Zamani na 2: Daga Warwatsewa zuwa Fitowa

Sashe na 1: An Rikita Harsuna Aka Warwatsa Mutane

Hasumiyar Babel

2234 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Farawa 11:1–9

1 To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce. 2 Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.

3 Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka. 4 Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”

5 Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini. 6 Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba. 7 Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”

8 Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin. 9 Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.

Jadawalin Al'ummai

Farawa 10

1 Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.

2 ’Ya’yan Yafet maza su ne,

Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.

3 ’Ya’yan Gomer maza su ne,

Ashkenaz, Rifat, da Togarma.

4 ’Ya’yan maza Yaban su ne,

Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. 5 (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)

6 ’Ya’yan Ham maza su ne,

Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.

7 ’Ya’yan Kush maza su ne,

Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.

’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne,

Sheba da Dedan.

8 Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya. 9 Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji. 10 Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar. 11 Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala 12 da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.

13 Mizrayim shi ne mahaifin

Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa, 14 Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.

15 Kan’ana shi ne mahaifin,

Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa, 16 Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa, 17 Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, 18 Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa.

Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu 19 har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.

20 Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

21 Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.

22 ’Ya’yan Shem maza su ne,

Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.

23 ’Ya’yan Aram maza su ne,

Uz, Hul, Geter da Mash.

24 Arfakshad ne mahaifin Shela.

Shela kuma shi ne mahaifin Eber.

25 Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.

Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.

26 Yoktan shi ne mahaifin,

Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera, 27 Hadoram, Uzal, Dikla, 28 Obal, Abimayel, Sheba, 29 Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.

30 Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.

31 Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.

32 Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.

Sassalar Shem 2348 kafin haihuwar Almasihu

Farawa 11:10–26

10 Wannan shi ne labarin Shem.

Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad. 11 Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

12 Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela. 13 Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

14 Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber. 15 Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

16 Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg. 17 Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

18 Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu. 19 Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

20 Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug. 21 Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

22 Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor. 23 Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

24 Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera. 25 Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.

26 Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.