Maryamu Ta Rera Waƙar Magnificat
Yankin tuddai na Yahudiya
7 ko 6 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Luka 1:46–56
1:46 Sai Maryamu ta ce,
“Raina yana ɗaukaka Ubangiji
47 ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
48 gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.
Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,
sunansa labudda Mai Tsarki ne.
50 Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa,
daga zamani zuwa zamani.
51 Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa;
ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.
52 Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu
amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
53 Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa
amma ya sallami mawadata hannu wofi.
54 Ya taimaki bawansa Isra’ila,
yana tunawa yă nuna jinƙai
55 ga Ibrahim da zuriyarsa har abada,
kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”
56 Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida.
Haihuwar Yohanna, Yarintarsa, da Rayuwarsa a Hamada
Haihuwar Yohanna Mai Baftisma da yarintarsa, da rayuwarsa a hamada.
Yankin tuddai na Yahudiya. Shekara ta 7 ko 6 kafin haihuwar Kiristi
Luka 1:57–80
1:57 Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa. 58 Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.
59 A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, 60 amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.”
61 Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.”
62 Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. 63 Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki. 64 Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah. 65 Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya. 66 Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.
67 Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,
68 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.
69 Ya tā mana ƙahon ceto
a gidan bawansa Dawuda
70 (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),
71 cewa zai cece mu daga abokan gābanmu
daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu
72 don yă nuna jinƙai ga kakanninmu,
yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73 rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,
74 don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu,
yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,
75 cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.
76 “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki;
gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,
77 don ka sanar da mutanensa ceto,
ta wurin gafarar zunubansu,
78 saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna,
hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,
79 don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu,
da kuma cikin inuwar mutuwa,
don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”
80 Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila.