Bulus Ya Rubuta Wa Tessalonikawa

Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta farko zuwa ga Tessalonikawa domin ya ƙarfafa su cikin bangaskiya, sa’ad da suke fuskantar hare-haren Yahudawa marasa bangaskiya, ta wurin nanata musu hujjojin gaskiyar Kiristanci.

51 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bulus Ya Gaishe da Tessalonikawa

Gabatarwa da gaisuwa.

1 Tessalonikawa 1:1–4

1 Bulus, Sila da Timoti,

Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi.

Alheri da salama su kasance tare da ku.

2 Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu. 3 Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.

4 Gama mun sani, ’yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku,

Hujjar Bulus ta Farko: Baiwowi na Mu’ujiza

Bulus ya samo hujjarsa ta farko game da gaskiyar Kiristanci daga baiwowi na mu’ujiza na Ruhu Mai Tsarki. Ya yi farin ciki da amincinsu marar tangal-tangal ga bangaskiyar Kirista, ya kuma yaba da wannan aminci.

1 Tessalonikawa 1:5–10

5 domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku. 6 Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar. 7 Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya. 8 Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne ko’ina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai, 9 gama su kansu su suke ba da labari irin karɓar da kuka yi mana. Suna faɗin yadda kuka juyo ga Allah daga gumaka don ku bauta wa Allah rayayye da kuma na gaskiya, 10 ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu, Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa.

Rayuwar Masu Wa’azi Ta Tabbatar da Gaskiyar Bishara

Ta wurin halaye, ɗabi’u da wahalolin masu wa’azin bishara, Bulus ya tabbatar da gaskiyarta. Ya gode wa Allah domin Tessalonikawa sun karɓe ta ba a matsayin tsarin falsafa ba, amma a matsayin maganar Allah, kamar yadda tasirinta a kan ɗabi’unsu ya nuna.

1 Tessalonikawa 2:1–13

1 Kun sani, ’yan’uwa, cewa ziyararmu a gare ku ba tă zama a banza ba. 2 Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba. 3 Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba. 4 A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu. 5 Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu. 6 Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu.

A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku, 7 amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta. 8 Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu. 9 Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah.

10 Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya. 11 Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa, 12 muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.

13 Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.

Halin Tsanantawa na Yahudawa

Bulus ya nuna halin tsanantawa na Yahudawa, wanda yake gwada ƙarfin bishara da bangaskiyar waɗanda suka juyo. Ya nuna ƙiyayyarsu ga yi wa Al’ummai wa’azin bishara, da muguntarsu da halakarsu. Ya bayyana ƙaunarsa ga Tessalonikawa da burinsa na ganinsu, wanda tasirin Shaiɗan a kan zukatan masu adawa da shi ne kaɗai ya hana cika shi.

1 Tessalonikawa 2:14–20

14 Gama ku, ’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa, 15 waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane 16 suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Al’ummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe.

17 Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku. 18 Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu. 19 Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne? 20 Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.

Bulus Ya Aika Timoti Ya Ƙarfafa Su

Bulus ya bayyana damuwarsa game da Tessalonikawa, ya kuma tunatar da su cewa ya aika Timoti domin ya ƙarfafa bangaskiyarsu, ya kuma ta’azantar da su cikin wahaloli da yawa da dukan Kiristoci suke fuskanta, kamar yadda aka riga aka gargaɗe su.

1 Tessalonikawa 3:1–5

1 Saboda haka da muka kāsa daurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Atens mu kaɗai. 2 Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku, 3 don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan. 4 Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani. 5 Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza.

Rahoton Timoti Ya Ta’azantar da Bulus

Bulus ya bayyana cewa rahoton Timoti game da su ya ta’azantar da shi. Yana marmarin samun wata damar sake ganinsu, yana kuma addu’a su dawwama cikin tsarki har zuwa zuwan Kiristi.

1 Tessalonikawa 3:6–13

6 Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku. 7 Saboda haka ’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku. 8 Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji. 9 Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku? 10 Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.

11 Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yă shirya mana hanya mu zo wurinku. 12 Ubangiji yă sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku. 13 Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.