Linjiloli

Sashe na 1: Tushen Bayanai na Linjiloli

Luka Ya Bayyana Hanyar Bincikensa

A cikin saƙon keɓe littafinsa, Luka ya bayyana hanyar bincikensa.

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Luka 1:1–4

1:1 Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu, 2 kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara. 3 Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus, 4 don ka san tabbacin abubuwan da aka koyar da kai.