Ayuba Ya Amsa wa Elifaz

2130 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ayuba 6–7

1 Sa’an nan Ayuba ya amsa,

2 “Da kawai za a iya auna wahalata

a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!

3 Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi,

shi ya sa nake magana haka.

4 Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina,

ruhuna yana shan dafinsa;

fushin Allah ya sauka a kaina.

5 Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci,

ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?

6 Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba,

ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?

7 Na ƙi in taɓa shi;

irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya.

8 “Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu,

da ma Allah zai biya mini bukatata,

9 wato, Allah yă kashe ni,

yă miƙa hannunsa yă yanke raina!

10 Da sai in ji daɗi

duk zafin da nake sha

ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.

11 “Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya?

Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?

12 Da ƙarfin dutse aka yi ni ne?

Ko jikina tagulla ne?

13 Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne,

yanzu da aka kore nasara daga gare ni?

14 “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki

ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.

15 Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba,

kamar rafin da yakan bushe da rani,

16 kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara,

yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,

17 amma da rani sai yă bushe,

lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.

18 Ayari sukan bar hanyarsu;

sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu.

19 Ayarin Tema sun nemi ruwa,

matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.

20 Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai;

sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba.

21 Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako;

kun ga abin bantsoro kuka tsorata.

22 Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina,

ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku,

23 ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina,

ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’?

24 “Ku koya mini, zan yi shiru;

ku nuna mini inda ban yi daidai ba.

25 Faɗar gaskiya tana da zafi!

Amma ina amfanin gardamar da kuke yi?

26 Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne,

ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi?

27 Kukan yi ƙuri’a a kan marayu

ku kuma sayar da abokinku.

28 “Amma yanzu ku dube ni da kyau,

zan yi muku ƙarya ne?

29 Ku bi a hankali, kada ku ɗora mini laifi;

ku sāke dubawa, gama ba ni da laifi.

30 Ko akwai wata mugunta a bakina?

Bakina ba zai iya rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba?

7:1 “Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya?

Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne?

2 Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi,

ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi.

3 Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza,

kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu.

4 Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’

Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe.

5 Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi,

fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki.

6 “Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri,

za su kawo ga ƙarshe ba bege.

7 Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai;

idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba.

8 Idanun da suke ganina yanzu ba za su sāke ganina ba;

za ku neme ni amma ba za ku same ni ba.

9 Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi,

haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba.

10 Ba zai taɓa zuwa gidansa ba;

ba za a sāke san da shi ba.

11 “Saboda haka ba zan yi shiru ba;

zan yi magana cikin ɓacin raina,

zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina.

12 Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa,

don me kake tsaro na?

13 Lokacin da nake zato zan sami salama

in na kwanta a gadona don in huta,

14 duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke,

kana tsorata ni da wahayi.

15 Na gwammace a shaƙe ni in mutu

maimakon in kasance cikin wannan jiki.

16 Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada.

Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.

17 “Mene ne mutum har da ka kula da shi haka,

har ka mai da hankali a kansa,

18 har kake duba shi kowace safiya,

kake kuma gwada shi koyaushe?

19 Ba za ka ɗan daina kallo na ba

ko ka rabu da ni na ɗan lokaci?

20 In na yi zunubi, me na yi maka,

kai mai lura da mutane?

Don me ka sa ni a gaba?

Na zame maka kaya mai nauyi ne?

21 Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba?

Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa;

za ka neme ni,

amma ba za ka same ni ba.”