.

16 Bai ci zalin wani

ko ya karɓi jingina ba.

Ba ya fashi

amma yakan ba da abincinsa ga mayunwata

ya tanada tufafi wa marasa tufafi.

17 Yakan janye hannunsa daga zunubi

ba ya kuma ba da bashi da ruwa ko karɓan riba da yawa.

Yakan kiyaye dokokina ya kuma bi ƙa’idodina.

Ba zai mutu saboda zunubin mahaifinsa ba; tabbatacce zai rayu. 18 Amma mahaifinsa zai mutu saboda zunubinsa, domin ya yi ƙwace, ya yi wa ɗan’uwansa fashi ya kuma yi abin da ba daidai ba a cikin mutanensa.

19 “Duk da haka kukan yi tambaya, ‘Me ya sa ɗan ba zai sami rabo a laifin mahaifinsa ba?’ Da yake ɗan ya yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina, tabbatacce zai rayu. 20 Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.

21 “Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. 22 Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu. 23 Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?

24 “Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.

25 “Duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ka ji, ya gidan Isra’ila. Hanyata ba daidai ba ce? 26 In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu. 27 Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa. 28 Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. 29 Duk da haka mutanen Isra’ila sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Hanyoyina ba daidai ba ne, ya gidan Isra’ila? Ba hanyoyinku ne ba daidai ba?

30 “Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba. 31 Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila? 32 Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!

19:1 “Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila 2 ka ce,

“ ‘Mahaifiyarki zakanya ce

cikin zakoki!

Takan kwanta cikin ’yan zakoki

ta kuma yi renon kwiyakwiyanta.

3 Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,

ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi.

Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta

yakan kuma cinye mutane.

4 Al’ummai suka ji labarinsa,

aka kuma kama shi cikin raminsu.

Suka ja shi da ƙugiyoyi

zuwa ƙasar Masar.

5 “ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba,

abin da take fata gani ya tafi,

sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta

ta mai da shi zaki mai ƙarfi.

6 Ya yi ta yawo a cikin zakoki,

gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi.

Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta

yakan kuma cinye mutane.

7 Ya rurrushe kagaransu

ya kuma ragargaza biranensu.

Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta

sun tsorata da jin rurinsa.

8 Sai al’ummai suka tayar masa,

waɗannan daga yankunan da suke kewaye.

Suka yafa raga dominsa

ya kuwa fāɗa cikin raminsu.

9 Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji

suka kawo shi wurin sarkin Babilon.

Suka sa shi cikin kurkuku,

saboda haka ba a ƙara jin rurinsa

a kan duwatsun Isra’ila ba.

10 “ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi

da aka shuka kusa da ruwa;

ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassa

saboda yalwan ruwa.

11 Rassanta suka yi ƙarfi,

suka dace da sandar mai mulki.

Ta yi tsayi

zuwa sama

ana ganin ta saboda tsayinta

da kuma saboda yawan rassanta.

12 Amma aka tumɓuke ta cikin fushi

aka jefar da ita a ƙasa.

Iskar gabas ta sa ta yanƙwane,

aka kakkaɓe ’ya’yanta;

rassanta masu ƙarfi suka bushe

wuta kuma ta cinye su.

13 Yanzu an shuka ta a hamada,

a busasshiyar ƙasa marar ruwa.

14 Wuta ta fito daga jikin rassanta

ta cinye ’ya’yanta.

Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta

da ya dace da sandar mai mulki.’

Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”