Bulus Ya Sake Rubuta Wa Tessalonikawa

Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta biyu zuwa ga Tessalonikawa domin ya gyara kuskuren da suka faɗa a ciki game da zuwan Ranar Shari’a kwatsam. Ya yi annabci game da ɓullowa, bunƙasa da rushewar babbar ridda a cikin ikilisiyar Kirista.

52 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bulus Ya Sake Gaishe da Tessalonikawa

Gaisuwar Bulus.

2 Tessalonikawa 1:1–2

1 Bulus, da Sila, da Timoti,

Zuwa ga ikkilisiya ta Tessalonikawa ta Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi.

2 Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Bulus Ya Yi Farin Ciki da Jimirinsu

Bulus ya yi farin ciki da tsayuwarsu daram a ƙarƙashin tsanantawa, ya kuma tabbatar musu cewa jimrewa da haƙurinsu shaida ce ta shari’ar da za ta zo, sa’ad da za su karɓi ladansu.

2 Tessalonikawa 1:3–6

3 Dole kullum mu gode wa Allah saboda ku, ’yan’uwa, haka kuwa ya dace, domin bangaskiyarku tana girma gaba-gaba, ƙaunar da kowannenku yake yi wa juna kuwa tana ƙaruwa. 4 Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha.

5 Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. 6 Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala

Kiristi Zai Zo Ya Yi Shari’a

Bulus ya annabta zuwan Kiristi domin shari’a, da halaka ta har abada ga dukan waɗanda suka ƙi bishararsa.

2 Tessalonikawa 1:7–12

7 yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko. 8 Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. 9 Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa 10 a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.

11 Sane da wannan, kullum muna addu’a saboda ku, don Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yă cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza. 12 Muna wannan addu’a don sunan Ubangijinmu Yesu yă sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.

Dole Babbar Ridda Ta Fara Faruwa

Yanzu Bulus ya fara gyara kuskurensu game da zuwan Kiristi da wuri domin shari’a. Ya gargaɗe su game da duk wata da’awar wahayi ta ƙarya ko wasiƙun jabu, ya kuma tunatar da su abin da ya riga ya gaya musu: dole babbar ridda ta fara faruwa. Ya bayyana halinta dalla-dalla.

2 Tessalonikawa 2:1–12

1 Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ’yan’uwa, 2 kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo. 3 Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. 4 Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.

5 Ba ku tuna ba cewa sa’ad da nake tare da ku nakan gaya muku waɗannan abubuwa? 6 Yanzu kuwa kun san abin da yake hana shi, wannan yana faruwa ne don a bayyana shi a daidai lokaci. 7 Gama ikon asirin tawaye ya riga ya fara aiki; sai dai wannan da yake hana shi zai ci gaba da yin haka sai an kau da shi. 8 Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa. 9 Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, 10 da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. 11 Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya 12 don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.

Bulus Ya Ƙarfafa Su Su Tsaya Daram

Bulus ya yi farin ciki saboda Tessalonikawa, ya kuma ƙarfafa su su tsaya daram cikin koyarwar da aka ba su.

2 Tessalonikawa 2:13–17

13 Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya. 14 Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.

15 Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.

16 Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, 17 yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.

Bulus Ya Roƙe Su Su Yi Masa Addu’a

Bulus ya roƙe su su yi masa da abokansa addu’a, domin a ɗaukaka bisharar Allah a cikin sauran al’ummomin Ba’al’ummai kamar yadda aka ɗaukaka ta a cikinsu, kuma a kuɓutar da su daga masu tsananta musu. Ya sake yin addu’a domin bangaskiyarsu da haƙurinsu.

2 Tessalonikawa 3:1–5

1 A ƙarshe, ’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku. 2 Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya. 3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan. 4 Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta. 5 Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.

Yadda Za a Bi da Malalata da Marasa Tsari

Bulus ya ba Tessalonikawa shawara kan yadda za su bi da waɗanda har yanzu suke rayuwar rashin tsari da lalaci, saɓanin bayyanannun umarnin da suka karɓa daga gare shi. Addu’arsa da albarkarsa.

2 Tessalonikawa 3:6–18

6 A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu. 7 Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba, 8 ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. 9 Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi. 10 Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”

11 Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. 12 Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci. 13 Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.

14 In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya. 15 Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa.

16 Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.

17 Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.

18 Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku duka.

An Kai Bulus a Gaban Galliyo

Bulus, wanda yake a Korint har yanzu, an kai shi gaban kursiyin shari’a na Galliyo, prokonsul wato gwamnan lardin Roma, ɗan’uwan Seneka.

Ayyukan Manzanni 18:12–18

12 Yayinda Galliyo yake muƙaddas Akayya, Yahudawa suka haɗa kai suka tasar wa Bulus, suka kuwa kawo shi cikin kotu. 13 Suka yi zarge cewa, “Wannan mutum yana rarrashin mutane su yi wa Allah sujada a hanyoyin da suka saɓa wa doka.”

14 A daidai sa’ad da Bulus yana shirin yin magana, sai Galliyo ya ce wa Yahudawan, “Da a ce ku Yahudawa kuna gunaguni game da munafunci, ko kuma wani babban laifi, da sai in iya sauraronku. 15 Amma da yake ya shafi gardama ce game da kalmomi da sunaye da kuma dokarku, sai ku ji da ita da kanku. Ni ba zan zama mai shari’a kan irin waɗannan abubuwa ba.” 16 Saboda haka ya kore su. 17 Sai duk suka juya kan Sostenes shugaban majami’a suka yi masa dūka a gaban kotun. Amma Galliyo ko yă kula.

18 Bulus kuwa ya ci gaba da zama a Korint na ’yan kwanaki. Sa’an nan ya bar ’yan’uwa ya shiga jirgin ruwa zuwa Suriya tare da Firiskila da Akwila. Kafin ya tashi, ya aske kansa a Kenkireya saboda alkawarin da ya yi.