An Annabta Zaman Yahudiya Kufai da Farfaɗowarta (continued)

Annabci na gaba ɗaya game da zaman Yahudiya kufai da farfaɗowarta.

714 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 26–27

1 A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda.

Muna da birni mai ƙarfi;

Allah yake ceton

katanga da kuma kagarunta.

2 A buɗe ƙofofi

saboda al’umma mai adalci ta shiga,

al’ummar da mai aminci.

3 Za ka kiyaye shi da cikakken salama

shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,

domin ya dogara a gare ka.

4 Ku dogara ga Ubangiji,

gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.

5 Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa

ya kawar da birni mai alfarma ƙasa;

ya rusa ta har ƙasa

ya jefar da ita cikin ƙura.

6 Ƙafafu sukan tattake ta,

ƙafafu waɗanda aka zalunta,

wato, sawun matalauta.

7 Hanyar masu adalci sumul take;

Ya Mai Aikata Gaskiya, ka sa hanyar masu adalci ta yi sumul.

8 I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka,

muna sa zuciya gare ka;

sunanka da tunani a kanka

su ne marmarin zukatanmu.

9 Raina yana marmarinka da dare;

da safe kuma raina yana son ganinka.

Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya,

mutanen duniya kan koyi adalci.

10 Ko da yake akan nuna wa mugaye alheri,

ba sa koyi adalci;

har ma a ƙasar masu aikata gaskiya sukan ci gaba da aikata mugunta

ba sa ganin girmar darajar Ubangiji.

11 Ya Ubangiji an ɗaga hannunka sama,

amma ba sa ganinsa.

Bari su ga himmarka don mutanenka su kuma sha kunya;

bari wutar da aka ajiye don abokan gābanka ta cinye su.

12 Ubangiji ka kafa salama dominmu;

duk abin da muka iya yi kai ne ka yi mana.

13 Ya Ubangiji, Allahnmu, waɗansu iyayengiji ban da kai sun yi mulki a kanmu,

amma sunanka kaɗai muka girmama.

14 Yanzu duk sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba;

waɗannan ruhohin da suka rasu ba za su tashi ba.

Ka hukunta su ka kuma kawo su ga hallaka;

ka sa ba za a ƙara tunawa da su ba.

15 Ka fadada al’umma, ya Ubangiji;

ka fadada al’umma.

Ka samo wa kanka ɗaukaka;

ka fadada dukan iyakokin ƙasar.

16 Ubangiji, sun zo gare ka a cikin damuwarsu;

sa’ad da ka hore su,

da ƙyar suna iya yin addu’a.

17 Kamar mace mai ciki da take gab da haihuwa

takan yi ta murɗawa tana kuka saboda zafi,

haka muka kasance a gabanka, ya Ubangiji.

18 Muna da ciki, mun yi ta murɗewa saboda zafi,

amma mun haifi iska.

Ba mu kawo ceto ga duniya ba;

ba mu haifi mutanen duniya ba.

19 Amma matattunka za su rayu;

jikunansu za su tashi.

Ku da kuke zama a ƙura,

ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki.

Raɓarka kamar raɓar safiya ce;

duniya za tă haifi matattunta.

20 Ku tafi, mutanena, ku shiga ɗakunanku

ku kuma kulle ƙofofi;

ku ɓoye kanku na ɗan lokaci

sai ya huce fushinsa.

21 Duba, Ubangiji yana fitowa daga mazauninsa

don yă hukunta mutanen duniya saboda zunubansu.

Duniya za tă bayyana zub da jinin da aka yi a kanta;

ba za tă ƙara ɓoye waɗanda aka kashe a cikinta ba.

27:1 A wannan rana,

Ubangiji zai yi hukunci da takobi,

takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna,

zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe,

dodon ruwa macijin nan mai murɗewa;

zai kashe dodon nan na teku.

2 A wannan rana,

“Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce

3 Ni, Ubangiji na lura da ita;

na yi ta yin mata banruwa.

Na yi tsaronta dare da rana

don kada wani yă yi mata ɓarna.

4 Ban yi fushi ba.

Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana!

Zan fita in yi yaƙi da su;

da na sa musu wuta duka.

5 Ko kuma bari su zo wurina don mafaka;

bari su yi sulhu da ni,

I, bari su yi sulhu da ni.”

6 A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa,

Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fure

ya cika dukan duniya da ’ya’ya.

7 Ubangiji ya buge shi

kamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi?

An kashe shi

kamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi?

8 Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi,

da tsananin tsawa kuma ka kore shi,

kamar a ranar da iskar gabas ta hura.

9 A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub,

wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa.

Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade

suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu,

har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare

da za a bari a tsaye.

10 Birni mai katanga ya zama kufai,

yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada;

a can ’yan maruƙa suke kiwo,

a can suke kwance;

sun kakkaɓe rassanta ƙaf.

11 Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su

mata kuma su zo su yi itacen wuta da su.

Gama mutane ne marar azanci;

saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba,

Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.

12 A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya. 13 Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.